Sashe 17
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya ya yi sai kuma ya zauna a gefenta."Haba Nasreen kamar ba wayayyiya 'yar jami'a ba? Matan jami'a da idanunsu yake a buɗe wayewa ta yi musu yawa. Su ne fa ranar da aka kai amarya take seducing ɗin angon ta, ba tare da kunya da jan aji ba. Ke ni don ina son mace mai ilmi da wayewa ne, amma babu abin da zai sanya na auri yar jami'a domin yawancinsu ragowar lecturer ne."
Da sauri ta ɗago idanunta tana kallonsa."Faruk, ka yi musu mummunar fahimta, domin wasu ke ɓata wasu..."
"Don Allah ki yi mini shiru. Yanzu ni da kaina zan tabbatar da hakan. Da na yi maganar makaranta kin iya tanka mini. Cases nawa muke ji a cikin makarantar namiji ya yi lalata da su?"
Share ta ji zubowar hawaye, ganin ya aure ta ba tare da yadda a tsakaninsu ba.
"Na lura dake fa kan karatu ne kawai zamu samu saɓani, saboda yadda kika ɗauki boko, bana tunanin turawan da suka kawo sun ɗauka da mahimmanci haka. Kuma wallahi matuƙar za ki tauye haƙƙina kan boko za mu samu matsala da ke." Ya ce cikin fushi.
Ba ta yi mamaki ba yadda yake mata magana cikin ɗaga murya. Ko kafin su yi aure in ya zo zance yana ɗaga murya. Tuni ta gama fahimtata sam ba shi da haƙuri.
"Ki tashi mu je mu kwanta na ce!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka.
Da sauri ta miƙe ganin yadda ya canza fuska.
Ganin ya yi hanyar ɗaki ta bishi idanunta na zubar hawaye. Bayi ya shiga da nufin ya yi wanka. Ganin haka ta zauna a bakin gadon tana ƙare wa ɗakinsa kallo, don ya tsaru matuƙar gaske.
Gefen gadon ta samu ta kwanta. Bacci har ya suma ɗibanta, saboda kanta da yake ciwo ta ji yana dukan filon da take kwance.
"Wannan wane irin wulakanci ne za ki zo ki kwanta da less a jikin ki? Ke ni fa ina son mace mai wayewa da iya rayuwar aure, don haka ki buɗe idanunki bani kula, saboda in har kika ƙi haka to za mu sanya ƙafar wando ɗaya ni da ke."
Jin kalamansa ya sanya ta miƙe ta za ta fita.
Komawa gadon ya yi, tare da jan tsuka yana harararta domin shiru-shirunta haushi yake ba shi. Ya fi don macen da idanunta suka buɗe wacce za su ci duniyarmu da tsinke. Wannan dalilin ya sanya har yau yake ganin zuciyarsa ba ta yi masa adalci ba, na son bagidajiyar mace.
Nasreen kuwa tana zubar hawaye, tana duba kayan baccin da za ta sanya. Ta san cewa a yau babu wata ƙauna da tattashin da za ta samu. Allah ne kawai zai ƙwace ta a hannunsa.
Da ƙyar ta iya saka wata doguwar riga, sannan ta sanya hijabinta ta dawo ɗakin.
Tsaki ya yi." Shi kuma hijabin da kika saka kamar wata mai zaman makoki ko matar liman fa?"
Banza ta yi da shi ta zauna tana faɗin,"Na fa ɗaya." A ranta don ko mai zai yi mata ba za ta iya cire hijabin ba.
Gani da gaske ba za ta cire ba, ya sa ya shi miƙewa ya zo inda take. Janyo ta ya yi ya rungume tare da sakin ajiyar zuciya.
Jikinta ya fara rawa sai kuka amma bai kulata ba ganin za ta kawo masa matsala. Faruk ba tare da tausaya wa ko tuna sabon shiga bace ya amshi sadakinsa.
Ta yi kuka sosai har sai da muryarta ya rushe amma babu tausayi a zuciyarsa.
