← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 92

Sashe 26

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana cikin ɗura wa duk ahalinta ashar ya ji bugun get kamar za a karye.

Da sauri ya nufi get ɗin yana huci kamar mesa."Wane ɗan iska..." Maganar ta tsaya sakamakon ganinsa, da ya yi fuskarsa babu rahma.

"Ɗan iskan da ya ba ka auren yarsa, ka ci moriyar ganga ka yada kyaurenta ne." Ya ce a harzuƙe yana kallon sa

"Babu sauran abin da ya haɗani da kai, 'yarka ce kuma na sake ta, wallahi in har ka zo ka ɓata mini rai zan gurza maka rashin mutunci." Ya furta ba tare da shayi ba.

"Yanzu kam babu kare bin damo, tun da ka saketa shi ya sa na dawo maka da yaranka, ka san ban ɗoro su a kayan gara."

"Ina baƙin talauci ya barka ka yi garan ma." Ya ce masa yana kallon sa.

"Haka ne dangin ƙaruna shi ya sa na dawo maka dasu, saboda wallahi ka san ba zan yarda su zauna ba. Nasreen na ji xan haƙura ta zauna tun da ni na haife ta, amma ban da waɗannan yaran."

"Ni kuma ba zan amshe su ba, saboda tun da muka yi aure na nuna mata bana son haihuwa, amma sai da ta na ce ta haihu."

"To ka kai bolansu ka zubar, amma ba zan riƙe 'ya'yan mara mutunci kamar ka ba." Ya ce tare da tura masa yaran, ya fara tafiya yana ja masa tsinuwa tun daga kakanninsa.

Faruk sai ya yi sororo yana kallon sa har ya ɓule. Tsawa ya daka wa Raihan tare da mangareta jin kukan da take yi."Rufe mini baki 'yar banzan yarinya kawai." Ya ce tare da daka mata tsawa, wanda ya sa ta yi shiru ba tare da ta ƙara ko tari ba, saboda mugun tsoronsa da take yi.

Jan Musaddik ya fara da yake kuka sosai, tun da Baba ya ɗauko shi, saboda kuka har muryarsa ta dushe. Ko rarrashinsa bai yi ba, ya ja su yana zagi zuwa cikin gidan.

Yana shiga cikin ɗakin Rashida ta miƙe tana kallonsa."Faruk, waɗannan yaran fa?" Ta yi masa tambayar cikin gatsali.

"Sato su na yi." Ya ce mata tare da zama yana harararta.

"No, ban gane bane wai an yi yamma da kare. Ka san dai ba zan riƙe 'ya'yan uban kowa ba? Saboda ka hana ni haihuwa babu 'yar iskar da zata haihu na yi mata wahala."

"Ubana kike zagi kenan?" Ya taso a harzuƙe ya tsaya a gabanta.

Ganin yadda ya fusata sai ta sausauta."Ni ban zage ba, amma wallahi ba zan riƙe su ba, kuma ba za su zauna a gidan nan ba, don haka ka mayar da su."

"Idan gidanki ne sai ki mayar da su." Ya ce mata ba tare da ya kalle ta ba, sai kuma ya miƙe ya shige ɗakinsa yana faɗin,"A gidan nan za su zauna, kuma dole ki kula da su in har kika son zama a gidan nan."

"Ka daina cewa dole don wallahi ba ka isa ba. Wannan ai zalunci ne ka hana ni haihuwa, sannan ka rabu da matarsa sai ka kawo mini wasu tarkacen yaranka."

Jin bai amsa ba ta gane ya shiga ciki. Wata uwar tsawa ta daka musu tana kallonsu."Rufe mini baki don uwarka wanda ya gadon masifa." Ta ce wa Musaddik tare da sanya hannu ta buge masa baki da yake kuka.

A maimakon ya yi shiru, sai ya ƙara sakin kuka ya faɗa jikin Raihan yana kiran Umma. Harara ta zabga musu tare da shigewa ciki. Raihann ta rungume shi tana kuka sosai. Miƙewa ta yi ta koma hannunsa da nufin su fita gidan, amma ganin sun kulle ƙofa, sai ta koma ta ci gaba da kuka.

Suna zaune a gurin har kusan awa ɗaya. Farouk da ya shiga cikin ɗaki da wanka ya yi ya kwanta. Bai san mai ya sa tun da ya yi sakin yake cikin damuwa ba. A tunaninsa rashin mutuncin da ta yi masa ya ɓata masa rai. Zagin da tasha Allah kawai ya sani.

Sai dai ya gama baccin ya tashi ya fito falo. Turus ya yi ganin Raihan rungume da Musaddik ya yi kuka har ya gaji yana bacci. Ita ma gyangyaɗi take yi a haka.

"Raihann," Ya kira sunanta cikin damuwa. Karon farko ya ji wani iri game da yaran.

Da sauri ta buɗe idanunta tana sosa kanta."Tashi ku shiga cikin ɗakinku." Ya ce tare da kamata ya ɗauki Musaddik da ya yi nisa cikin bacci. Babu musu ta mike zuwa cikin ɗakin. Kwantar da shi ya yi, sannan ta kwanta ya ja musu ƙofa, ya fita zuwa ɗakin Rashida.

Tana zaune a tsakiyar gado da waya a hannunta. Jin shigowarsa sai ta ije wayar tana kallon ƙofa."Saboda iskanci yaran a falo kika barsu, in har na ki ne za ki yi musu haka?"

Cikin gadara ta ce,"Ba ka bar ni na haifa ba ballantana na san xafinsu."

Jin abin da ta ce ta sa ya ɓaci.'Yarannan babu inda za su je, don haka ki kwantar da hankalinki ki kama su ki riƙe...."

