Sashe 88
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amare ba tare da sanin su ba, angwaye suka yi musu viser zuwa honeymoon. Sai ana saura kwana biyu ya kawo mata tikiti jirgin Australia. Rungume shi ta yi cikin tsananin farinciki.
Zainab da mai aiki aka bari su kula da yaran. A ranar safiyar Laraba jirginsu ya tashi zuwa Australia. Mamaki da alja'abi ta rinƙa yi wai yau ita ce zata je honeymoon da miji. Yana maƙale da hannunta, duk da idanun Marwana da Ahmad bai sa ya ji kunya ba. Ko motsi ta yi sai ya kalle ta. Yadda yake nuna mata ƙauna har mamaki take yi.
A hotel ɗaya suka sauka mai suna; Four seasons hotel Sydney. Tun da suka sauka, wanka kawai Nasreen ta yi ta kwanta saboda gajiyar tafiya. Damir shi ma wanka ya yi, sannan ya ja bargon ya shiga ciki. Bacci sosai suka yi, sai da suka kwashe awa da rabi. Shi ya fara farkawa, sannan motsinta ya farkar da da shi.
Cikin magagin bacci, ya miƙa mata hannu da nufin ta zo su ci gaba da bacci."Baby please yunwa na ke ji." Ta ce tare da kama hannun ta miƙar da shi ya zauna.
"Ok, bari na yi waya a kawo abinci."
Wanka suka sake yi sannan suka haɗu a gurin cin abinci. Marwana ta fito da Ya Ahmad. A tare suka ci abincin suna hira har suka gama. Bayan sun gama ciki suka shiga, domin har wannan lokacin akwai gajiya a tare da su.
Sai da suka yi bacci gajiya, sannan suka fara ganin gari, sun je gurin shaƙatawa irin su;Stunning beaches da kuma Iconin cities har da Melbourne. Sun je guraren sosai musamman gidan tarihi irin su;Harper's Mansion Da Experiment Farm Cottage tarihi.
Hotuna kuwa har sun gaji da ɗauka. Wani irin soyayya yake nuna mata tamkar ya cinye ta. Tun da suka je sai dai su fita yawo su yi siyayya, sanann su zaga gari su dawo. Kodayaushe suna maƙale da juna, in ba bacci ba suna tare ana soyayya, domin ya sabar mata a jikinsa take zama. Kafin su dawo dai da ya cire duk wani kunya na shi da take ji, saboda sosai ya nuna mata soyayya har ya daina ba ta mamaki, ta gane yana daga cikin maza da suka bawa soyayya mahimmanci. Siyyayyar da yake yi kuwa tun tana taya shi zaɓe har ta hana shi. Sosai ya siya mata kaya musamman ƙanana. Su Marwana ma kullum suna maƙale da juna ana soyewa
Wasu mazan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 46
Wata ɗaya suka yi, sannan suka tattaro suka dawo. Nasreen daga ciwon gajiya sai kuma ya zama laulayi. Saboda cikin dare suna kwance Damir ya ji jikinta ya yi zafi sosai. Miƙewa ya yi sannan ya taɓa kanta. Mamaki sosai ya cika shi ganin ta takure guri ɗaya.
"Nasreen ba ki da lafiya, amma ba ki gaya mini ba?" Ya ce mata bayan ta farka.
"Zazzaɓi ne kuma na sha magani, amma kuma ya dawo."
"Gobe da safe za mu je ganin likita, kuma ya zama na ƙarshe, da za ki ji zazzaɓi ba ki gaya mini ba.
Kafin safiya jikinta ya rikice domin ta yi amai yafi sau uku. Damir rikicewar ya yi, ganin yadda take zazzaɓi tana kakkarwa kamar za ta jijjige gadon. Hankalinsa ya tashi sosai, domin bai taɓa sanin akwai masu zazzaɓi irin haka ba.
Amai kuwa duk a jikinsa ta yi, domin duk yadda ta so ta raba jikinta da shi, don ta yi aman ya ƙi. Bayan ta gama ya canza kayan jikinsa ya yi wanka. Ita ma wanka ya yi mata, sannan ya sanya mata kaya. Kiran sallar farko ya nufi asibiti da ita.
Gwajin farko aka gane tana ɗauke da cikin sati biyu. Ta yi mamakin murnar da yake yi, saboda kamar bai taɓa haihuwa ba, kawai sai ta ji ya manna mata kiss.
Zare idanunta ta yi, tare da kallon inda likitan yake cikin jin kunya, amma sai ta ga ya yi kamar ba ya ganinsu. "Babyna kina da ciki za ki haifa mini baby?" Ya furta cikin tsantsar farinciki tare da rungumeta."Please doctor a ɗaura mata drip ta sha wahala sosai."
"Ina ga ba sai an sanya mata ruwa ba, maganin da na ba ta sun isa."
"No don Allah ka sanya mata ruwa."
Ganin ya kafe sai ya sanya mata ruwan. Yana kusa da ita sai aikin sannu yake mata. Bacci ne ya kwashe ta, saboda har da maganin bacci ya buƙaci a sanya mata a ruwa. Kamar wanda ba a taɓa masa haihuwa ba, sai ya ɗauki waya ya shiga kiran dangi yana gaya musu. Kafin kace me duk sun zo asibitin, har da Marwana da Ahmad.
