← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 92

Sashe 64

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aikuwa Allah ya sakamata tun kafin aje ko ina."Ahmad yace yana duba wayarsa.

Ita dai shiru ta yi, tana jinjina lamarin sai ta kalle su ta nisa ta ce,"Ina ga zan canza wa su Raihann makaranta kar yaje ya ɗauke su don ya ƙuntata mini, saboda ba zan iya barin masa yarana ba."

"Babu abin da zai yi musu, ki kwantar da hankalinki ina tare da ke."

Miƙewa ta yi jikinta babu ƙwari ta shige cikin ɗakinta. Bayan ta yi wanka, tana zaune tana tuna rayuwar da suka yi a baya. Hawaye ya wanke mata fuska tuna wulaƙancin da ya yi mata. Hawayen ta share, sannan ta kwanta tana juya wayarta cikin damuwa. Zuwan Faruk ya ɓata mood ɗin ta, ko aikin da ta kwaso don ta yi kasawa ta yi.

Washegari da yamma, Faruk ya ɗauki wanka sosai ya ƙure a daka, saboda ya san ba zai ji daɗi ba in yaje gidansu don haka ya bita gurin aiki.

A lokacin da ya iso basu tashi aiki ba, har ya faka motarsa zai kira, sai wata zuciya ta ba shi shawarar ya sanya a kira ta don Damir ya gan shi.

Maigadi ya tura kiranta. Tana cikin ofis hankalinta na kan aikin da take sauri ta gama kafin a tashi, maigadin ya tura kofa ya shigo.

"Barka da hutawa Hajiya." Ya ce mata lokacin da ya yi sallama ya shigo.

"Yauwa barka Baba." Ta amsa tana kallon sa.

"Kina da baƙo a waje yace nayi kiran ki."

"Ni?" Ta dago tana kallonsa tare da yi masa tambayar hakan.

"Eh yana waje don a waje ya faka motarsa."

Mamaki sosai ya kamata, a ranta tana tunanin waye, domin ba ta yi da wani zai zo ba. Har ta buɗe baki za ta ce masa ba ta nan, amma sai ta miƙe ta kashe laptop ɗin.

"Ok Baba muje." Ta ce mishi tana tunanin baƙon ko kaɗan ba ta yi tunanin Faruk bane.

Tana wannan tunanin ta sauko ƙasa. A lokcin Damir yana tsaye a windo yana kallon waje. So yake ya tafi gida, amma yana son ganinta kafin ya tafi. Ganin ta a ƙasa da sauri ya kwashi tarkacensa zuwa ƙasa.

Cikin mamaki Nasreen ta tsaya tana kallon Faruk da ya juya baya. Mamaki sosai ta yi, sai kuma ta fara juyawa zata koma ganin bai ganta ba.

Faruk da yaji taku, ya juyo gabansa na faɗuwa yana addu'ar Allah ya sanya ita ce.

Wani irin razana ya yi, ganinta domin a ranar bai ganta da kyau ba, ganin yadda ta canza ya wuce tunaninsa.

Idanu suka haɗa yayin da yake kallonta cikin shaukin so, ita kuma tana yi masa na tsana. Sosai ta ji tsanarsa a cikin zuciyarta har ba ta son ganinsa. Ranta ya ɓaci take fuskarta ta canza.

Fara tafiya ta yi, ganin haka ya biyota yana kiran sunanta, amma ba ta kula shi ba, wanda ganin hakan ya ja mayafinta, karab sai a idanun Damir da aka buɗe masa get zai fita.

Jiri ne ya ibe shi har sai da ya jingina da motar. Sau daya ya taɓa ganinsa, amma kuma kammanninsa sun zauna masa a idanunsa, saboda baya manta ranar da ta zama baƙar ranar da ya rasa Batula, amma ya zo ya yi masa rashin mutunci. Wani irin tashin hankali ya kama shi, sai ya yi luuu zai faɗi. Muhsin da ya ƙaraso don su tafi tare ya ga halin da yake ciki.

