Sashe 10
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Amma kin san na rantse ba za ki yi ba ko? Saboda wannan iskanci da ake yi a gurin kina matar aure ba zan bar ki ba."
Ƙaramin tsaki taja jin abin da ya ce."Kishin banza bayan ka jingine ni."
"Na gaya maka wallahi sai na yi service ka yi haƙuri kawai."
"Ashe kuwa za ki ɗauko wa kanki tashin hankali."
"A shirye na ke wane dare ne jemage bai gani ba." Ta ce masa.
Jin abin da ta faɗa sai ya ce,"To babu inda za ki kuma in kika fita sai na yi mugun saɓa miki..."
Kafin ya gama maganar ta daƙile wayar ganin yana ɓata mata lokaci. Jakarta ta ɗauka ta kai Musaddik da Raihan gidan Maman Muwaddat, sannan ta tafi hankalinta kwance. Sai da ta gama komai ta dawo, saboda rashin tsoro gidan Maman Muwaddat ta yi zamanta har sai da ta yi ninyar tafiya.
Farouk kuwa tun da ya san ya hana ta kuma za ta iya tafiya, don ya ga yanzu tashen rashin kunya yake damunta. Bai jima ba ya kashe kayan wutar ofis ɗin da ya dawo gida. Ganin ƙofarta a kulle ya kalli Rashidat ya ce,"Ina wannan 'yar iskar yarinyar ta tafi?"
A banza ce ta kalle shi don yanzu ba ta tsoron shi."Ka ba ni ajiyarta ne?" Ta ce tare da ɗauke fuska.
Zagayowar ya yi ya zauna a a gurinta."Wato saboda ta raina ni sai da ta fita?"
"Ai kana son rainin me tun yaushe na ke cewa ka sake ta, sai ka ce sai ka wulaƙanta rayuwarta."
"Ban shirya sakinta yanzu ba domin sakin na ta kamar farinciki za ta yi, ni kuma sam bana son ganin farincikinta."
Tsuka ta ja mai ƙarfi tana cin cingam ba tare da ta kula shi ba."Ai sai ka ci gaba da zama da ita, kana ciyar da ita ba ta maka amfani, kuma wallahi na gaji dole a raba kwana, matuƙar ba zaka bani wannan kuɗin na fara jari ba."
"Ya yi yawa gaskiya saboda da wannan kuɗin zai yi wani abu ko na sayi fili."
"To shikenan Faruk, in ka tashi mutuwa don Allah a haɗaka da kuɗaɗen da kake tarawa ba ka sakar mini. Haba ina matsayin matarka, amma ko mota ka kasa siyen mini alhalin kana da shi."
"Ban yi ninya ba kin san ba kwanciya na ke yi ba ina amansu."
"Jin abin da ya ce sai ta yi shiru ta fara tunanin komawa gurin Malam.
Tsaki ya yi ya wuce cikin ɗakinsa. Saboda bala'i yana zaune a falo da ya yi wanka. Ganin ta shigo ya tashi zuɓbur.
"Daga ina kike?"
"Ai na kira ka na gaya maka, da na dawo sai na zauna a gidan Maman Muwaddat."
"Da izinin uban wa?"
"Nawa don na ga Rashida ita ma ba ta gaya maka sai ta fita."
"An gaya miki ke da ita matsayinku ɗaya? Ita na yarda da ita, amma ke ina tantama a kanki."
"To shikenan duk abin da ka zarga a zuciyarki shi na yi." Ta ce masa ciki gatsali.
Matsota ya yi amma sai da take tana kallonsa."Nasreen kin san Allah in har ina aurenki ba za ki yi service ɗin nan ba."
"Saboda kana tsoron kar na yi na tara kuɗi na kaika kutu, ko baƙi cikin da kake mini ya kai haka."
"Yin ne ba ni da ra'ayi, kin san in na sake ki, na huta da kaina ne da ciyar dake babu amfani."
"To tun da ka san haka ka sauwaƙe mini, na gaji da zama da kai, don ban ga amfanin rayuwar aurenmu ba, tun da ka jingine ni."
"Eh, ba zan iya kwanciya dake bane, saboda na samu wacce take da komai, ke kuwa ƙashi ne zai soke ni."
Watsa masa banzan kallo ta yi za ta wuce."Ni kike harara?"
"Abin da ya fi harara zan yi maka. Fatana na tara kuɗi na biya ka, wallahi na gaji da zama da kai, da na ci gaba da rayuwa a gidanka gara na yi a burtsuna."
Ta ce masa cikin ɗaya murya. Da sauri ya nufota cikin ɓacin rai ganin yadda take masa magana. Da sauri ta shige cikin ɗakinta ta kulle ƙofa."Mugu azzalimi na gama yarda ka duke ni." Ta ce tare da cire hijabinta ta shiga bayi don ta yi alwala jin an fara kiran sallah.
Tun tana tunanin lamarin da wasa yake yi, har ta cire ganin ya kafe dole ba za ta yi ba. Magana har gurin Baba suka je."Kallonta ya yi ya ce,"Tun da ya ce ba ya so, sai ki yi haƙuri ki bi maganar mijinki."
"Wallahi Baba, inhar ka ga ban yi ba, sai dai in bana raye. Farouk baƙinciki yake mini, kuma sai dai ya mutu."
"Baƙincikin me zan yi miki, bayan kin san abin da za ki samu ina da ninkin su?" Ya ce a harzuƙe kamar zai mareta.
