← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 92

Sashe 68

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai da gaske zarginsa kike yi? Uban me kike da shi har zai ɗauka? Ki yi minimizing wayar sai ki duba abin da ya yi."

"Yauwa haka ne kuwa kaina ya kulle." Ta ce tare da yin abin da ya ce.

Ganin gallary ya shiga sannan ya kuma shiga Whatsapp. Shiga cikin Whatsapp ɗin ta yi tana dariyar farinciki don ta gano shi, musamman da ta ga an buɗe data, saboda messages sun shigo a lokacin.

"Ok, wato hutunanta ya tura sai ya goge?" Ta yi ma kanta tambayar tare da kwashe wa da dariya.

"Lafiya mai ya yi?"Muhsin ya tambaye ta ganin yadda farincikinta ya ninku.

"Ban sani ba ranar da na tambaye ka ba haka ka ce mini ba? To ba zan gaya maka ba sa..."

"Ke ina wasa dake ne?" Ya ce mata tare da nufota a fusace. Ganin haka ta ruga da gudu suka shiga zagaye ɗakin daga baya kuma suka yi falo, ba tare da sun kula da kiran da Mommy take musu ba.

Saura kaɗan su buge shi da ya fito zai tafi aiki."Ba ku da hankali ne Muhsin mene ne haka?" Ya yi musu tambayar yana daka musu tsawa.

Natsuwa suka yi, amma tana kallonsu tana mishi dariya.

"Yauwa ya Damir cewa ta yi wa..."

Da sauri ta toshe masa baki tana faɗin,"Wallahi ƙarya ne ban ce komai ba, wai sharri zai yi mini kar ka bani kuɗin da na tambaye ka."

Tsaki ya yi tare da fita ba tare da ya kar kallonsu.

"Kin san Allah in baki faɗa mini ba, sai nace kin ce masa ɓarawo."

Zare idanunta ta yi, tana kallon da da yake mata dariya zai fita."Wallahi in har ka furta ni kuma sai na gaya wa Hajar, yarinyar da kake waya da ita kana fakewa da mate ɗinka ne."

"Da na karya ki a gidan nan." Ya ce mata da sauri.

"Allah ya ba ka sa a ka gaya masa to." Ta ce tare da yi masa gwalo ta wuce ɗakinta. A cikin ɗakin murna take yi sosai da tabbatar da ya kamu da ƙaunarta. Zama gefen gado cikin farin ciki, sai hankalinta ya kwanta yanzu kuwa za ta tunzura shi yadda zai furta yana sonta, ba tare da ya wahalar da su ba.

A ofis wuni ya yi yana ta kallon hotunan da ya tura. Wani ya yi murmushi wani kuma ya saita bakinsa daidai bakinta ya yi kissing. Haka ya kasance cikin farinciki har zuwa aka tashi. Kasancewar aiki suke yi sosai sai bai samu damar ganinta ba, duk da yana yi yana sauka ƙasa don kawai ya ganta.

Da dadddare suna dinner, mommy ce take masa hira, amma gabakiɗaya hankalinsa ba ya gunsu. Ji yake a zuciyarsa ba zai iya kwanciya ba tare da ya kira ta.

"Mommy, Ya Annur gaskiya ya iya soyayya har na ji Nasreen tana faɗin za ta bashi dama ya turo, ganin Faruk zai takura ma...."

Wani irin tari da ya tsarƙe shi, ya sanya ta kasa ƙarashe maganar. Gabakiɗaya suka yi kanshi suna faɗin,"Sorry."

Ruwa Marwana ta miƙa masa sai ya karɓi na Muhsin ya kurɓa."Sannu ka ci abinci a hankali." Momi ta ce masa dariya na son kubce mata ganin yadda ya koma.

Tun da ta faɗi haka ya ji abincin ya fita a ransa. Ko da Mommy ta tura masa abincin bai ci ba.

"Aiko da Annuri ya dace mata ni fa yarinyar nan burge ni take yi, saboda sanyin halinsa da kuma natsuwarta."

Marwana ta karɓe da cewar,"Ga hakuri Mommy in har ya aure ta zai yi farin ciki, saboda haƙurinta a lokacin da take auren Faruk sai kin ga haƙurin da ta yi."

"Wallahi the girl is innocent." Cewar Muhsin.

WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 36

"Wallahi the girl is innocent." Cewar Muhsin.

"Ai ga shi nan Allah ya saka mata da miji na gari, domin yaron yana da haƙuri ko Damir?"

Da sauri ya ɗago kansa cikin damuwa jin abin da ta ce,"Ni ma ban sani ba, abokina ne ba kwana nake da shi ba, ballanatana na san halin da duka."

"Amma tsawon shekara nawa kuna tare? Bana manta aurensa na farko har dakai aka je jin magana?"

"Hmmmmh! Ya canza yanzu sam ba ta dace da shi ba." Ya tsinci kansa yana faɗin haka, domin shi kansa bai san lokacin da ya furta hakan ba.

"Saboda me zaka ce haka, kuma da wa ta dace?"

Da sauri ya miƙe yana hararar Marwana jin tambayar da ta yi masa."Mommy gaggawa aikin sheɗan ne. Yai dai kamata ta zauna ta natsu ta samu miji na gari, kuma duka yaushe auren na ta ya mutu?"

"Babu zancen gaggawa Damir, tun da ta samu miji ta yi aurenta kawai."

