Sashe 61
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maganar ta katse masa, sakamakon ganin Nasreen a kicin ɗin tana suya. Sosai ya razana domin ya ɗauka fatalwarta ce da kuma gizon da take yi masa ne. Sai ya yi matsaya jingina da bango yana salati, ganin lamarin ya fara yin nisa, ganin yana ganin 'yar'uwarsa da siffarta.
Nasreen tsoro ta ji, ta matsa da sauri tana kallonsa ganin yadda ya razana."Ina kwana Ya Damir?" Ta ce masa tare da kauda kanta.
Watsa mata wani irin kallo ya yi, wanda ya sanya a karo na farko ta ji wani abu ya harba har cikin zuciyarta. Ba tare da ya amsa gaisuwar ba, ya fita daga kicin ɗin yana jin yadda zuciyarsa ke bugu bisa rashin ƙa'ida.
Yana ƙoƙarin barin gurin Marwana da dawo. Ganinsa ya sanya ta ƙaraso sauri." Sorry coffee ko? Yanzu na tuna da shi na je tam..."
Binsa da kallo ta yi, lokacin da ya fara tafiya ba tare da ta ƙarashe ba.
Kicin ɗin ta shiga tana kallon Nasreen."Ya Damir ya shigo nan ne?"
"A'a." Ta yi mata ƙaryar haka tana sai ta natsuwarta.
Bin ta da kallon rashin yadda ta yi, sai ta haɗa masa coffee ta haye sama. Yana jin tana buga masa ƙofa da kiran sunansa, amma ya yi banza da ita cikin jin haushinta. A ransa ya gane so kawai take ta kashe shi da ransa game da Nasreen, domin da ta san halin da yake shiga inya ganta da ta tausaya masa.
Bayan sun kammala breakfast, suka shirya 'yan matan suka je gyaran jiki sannan in suka dawo za a yi musu lalli. Nasreen da Marwana kamar su ne amaren domin sun yi kyau sosai. Da aka zo lallin Marwana ta kalli mai ƙunshin ta ce,"Please ki yi mini yafi na amaryar zan biya ki ko nawa ne, saboda habibina ya biya kuɗi sosai."
Nasreen kama bakinta ta yi cikin tsantsar mamaki."Wai yaushe kika fara soyayar da har kika haukace haka?"
Dariya ta yi ganin yadda suka yo kanta suna tsokanarta. "Ki dai zauna kina jin kunya bakya iya more soyaya. Ni wallahi ina educated ba zan zauna ina jin kunya ba."
"Lallai Marwana kin fi ƙarfina." Ta ce tana mamakinta.
A gurin lallin haka ta yi ta soyayya da ya kira, kuma ta hana su magana. Ganin ta ishe su Nasreen ta miƙe za ta karɓe wayar, ganin haka ta kashe tare da miƙa mata tana dariya."Saboda irin ku 'yan sa ido na canza password ɗin wayata, yadda kika ja mini aji kafin na san kina tare da Ingawa sai na rama."
"Allah ya kaimu dole mu gansa in har ba auren sirri za ku yi ba." Ta ce tare da komawa ta zauna
Sosai suka fito sun yi kyau kamar saman alale. Tun da ya fuskanci tana cikin gidan ya daina sakkowa in sun falo, saboda in ya ganta sai ya ji kamar zai haɗiyeta. Ya gane sonta yake yi, amma kuma ba shi da courage da zai iya tunkararta.
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whats
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 32
Ranar ɗaurin auren sun sha kyau sosai. Bayan an ɗaura aure Ahmad ya gaya mata yana waje, domin shi ya kawo Mama, sannan ya wuce masallacin da za a ɗaura auren
Marwana tasha kyau sosai kamar ka sace ta ka gudu.
Ahmad ne ya kira ta, don haka ta gudu ba tare da Nasreen ta sani ba. Tarba ta musamman ta yi masa suka sha soyayyarsu. Duk hidima da ake yi tana can gurinsa suna shan soyayya. Sosai ta saki jiki ta da shi, domin zuciyarta ta gama aminta da shi.
Tana zaune a gefensa, Nasreen da ta gama nemanta ta gaji ta kira wayarta. Kallon wayar suka yi tare da sakin murmushi."Ɗauka amma kar kice mata kina gurina, so na ke mi yi mata bazata."
"Ok,"Ta ce masa idanunta na kansa.
"Hello kina ina ana ta neman ki Ya Damir ya aiko ki je ki kai masa abinci da abokansa."
"Ina can ina bawa fulawa ruwa."
"Marwana wai yaushe kika zama haka ne?"
Kallon Ahmad ta yi da yake ji kamar ya lashe ta."Tun ranar dana samu muradina"
"To ya yi, in kin ga dama ki zo ki kai ma fusataccen ɗan'uwanki abinci."
"Na ga kema yayanki ki ne don Allah ki..."
"Ba ki da hankali wannan damisar ya'yan na ki sai ke, saboda na hango shi yana ta huci." Kashe wayar ta yi ta suna dariya.
Miƙewa ta yi ganin shi ma ya miƙe."Ki je ki ba shi kulawa bari na je mu yi waya, sannan ki kula mini da kanki, bana son ki bari maza su yi miki magana."