Yana kwance idanunsa a rufe yana jin yadda take ajiyar zuciya. Shiru ya yi a ransa yana mamakin yadda aka yi ta kula da mutuncin kanta, duk da halin talaucin da suke ciki.
"Ki yi shiru kin dame ni da kuka, bacci zan yi." Ya furta tare da juyawa sai bacci.
Tsananin mamaki ya kamata, domin tasha jin ango yana taimakawa matarsa a ranar amarcinsu.
Tana zaune cikin damuwa ta ji yana jan rago.
A hankali ta ɗan miƙe, amma sai ta koma ta zauna da sauri tana jin raɗaɗin azaba. Rintse idanunta ta yi cikin muryar kuka tana kiran sunan Allah.
"Faruk, ka taimaka mini na ba zan iya tashi ba." Ta furta cikin muyar kuka.
"Ki yi shiru ki kwanta mu yi bacci." Ya ce yana jawo ta jikinsa.
Da sauri ta ƙwace jikinta cikin hawaye.
"Ba zai tsabtace kansa ba?" Ta yi ma kanta tambayar haka duk da ta san cewa ba wai ya haramta bane, amma kwana da tsarkin yafi.
Cikin dabara ta bi bango zuwa kicin. Ruwan zafi ta ɗora ta zo ta bawa kanta duk wata kulawa. Sannan ta samu sama-sama. Falo ta dawo ta ɗauki kazar da ya rufe mata ta ci, jin yadda cikinta yake juyawa.
Ba ta wani ci sosai ba ta ije kazar saboda hatta bakinta ba ya mata daɗi. A maimakon ta koma ɗakinta, kwanciyarta ta yi kan kujera tana mamakin halin angonta.
Cikin dare zazzaɓi mai zafin gaske ya kamata. Ta miƙe don ta rufa jin yadda kyarmar sanyi ya kamata.
Ga mamaki ta sai ta ji ta a jikin mutum. Da sauri ta fara kiciniyar matsawa daga jikinsa.
Buɗe idanunsa ya yi, yana hamma a lokacin kuma aka fara kiraye-kirayen sallah.
"Gari ya waye haka? Gaskiya ban yi bacci sosai ba." Ya ce mata yana kallonta.
"Ba ki da lafiya da safe zan siya miki paracetamol." Iya abin da ya furta kenan ya ci gaba da baccinsa.
Ranta ya ɓaci sosai cikin mamaki take kallonsa. Miƙewa ta yi tana mamakin yadda aka yi ya ɗauko ta, ba tare da ta ji ba.
Tuna da paracetamol a jakarta da Ya Ahmad ya kawo mata juya da rana. Ya sanya ta miƙe ta ɗauki jakarta sha maganin.
Ɗan komawa ta yi ta kwanta don ta bawa jikinta hutun mintina. Bacci mai ƙarfi ya ɗauke ta. Ba ta farka ba sai ta ji ana sallar asuba.
Da sauri ta tashi tana salati. Gefen Faruk ta kalla da yake shara baccinsa kamar ba musulmi ba, domin duk musulmin ƙwarai wanda ya yi riƙo da addininsa ya kuma tsaida sallah. Bai kamata ace lokacin sallah sai an tashe shi ba.
"An ya na yi dacen miji kuwa? Wanda zai ɗora ni a tafarkin tsira ina kauce? " Ta yi wa kanta tamabayar cikin damuwa
"Faruk, sallah ake yi." Ta tana kallonsa.
"Ke ki kyale ni zan yi ta ina tashi saboda na gaji jikinsa ko ina ciwo yake mini. Ga gajiyar biki ga wanda kika sa ya ni." Ya ce yana kallonsa sai kuma ya miƙe mata hannu.
"Zo mu kwanta in muka tashi mu yi tare."
Ta kasa ce masa komai, wanda ganin haka ya juya ya ci gaba da baccinsa.
Hawaye take zubarwa, hawaye da ta san in har haka rayuwarsa za ta ɗora ta rinƙa yi har ƙarshen rayuwarta.