Nasreen farkawar ta yi, kawai ta ga suna zaune suna jiran ta tashi. Ganin ta buɗe idanunta duk suka yi kanta suna mata ya jiki.
Saura ƙiris! Ta saki kuka ganin yamaɗiɗi da ya yi da ita. Kallon sa cikin kunya ta yi da ya kama hannunta yana faɗin,"My wife kin tashi ya jikin?"
Saboda takaici ba ta amsa masa ba. Sai ta kalli Marwana da ta riƙe ɗaya hannunta. Cikin tsananin kunya ta kalli Mommy da take mata sannu.
Kunya sosai ta ke ji, amma duk suka zauna a asibitin har sai da ruwa ya ƙare aka sallame ta.
Magunguna ya ba ta, sannan suka shiga mota don su tafi. Daga asibitin gida suka rakata. Duk yadda Mommy take kula da ita, ta sanya an dafa mata fate saboda shi take so, amma Damir baya gani. Yana gefen inda take zaune. Ko kallon sa ta yi sai ya ce mata sannu.
A ranar ta ga gata sosai, domin rasa gane ta yi tsakanin Mommy da Marwana har da uban gayyar wanda yafi murnar cikin. Tun tana jin kunya har ta rage ganin yadda ko a jikinsu.
Mommy na zaune yake addu'ar Allah ya sanya ta haifi namiji, ya sanya sunan mahaifinsa. Sai kuma ya fara addu'ar Allah ya sa 'yan biyu za ta haifa. Mommy da mahaifinsu. Ita kam ta ga inda aka riƙe boko domin babu kunya, Mommy ta zauna suna maganar cikin. Saboda kunya da suke bata ƙaryar bacci ta yi.
Sai da daddare Mommy ta kom gida, Ahmad ma ya kawo su Mama, sannan ya ɗauki Marwana.
Nasreen kam ta ga inda ake maraba da ciki. Tamkar za su cinyeta haka suke yi. Kullum yana cikin siyo mata fruit da kayan ƙwalama. Duk da cewar gidan akwai, amma sai ya nunka domin duk ya fita sai ya siyo. Sai ta tuna lokacin cikin Raihan da ta rinƙa na cin Faruk ya siyo mata fulawa, don ta yi wainarta, amma ai sai Fadila ta fito mata. Nan kuwa Damir, bayan ya siyo da kanshi zai gyara ya kawo mata yana riƙon ta ci.
Laulayin wata ɗaya ta yi, ta warke tamkar ba ciki take da shi ba. Saboda ƙarfi sosai ta yi. Ta yi wani irin kyau da haske kamar ba ita ba. Cikin sosai ya sanya ta canza ta ƙara haske.
Shiryen-shiryen komawa aki ta fara, amma da ya daka tsalle ita da aiki sai ta haihu. Hankalinta ya tashi sosai domin tana so yin aiki, kuma a gida babu bin da take yi, saboda bayan Baba ya ƙaro mata wata, ga kuma Zainab da ya ɗauko ta dawo gidansu gabakiɗaya.
Cikin shagaɓa ta ƙarasa kan gadon, da ya zauna a gefensa yake ƙoƙarin sanya safa. Karɓa ta yi ta saka masa sannan ta ɗauki takalmin. A maimakon ta sanya masa, sai ta kalle shi kamar za ta yi kuka.
"Don Allah, ka bar ni na je aikina zaman gidan ya ishe ni. Ingawa ba shi a campany ballantana ka ce don shi ne za ka hana ni zuwa."
"Dama mahaukaci ne ni da zan barshi ya ci gaba da aiki a can? Yana kalle mini kyakkyawar matata yana haɗiye miyau."
Zare idanunta ta yi ta ce,"Dama kai ka kore shi? Sam ba ka yi masa adalci ba, domin ka haɗa masa zafi biya."
Jawota ya yi ya sumbace ta ganin yadda ta damu."Na tura shi gurin abokina a can aka ba shi aiki, sai ya tura mini na shi ma'aikacin. Ke ma kin san bai yadda za a yi na ƙyale shi, bayan ya yi takara da ni. Kin san yadda na ke ji a lokacin da na ke ganinku? In na koma gida bana iya bacci."
Dariya ta yi tuna lokacin, amma ya yi ta shan ƙamshi yana bonewa.
"Ki yi haƙuri, kar ki wahalar mini da yaro ki bari sai kin haihu." Ya ce yana shafa cikin nata da yake tamkar ba a sanya masa abinci.
"Cikin da ko wata biyu bai yi ba. Don Allah ka bar ni na koma aikina."
"Ok, bisa sharaɗin ba za ki wahalar mini da shi ba?"
Cikin farinciki ta rungume shi ta ce,"Eh na yarda."
"Ok, je ki shirya." Ya ce mata tare da kallonta.
"Husband nurina." Ta ce bayan ta manna masa kiss.
Murmushi ya yi, ya zauna yana jiranta. Shiga mai kyau ta yi kalar kayansa. Hakan da ta yi sai ya ji daɗi sosai.
Hannunta ya kama suka fita suna hira har gaban mota. Sai da ya buɗe mota gurin mai zaman banza, ta shiga sannan ya gyara mata gyalenta ya za gaya ya shiga cikin mota.
Tafiya suke yi tamkar ba za su je ba, saboda yadda yake yin tuƙin a lalace kasar wasu masoyan da suka haɗu a ranar.