"In kasan kana da su, ban ga dalilin da zai sanya ka damu kanka sai ka hana ni ba."
"Service ɗin ne na ce ba za ki yi ba, kuma ki bar mafarkin za ki yi aiki, wallahi ba ki isa ba."
Dariyar rainin wayo ta saki tana kallon sa."Wasa kake yi Faruk in har ka ga ban yi aiki ba, sai dai in na mutu, amma wallahi ko koyarwa ce sai na samu."
"Haka kika ce to mu zuba shege ka fasa." Ya ce mata sannan ya juya yana kallon Baba da ya yi shiru yana mamakinsa. Shi a kam harkan kuɗi ba zai goyi bayansa ba, saboda ya san ana samun kuɗi a service musamman yanzu da aka ce an ƙara musu, ya san in har ta yi zata tuna da shin watakila tafi shegiyar dubu goma ko biyar da yake basa, bayan ya gama tijarasa.
"Kana jin abin da fitsarrarriyar harka take cewa ko? Wallahi na yi dana sanin auren mace mara tarbiya irin ta, sam ba ka iya ba da tarbiyya ba." Ya ce tare da ficewa.
"Sai ka ɗauki mataki ba wai ka tsaya kana kumfar baki ba."Ta ce masa daidai lokacin da ya fice.
"Yaushe kika ko yi fitsara da rashin kunya Nasren? Ke da ada na sanki ko hannu aka sanya miki ba za ki cika ba?"
"Tun ranar da Ya Ahmad ya ɓace na san ba ni da gata sai Allah da kuma kaina. Tun ranar da na san cewa Baba, ba ka damu da halin rayuwar da na ke ciki ba. Tun ranar da na gane ko da Ya Ahmad yana nan ya raba aure da shi, inhar na ƙara wani auren na bari yana cusguna mini, sai dai ya sake ni, ko na ƙara masa hulɗi. Na zauna na yi wa kaina shawara na gane cewar kuka da haƙuri ba shi ne zai ƙwatar mini 'yanci ba. Kuma wallahi duk ranar da ya ƙara ce mini bani da tarbiyya, sai na goranta masa uwarsa da ta bar ƙasar ta tafi takaru neman kuɗi, don ta ciyar da su, shi ya sa shi ma ya tashi cikin rashin tarbiyya kamar ni."
Zare idanunsa ya yi yana girmama abin da ta ce. Shi kansa tsoro ta ba shi ganin yadda take magana ba tare da jin shakka ba. "Kar ki gaya masa haka, kin san lamarin ba zai yi dadi ba."
"Na gaji ne ya yi ta gaya mini, bani da tarbiyya sai ka ce shi yana da ita." Ta ce tare da ficewa daga ɗakin ba tare da damu da kiran da yake mata ba.
Tun daga ranar sai ya daina ba ta abinci ba ta damu ba, ta ci gaba da ciyar da kanta. Ta riga ta kammala komai jira kawai a fara posting ɗin su. Yayi maganar wayarta da ta siya a boye
A ranar da aka kira su don a yi musu tantancewa ba tare da shakkar koma ba ta shirya. Kasancewar da wuri za ta fita, don haka ta shirya Raihan ta yi wa Musaddik wanka. A falo ta zauna bayan ta gama soya musu dankalin Hausa ta sanya mata a jaka, ita ma ta ibi na ta.
Tana zaune ya fito da shirin fita Rashida na bayansa ɗauke da jakarsa. Ganin sa ya sanya ta miƙe. Tana lura da mugun kallon da yake aikata mata.
"Sai ka dawo honey." Ta ce masa tare da miƙa masa jakarsa.
Jawota ya yi ya rungume ta ganin haka ta kauda fuskarta."Ki kula mini da kan ki."
Far ta yi masa tare da ɗaga kanta.
"Farouk, zan je makaranta maganar service ɗin mu, a cikin watannan za a fara raba mu."
"Ai mun riga mun gama magana, na gaya miki ba da yawuna sai dai dai in za ki je ba da izinina ba."
"Ok to shikenan ba matsala na amince." Ta furta hankalinta a kwance tare da kama hannun yaranta za ta fita.
"Nasreen, tafiya za ki yi, a shirye kike duk abin da zan miki?" Ya yi mata tambayar yana kallon ta
"Eh," Ta ce za ta fice.
'in har kika fita gidan a ba...." Sai ya fasa furucinsa ganin babu nadama a fuskarta. Tuni ya san ta gaji da zama da shi saki take so.
"Ka ƙarasa mana tuntuni nake jiran wannan ranar, saboda babu amfanin aurenmu."
"Ba zan saki ba, amma wallahi in har kika bar cikin dakin nan sai na lahira ya fi ki jin dadi."
"Ko kashe ni za ka yi sai na je." Ta ce masa tare da fara tafiya da sauri.
Ganin haka ya iske jakarsa ya fisgota tare da kaura mata mari. Jakarta ya fisge ya fito duk takaddun ciki ya yaga su. Ganin haka ta sa ya ƙara ta yi kansa, ganin ya yaga mata takuddun da za ta kai."Mugu azzalimi wanda mugunta ce kawai aikinsa." Ta cakume shi tana faɗin haka.
Cikin fusata ya ƙara kai mata mari sannan ya haɗata da gini."Wawuya mara tarbiya kawai!"
'"Kai ne mara tarbiyya! Kai ma har wani tarbiyya kake da shi? Mahaifiyarka da ta tafi takaru ta barka shi ya sa ba ka samu cikakkiyar tare..."