"Shikenan Ya Ahmad ba ka da matsala."
Har ta juya za ta tafi ya kira sunanta.Waigowa ta yi ganin yadda yake kallonta da idanunsa da suke saukar mata da kasala.
"Yaushe ne za a yi namu auren, ki zama 'yar Mama kuma Antyn Nasreen?"
"Duk ranar da ka shirya, ina farin ciki na kasance cikin ahalinka." Ta ƙarashe maganar tare da rugawa da gudu.
Dariya ya yi sannan ya tafi cikin tsanannin farinciki.
Marwana abinci ta haɗa masa a kicin, sannan ta ɗauka ta nufi ɓangarensa. Yana zaune cikin abokansa suna ta hira. Yana kusa da Annur da ya ci wanka kamar za shi gasar kyau, saboda ya ga sahibarta, amma Damir ya hana shi sosai ya ɗauke fuska ya dake da suna hira. Da ya miƙe sai ya kamo shi ya zaunar da shi ya rantse babu inda za shi.
Dariya sosai yake yi masa ganin kishinta. Wayarsa ya zaro ya fara chatting da ita. Damir kuwa tun da ciro wayar hankalinsa na kan wayar. Ji yake kamar zai kwace don ya san da ita yake chatting, musamman da yi kalli wayar sai ya yi murmushi.
"Sannu Laila da majnun wato ke kina soyaya ki barmu da aiki?"
"Kar ki ga laifina shi ɗin mai zafi ne."
Tsaki ta yi ta fara tafiya tana faɗin,"Sai ki je ki bawa ƙawayenki abinci don na gaji."
An shirya dinner, bayan an kai amarya su Marwana kowacce sai da ta kwashi mutane a cikin motarsu. Damir sam ba shi da ra'ayin zuwa, tun da ya ji Annur ya ce za shi, sai shi ma ya shirya. Kallon mamaki ya bi shi dashi lokacin da yake fesa turare.
Gurin dinner ya cika maƙil, kowa sai murna yake yi. Duk inda Annur ya sanya kafa sai ya bi shi, duk ya hana shi sakewa. Annur da aka fara dinner ya so ya keɓe da Nasreen, amma sai Damir ya hana shi ko jirgawa suna tare. Dariya ya yi ya kalle shi,"In aka ɗaura aurenmu sai ka zo gidanmu, ka hana mu cin amarci, wannan masifa har ina ka ƙi aure ka kuma ce zaka hana ta."
Tsaki ya yi, yana kallon wayarsa ba tare da ya ce masa komai. Tun da suka zo gurin yake kallonta kamar makahon da ya warke daga makanta. Nasreen ta yi kyau sosai sai ƙamshi take yi. Idanunsa na ƙasa da take ta hidimar ta ba tare data kula da shi ba. Sosai ta sake tana ta hidimar bikin.
Da aka zo rawa zuciyarsa bugawa take kamar za ta fito, a tunaninsa ya ɗauka za ta yi rawa, Annur ya yi mata manni, amma karo na farko da ta fara burge shi duk rawar da suke yi, domin har Marwana ta taka, amma iya kallon su kawai take yi. Ko da Marwana ta ja hannunta don su shiga filin sai ta noƙe tana dariya, wannan abu da ta yi, ya sanya zuciyarsa nishaɗi har sai da ya murmusa, domin Annur bai samu damar yi mata manni ba.
Bayan an gama dinner washegari aka yi kamu, sai a washegarin bikin Annur ya samu suka sha hira. Duk yadda ya hana shi keɓewa da ita, zuciyarsa tafarfarfasa take yi. Haka dai aka yi biki aka ka amarya gidansu. Duk da cewar tsoron fitowa yake yi da take gidan, amma da ya ji Marwana tana faɗin yau za ta tafi, sai ya ji hankalinsa ya tashi, ji ya yi tamkar ta zauna a cikin gidan.
A kwanakin ya rasa gane kansa, domin shi kansa bai tabbatar da lamarin da yake ji a cikin zuciyarsa ba. Wannan zafin na ta da yake ji, ya rage sai yawan tunani ta, musamman kwalliyar dinner da ta yi ya kasa manta shigar. Sannan a duk lokacin daya tuna ta, amaimakon ya ji haushinta kamar yadda yake ji a da, sai ya ji zuciyarsa ta yi sanyi tare da sakin laulausar murmushi a fuskarsa.
Damuwarsa ɗaya, da suka koma aiki sai ya kasa sukuni ya yi ta zarya a harabar gurin. Burinsa ko zai ga gilmawarta, amma haka zai gama kaiwa da komowa tsakanin sama da ƙasa ba tare da ya ganta ba. In kuma ya yi sa'ar ganinta da Ingawa da yake jin kamar ya sallama me shi.
Washegari da safe, ya zo aiki tun daren jiya ya ƙasa gari ya waye, don babu bin da yake so sai ya ganta. Cikin sama ya ganta tsaye ita da Hajar da S. Bako suna tsaye a kusa da hanyar da zai shige ofis ɗinsa yana nuna musu aiki.
Nasreen sam ba ta lura da shi ba, domin hankalinta yana gurin S. Baƙo tana sauraren bayanin da yake musu.