"Subuhanallahi! Yaya take easy." Ya ce masa, tare da kama shi yana kallon inda yake kallo, dai dai lokacin da Nasreen ta watsa wa Faruk mari mai zafin gaske!

"Ƙarka sake kiran sunana har ka yi tunanin riƙe mayafina, saboda ba ni da alaƙa da kai." Ta furta cikin zafi tana kallon sa, sai kuma ta fara tafiya.

Cikin tsananin mamaki ya dage ƙuncinsa yana kallonta, sai kuma ya shanye mamakinsa, ganin za ta koma ciki ya ce,"Please Nasreen ki tsaya ki saurare ni wallah..."

"Na gaya maka karka ƙara kiran sunana, saboda bani da alaƙa da kai, in har ka kuma ka ƙara gigin haka ko ka biyo ni gurin aiki, wallahi sai na gurza maka rashin mutuncin da ba ka taɓa tunani ba, domin na tsane ka nayi dana sanin ranar dana fara haɗuwa da kai. Ko mai sunanka bana fatan na sake ganinka."

"Ina da alaƙa dake karki manta ina da yara dake."

"Yaran da ka wulaƙanta sai yanzu ka san da su? Wallahi ka fita cikin rayuwata domin bana ƙaunar ganinka." Tana gama faɗin haka ta wuce ciki tana huci.

Damir da Muhsin suka raka ta da idanu, wacce ba ta kula da suna gurin ba. Tana shiga cikin ofishin ta zauna tana huci tare da mamakin yadda akayi yasan gurin har ya biyo ta. Ranta ya ƙara ɓaci sosai tana ƙara jin tsanarshi. Frij ta buɗe ta ɗauki ruwa ta sha, sannan ta ji ta fara dawowa daidai.

Farouk ya daɗe a gurin, cikin yanayi na nadama yana kallon inda ta bi. Hankalinsa ya tashe yayin da madarar sonta da ƙaunarta ya kara shigarsa. Shi da yake son mace kalar madara kuma ya kasance komai ya ji. Yau ga Nasreen ta dawo irin matar da yake so, amma kuma ba ta a hannunsa. Ji ya yi ko mai zai faru ba zai bar ma wani ita ba. Da ƙyar ya ja jiki, ya shiga motarsa cikin tsananin tashin hankali hawaye yana bin fuskarsa.

Damir rasa tunaninsa ya yi, gabakiɗaya ji ya yi kamar zai yi hauka. Mota Muhsin ya buɗe masa ya shiga."Please ka ja motar mu bar gurin nan." Ya furta yana furzar da numfashi mai huci.

Waiwawoya ya yi, ya kalle shi ganin yadda ya rikice. Muhsin tuni ya gama fahimtar son da yake yi wa Nasreen, amma ya kasa fahimtar hakan, ko kuma ya gane girman kansa da izza bazu bar shi ya furta ba.

A cikin wannan halin suka isa gida. Da ƙyar ya samu ya fito daga cikin motar. Kai tsaye falo ya shiga sannan ya haye sama. Da sauri Momi ta miƙe tana kallon Muhsin da ya shigo.

"Lafiya?" Ta ce masa cikin damuwa. Ya kasa bata amsa sai ya bi shi ganin yadda yake tafiyar kamar zai faɗi. Da suka shiga cikin ɗakin ya taimaka masa ya kwanta.

"Please kunna mini A.C da fanka." Ya haɗa maganar da ƙyar yana jin kamar numfashinsa zai ɗauke.

Babu musu ya kunna masa, sannan ya dawo kusa da shi ya ce,"Ya Damir y...."

"Please Muhsin go." Ya daka masa tsaya yana faɗin haka.

Da sauri ya fice cikin tausayawa ɗan'uwansa. Yana fita hawayen da suke ƙoƙarin zubo masa suka zubo."Yaushe na kamu da sonta, haka har na ke jin zan yi hauka ganin tsohon mijinta?" Ya yi wa kansa tambayar cikin damuwa.