Fara hawa sama yayi, ba tare da ya ce komai ba. A tare suka kalli juna suka yi murmushi. Yana shiga cikin ɗaki ya kulle kofar tare da nemo numbarta ya kira.

Cikin sa'a ta shiga ta fara ringing. Da sauri ya kashe wayar, don ƙarar da kiran yake yi tamkar zuciyarsa ke bugawa. Cikin takaici ya kaiwa kansa duka, ganin ya kasa samun ƙarfin gwiyar kiranta.

"Mai ya sa nake jin tsoronta?" Da sauri ya ƙara kiran cikin dakuwar zuciya.

Nasreen tana zaune a kan gado da waya tana murmushi. Ta gama waya da Annur kenan.

Ganin baƙon number sai ta yi tunanin Faruk ne. Ƙin ɗaukar wayar ta yi har sai da ta yi ringing sau biyu.

Cikin sarewa ya ije wayar ya zauna jikinsa a sanyaye. Har ya yi fushi ba zai ƙara kira ba, sai kuma ya kasa sakamakon zuciyarsa da ke addabar sa daya kira ta, domin hankalinsa ya tashi sosai jin an fara zancen a tura.

A kiran na uku har ta kai ƙofa, sai kuma ta dawo cikin tsanannin fushi ta ɗauka. A zuciyarta ita kaɗai ta san irin zagin da za ta yi masa.

Da ta ɗauki wayar, sai wata zuciya ta ba ta shawarar ta bari yayi magana, don haka ta yi shiru tana sauke numfashi.

Da sauri Damir ya kanga wayar a ƙuncinsa cikin rashin abin da zai ce. A tunaninsa za ta yi masa sallama, sai ya samu abin da zai furta.

Cire wayar ta yi a kunninta don ta yi tunanin an kashe, amma sai ta ga ba a kashe ba.

"Assalamu alaikum." Ta furta cikin sanyanyar murya.

Zuciyarsa ta buga ya kasa amsawa. Ganin haka sai cire wayar a kunninta." Wa alaikis sallam. Nasreen." Ya samu damar iya furtawa yana rintse idanunsa.

Cikin tsananin razana, ta kalli numbar tana tunanin ko muryarsa ke mata gizo. Mamaki sosai ta yi har ta kasa cewa komai." Nasreen ce?"Ya yi mata tambayar da ya sanya ta kasa amsawa har na wani lokaci, kafin ta saita zuciyarta dake bugu.

"Eh ni ce ina wuni Ya Damir?" Ta ce masa cikin sanyin muryarta.

Gaisuwar da ta yi masa, sai ya samu ƙarfin gwiya, duk da cewar ba shi da abin da zai ce.

Dubara ta faɗo masa ganin sun yi shiru sai zuciyarsu da ke bugawa.

"Na kira na yi miki godiya saboda kin yi aiki da kyau." Ya furta yana jin takaicinsa.

"Ok ba komai." Ta furta bayan ta ja numfashi.

Tsintar kansa ya yi da kashe wayar ya jefe da ita kan gado.

Kasa bacci ya yi, yana ta tunanin yadda zai hana auren da Annur ya bayyana mata sirrin zuciyarsa. A daren bai iya rintsawa ba har sai da ya samu mafita. Murmushi ya yi, tare da cusa hannunsa a a cikin sumar kansa.

Washegari da safe cikin farinciki ya isa ofis. Sanarwa ya yi akwai canje-canje da zai yi a gurin aiki. Ya canza wa ma'aikata da dama ofishin daga ƙarshe jin canjin da ya yi wa Nasreen ya shayar da su mamaki.

Hajar ta kalle ta cikin mamaki, wacce tun da ta ji inda ya mayar da ita ta kasa cewa komai.

"Ikon Allah gaskiya na fara zargin wani abu. Kamar Ya Damir akwai wani abu a zuciyarsa, domin in ka ga kare yana shinshinar takalmi ɗauka zai yi."

"Wallahi Hajar tun da ya ce ta zama sakatariyarsa na shiga mamaki. Ke Nasreen ki gaya mana ko soyayya kuke yi a ɓoye?"

Jin tambayar da suka yi mata sai ta ɗago a birkice tana kallonsu.

"Abin ne da mamaki lokaci guda ya ba ki sakatariyarsa?"

Ta kasa ce musu komai, saboda kamar yadda kansu ya kulle haka ita ma. Fara tafiya kawai ta yi suka rakata da ido.

Tana tafe tana tunanin dalilin sa na yin haka har ta isa ofis ɗinta. Zama ta yi tana tunani sai ga Ingawa ya shigo a birkice."Nasreen na shiga cikin tashin hankali sosai jin oga Damir ya mayar dake sakatariyarsa. Na fara jin tsoro kamar rasa ki zan yi! Please in har kika sona ki ba ni damar na tura gidanku, saboda duk abin da ya faru tsakaninku ba zan iya zuba idanu ya aure ki ba, ina son ki kan soyayyarki zan zamo mai son kaina."

Kasa ce masa komai ta yi, tana kallon sa ganin yadda ya tayar da hankalinsa."Please Nasreen in har kin sona ki ba ni dama na tura iyayena a cikin satin nan." Yana ƙarashe maganar ya fice daga ofis ɗin yana jin tamkar zai yi kuka.

Damuwa ce ya yi mata yawa sosai har ta kasa cewa komai. Ta kasa gane nufinsa na mayar da ita sakatariyarsa, in har ya yi hakan ne don ya ƙuntata mata, sai dai su ƙuntata wa juna.
Chapter 68 · 0% Book details