Alwala ta yi ta yi sallah sannan ta yi azkar. Miƙewa ta yi ta shiga bayi ta ƙara gasa jikinta.
Tana zaune tana jan carbi har gari ya waye. Ganin bakwai ya yi ya sanya ta ƙara tashinsa.
Hannunsa ya sanya ya ja jata ta faɗa jikinsa. "Bari na sanya ki taya ni wankan."
Duk yadda ta so ta ƙwace jikinta ya ƙi har sai da ya gama abin da zai yi. Mamaki da takaici suka cika ta.
"Zo mu je mu yi wankan." Ya ce mata babu alamun ya damu da wucewar lokaci.
Miƙewa ta yi wanda bai ja da tsawo ba ya shige bayi, musamman ganin kallon da take masa.
"Na shiga uku! Wani irin miji na samu wanda baya kula da addininsa?" Ta furta cikin zubar hawaye.
Da ya fito daga wankan sai da ya gama ɓata lokacinsa gurin shirya wa. Sannan ya reshe jikinsa da turare, ya shinfiɗa dadduma ya yi sallar da ba ta ɗauke shi tsawon minti biyar ba.
"Baby ba gaisuwa?" Ya yi mata tamabayar ba tare da damuwa da kallon tuhuma da take masa ba.
"Ina kwana? Amma ka san lokacin da ka yi sallah bai kamata ba?"
Kallon banza ya yi mata tare da amsa gaisuwar a gajarce.
"Takwas ɗin?" Tambayar da ya yi mata ya ƙara ninka tashin hankalinta.
Cikin rawar murya ta ce,"Eh, saboda a loka..."
"Nasreen dakata..!" Ya katse ta yana fadin haka.
"Sallah sallah ce in har mutum da safe zai yi. Da ma kin ga na barta har zuwa azabtar sai ki yi mini karabbanin wa'azi. Kuma ai na fi wasu, domin wasu suna nan ba sa yi sallar, suna kuma amsa sunan su na musulmai."
Hankalinta ya ƙara tashi jin abin da tace, wanda ta gane tsantsan jahilci damunsa.
"Faruk, don wani na aikata zunubi bai kamata ace kana duba wannan ba, domin wannan dalilin ya sanya Ubangiji yake kar mutum ya duba halin wanda ya yi masa nasiha, abin da ya fado..."
"Mu bar maganar nan, tun kafin ki ɓata mini rai, don ni ban shirya jin wa'azi ba 'yar gidan malamai."
Ta san abin da ya faɗa gatse yake mata. Jin haka ya sanya ta miƙe zata fita daga falon ba ta ce masa komai ba.
"Yunwa na ke ji. Ina fatan kin zo da gara?"
Katsa da kanta ta yi jin abin da ya ce, wanda kamar ba za ta amsa ba, sai kuma ta ce,"Eh, amma iya shinkafa ce kawai da taliya."
Wawan tsaki ya ja, tare da miƙewa saboda tsananin talauci garar ma ba za a kawo ma? Bayan duk wahalar da na yi?"
"Za a kawo sai yau Ya Ahmad zai je da Anty su siyo."
"Kar ma su suyi su bar shi, ai ba zan mutu da yunwa ba."
"Da ma na san za a rina, wai an saci sanin mahaukaciya. Na san cewa rayuwar aure a da kai ba zan kurɓi ruwan daɗi ba, wadannan abubuwan na yi ta kaucewa, amma Baba ya nace auren mu, bayan ya gama zubar mini da mutunci." Ta furta cikin zuciyarta.
Takalminsa ya saka tare da ficewa daga gidan yana ƙunkunai. Ta ɗauka abin kirki zai siyo, amma ga mamaki ta sai ta ga ya siyo biredi saba da ɗaya da madara na sachet, sai Lipton da siga gwangwani ɗaya. Da kwai guda biyu, sai magi biyar da gwangwani mangyada da kuma kayan miya.