"Dole na bar ƙasar nan ba zan zauna ba, domin matuƙar ina ganinta da shi xuciyata za ta iya bugawa. Ba zan iya jure ganin ta da wasu ba ballanatana tsohon mijinta da na son za ta iya haƙuri ta koma duk da abin da ya faru." Ya ƙarashe maganar tare da ɗaukar wayarsa ya nemi flight, domin ya gama yanke shawarar haka shi ne kawai mafita.

A falo da Muhsin ya sauko, gabakiɗaya suka yi kansa suna tambayarsa."Mai ya faru da shi?"

"Tsohon mijin Nasreen ya gani ya zo gurinta."

Cikin mamaki Marwana ta zare idanunta ta ce,"Kana nufin faruk?"

"Eh shi shi."

"Lallai Faruk ba shi da kunya, duk abin daya yi har yana da idanun da zai kalle ta?"

"Namiji ne ai musamman da yana taƙama da yana da yara a gurinta, wataƙila ya gane kuskuren shi ya dawo gareta."

"Haba Mommy, a tunanina Faruk ko mai zai fuskanta ba zai iya nuna mata fuskarsa ba. Mutumin nan azzalumi ne."

"To shine don ya gansu da ya rikice haka? Ya san yana sonta yake tayin hauka. Sai ya zauna in hakan da yake yi zai sanya ta fahimci yana sonta Allah ya bashi sa'a." Mommy ta ce cikin takaici.

"Ya yi ta sanya wa kishinta yana cutuwa, haka sai wani ya aure ta." Marwana tace cikin takaici.

Momi saboda jin haushinsa miƙewa ta yi ta wuce cikin ɗakinta.Marwana jikinta na rawa ta ɗauki wayarta. Numbarta ta kira wacce ringing biyu ta ɗaga."Da gaske Faruk ya zo gurinki?"

Mamaki sosai ya kamata na jin tambayar da ta yi mata."Ya akai kika sani?"

"Ya Damir ya shigo a birkice shi ne ya Muhsin ya ce Faruk ne ya zo gurinki."

Ƙara shiga cikin mamaki ta yi."Wallahi ban gan su ba, amma ya zo Marwana ko kunya bai ji ba. Ai dama da kika gaya yazo gidanku na gaya miki zai dawo. Nasreen cutar da ya yi mini dole Allah ya hukunta shi, abin da za ki yi kawai ki yi aure."

"Ni ma shawarar dana yanke kenan, saboda naji tsoron da ya bini gurin aiki, har marin shi na yi amma wallahi bai ɗauki mataki ba."

"Lallai duniya ta yi masa kamun kazar kuku. Gara da kika wanka masa mari. Don ya gane Nasreen ɗin yanzu ta bambanta da wacce ya sani."

"Ki bari kawai yau ya ɓata mini rai." Maganar suka ɗan yi sannan suka kashe wayar. Aje wayarta ta yi, tana mamakin yadda a ka yi ya gani da kuma rikicewar da ya yi.

"Wai hakan sona yake yi.?" Ta yi wa kanta tambayar cikin shakku, sai kuma ta ce,"Kai da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa.."

Farouk ya haukace, idanunsa sun rufe burinsa kawai ya samu hanyar da zai dawo da Nasreen. Cikin dare gaza bacci take yi, domin da ya rufe idanunsa ita yake hangowa. Gabakiɗaya ya susuce ganin yadda ta koma. Hango Nasreen ta dawo gidan a matsayin matarsa kawai yake yi.

Damir ba tare da sanin kowa ya yi burking viser. Yana ta shiryen-shiryen tafiya, domin yana ganin hakan shi ne mafitar da zai kawo sauƙi a rayuwarsa.

Ranar sati, Nasreen tana zaune ta ji sallamar mace a kofar falon su. Cikin mamaki ta tashi ta buɗe kofar."Fadila? Dama kina duniyar?"

Fadila ita ma tsayawa ta yi da tsohon cikinta, tana kallonta cikin mamaki."Nasreen kece kika dawo haka?"

Harararta ta yi tana faɗin,"Ko da yake bai kamata na yi miki magana ba, haba Fadila tun da kika auri soja kika manta ni."
Chapter 64 · 0% Book details