"Wallahi ba zan riƙe su saboda ba, zan sha wahala da yaran da ba nawa ba, sai sun girma su kama mahaifiyarsu."

"Aikuwa zaki fuskanci matsala da na...."

"Faruk, ni fa bance ka saki mahaifiyarsu ka ɗaura mini wahala ba, tun da ka ga na aminta da planning ka san bani da ra'ayin kula da yara. Don haka ba zan wahala da ɗan kowa ba."

"Ke! Gidan ki ko nawa? In har kina son zama da ni, ki kula da su, sannna ki yi musu abinci ki ba su." Ya daka mata tsawa tare da magana cikin tsanannin ɓacin rai.

"Ba zan iya ba ka dawo da uwarsu don bai ce ka sake ta ba, in har ba za ta tafi da yaranta ba. Ni kuma ba zan yi wahala da su ba."

"To shikenan ni da ke mu zuba shege ka fasa." Ya ce tare da juyawa ya fice daga gidan.

Nasreen tun da Baba ya fita take ta kuka kamar ra ta zai fita."Mama don Allah ki yi sani abu ya bar ni na kula da yarana, wallahi zan tsaya tsayin daka na basu abincin da za su ci. Yaran wahala za su yi, sam ba zai kula da su ba."

"Ki yi haƙuri kawai tun da ya ce ba za su zauna ba, ki barwa Allah komai ki yi musu addu'a. Yara nawa iyayensu suke mutuwa a barsu a hannun matan babaninsu, kuma su rayu cikin wahala su zama wani abu? In kika yi haƙuri komai zai wuce." Ta ce mata tare da dafa kafaɗunta.

"Wash! Na shiga uku! Abin da na guda sau da ya faru. Yau Faruk ya sake ni. Kuma yarana suna hannunsa." Ta ce tare da sakin razanannen kuka.

Da ƙyar suka rarrasheta ta yi shiru, ta zauna ta zabga tagumi tana addu'a a ranta. Jin muryar baban ya sanya ta miƙe da sauri. A tunaninta ko ya dawo da su, amma sai ta ga babu su yana ta masifa shi kaɗai.

"Ɗan iska matsiyaci an gaya mishi shi kaɗai ya iya tijara." Ya shigo yana faɗin haka.

"Baba, do...."

"Ke Nasreen rufa mini baki, kafin na gaura miki mari, duk abin da ya faru ke kika ja. Da nace ki haƙura tun da ya nuna baya so, amma sai kika kafe ga abin da kika jawa kanki nan. Kin san kina son zama da su, kika kasa zaɓan su ki haƙura da yin bautar ƙasar?"

Kuka ta ke yi ta kasa cewa komai jin abin da ya ce.

"Ban ga laifinta ba, mene amfanin zama da mutum mugun wanda ba ya son cigaban iyalinsa? Saboda ya san kuɗi za ta samu shi kuma ba ya son cigaban ta." Cewar Goggo.

Ganin ta yi shiru ba ta ce komai ba. Ba tare da ya kalle ta jin abin da ta ce ba ya ce,"Bari ki ji tun da ya yi sakin babu yadda zan yi. Kina gama idda aure za ki yi."

"Allah ya kaimu ta samu mai hankali mene amfanin zawarcin?" Mama ta ce masa. Ita kuwa da gudu ta shige ɗaki a ranta tana jin ita da aure sai a lahira.

Da dadddare kasa bacci ta yi tana ta juye-juye. Kuka sosai take yi tana tunanin halin da za su kasance, musamman Musaddik yaron da kullum yana jikinta. Ta yi kuka har ta ji babu daɗi. Ganin kukan ba mafita bane, sai ta tashi ta ɗauro alwala ta yi sallah.

Raihann da baccin dole ya kwashe ta. Rungume Musaddik ta yi suka kwanta. Da ya tashi ita ta cire masa wando ta sanya shi ya yi fitsari. Hannunta yake ja yana kuka."Anty Rai'an, ummaa." Haka yake kuka yana jan hannunta.

Kama shi ta yi ta rungume sam ba ta son su fita waje. Ganin kukan ba ƙare wa zai yi ba sai ta ruɗe ita ma ta saka kuka, suka cika gidan da kuka.

Rashida wacce take kicin tana girki. Tun da suka tashi suka fara kuka take surfa musu ashar. Ganin kuka na su ba zai ƙare ba, sai ta fito cikin tsanannin ɓacin rai.

Wata uwar tsawa ta daka musu da ya sanya suka yi shiru."Ka ga mini 'yan iskan yara! Ko ni na sanya aka saki uwarku? Za ku yi mini shiru kafin na kashe ku da duka!" Ta daka musu tsawa tana kai wa Raihan duka.

"Har da ke da girmanki kin kuka dai ka ce an miki wani abu. Bacin ina tsoron abin da tijararren ubanku zai yi mini, wallahi buɗe muku ƙofa zan yi ku tafi gurin uwar na ku. Don bai haifa ba ballantana na yaya." Ta ce tare da juyawa ta fita.

Shiru suka yi babu wanda ya ƙara tari sai hawaye da suke yi. Wata uwar tsuka ta saki ta ci gaba da girki. Da ta gama sa ya musu ta yi kaɗan ta kai musu, ba tare da ta damu ko sun ci ba. Saboda yunwar da suke ji da sauri suka ɗauka, sai dai suna kai baki suka ije. Yaji sosai ta sanya domin da biyu ta ƙara yajin. Musaddik yana kuka yana tsoronta. Haka suka wuni har dare sun kasa cin abincin, kuma sun kasa fitowa saboda tsananin tsoronta da suke ji.
Chapter 26 · 0% Book details