Sashe 21
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗaki ta ya shiga ya yi tsaye a kanta."Yanzu ke saboda ba ki da mutunci ko? Kin zaɓi karatunki fiye da samun kwanciyar hankali a zaman aurenki?"
"Ka yi haƙuri ba ni da zaɓi ne. Ina son karatun, kuma ba zan iya watsa ma Ya Ahmad ƙasa a ido ba. Bayan wahalar da ya yi da ni."
"Aikuwa kin sayi rashin kwanciyar hankali a cikin rayuwar aurenmu, tun da har ni da nake ci da ke zan hana ki abu, amma ki bi maganar wani banza can. Wallahi Nasreen, in har na canza miki sam ba za ki ji dadi ba. Da kika ganni nan ba ni da kirki. Macijin sari ka noƙe ne ni."
Shiru ta yi ba ta amsa masa ba domin karatu ta dai babu fashi, wanda ta gane shi ne kawai gatanta a halin yanzu.
Ganin ta ƙi magana ya sanya shi hawa gadon."Ina sonki wallahi ina ƙaunarki. Ki zauna a gidana, ni kuma zan kula dake. Karatun wahalar da kanku kawai za ki yi. Mutane nawa suke da phd babu aiki?" Ya yi mata tambaye tare da rungimeta yana haɗa fuskarsa, cikin tsigar rarrashi.
Ba ta ce masa komai ba."
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 11
Ganin ta ƙi magana ya sanya shi hawa gadon."Ina sonki wallahi ina ƙaunarki. Ki zauna a gidana, ni kuma zan kula dake. Karatun wahalar da kanki kawai za ki yi. Mutane nawa suke da phd babu aiki?" Ya yi mata tambaye tare da rungumeta yana haɗa fuskarsa, cikin tsigar rarrashi.
Ba ta ce masa komai ba, har ya gama lallameta ya rungume ta yana sauke numfashi.
Washegari da safe saboda ba ta da lecture sai ƙarfe sha ɗaya zuwa magariba. Ganin bata fita ba, ya sanya ya yi tunanin ko ta haƙura ne.
Abinci ya ba ta ta yi musu mai rai da lafiya sannan ya fita.
Tana shara alert ya shigo wayarta. Dubu bakwai. Murmushi mai ɗauke da hawayen murna suka zubo mata, domin ta san da ace ana samun yaya irin Ahmad da mata da yawa ba su shiga cikin damuwa ba.
Bayan ta gama aikin ta yi wanka, ta shirya cikin shiga mai kyau ta wuce school.
Farouk kuwa don ya gane ko ta haƙura da karatun. Tun ƙarfe huɗu ya dawo gidan. Ga in ba ta a gidan ransa ya ɓaci. Zama ya yi tare da kunna kallo yana cika yana batsewa.
Yana zaune har magariba ba ta shigo ba. Ana sallame magariba ta yi sallama a falon cikin tsoro ganin yana nan.
"Da ga ina kike?"
"Makaranta." Ta ba shi amsa kai tsaye.
"A wannan lokacin?"
"Ƙarfe shidda muka tashi kuma rashin abin hawa ya sanya sai da na yi tafiya mai nisa na samu napep."
"Ke!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka.
"Wallahi ba zan lamunta da wannan tsinannen karatun na ki ba, da za ki gane da shi kina gantali."
"Wallahi babu inda na je." Ta ba shi amsa.
Kanta ya yi kamar zai shake ta domin ya rasa bakin magana. Ganin haka hankalinta ya tashi matuƙar gaske!
"Kin san Allah tun da kin zaɓi karatun nan, kin siya ma kanku tashin hankali a cikin gidan nan." Ya ce tare da jan tsuka ya fice daga gidan.
Raka shi da kallon mamaki ta yi domin yanzu ta rage tsoronsa. In dai a kan karatu ne ta shirya ta ɗauki duk abin da zai yi mata.
Ɗaki ta wuce ta je ta tube kayanta ta zauna kan gado tana tunanin mugun halinsa. Saboda wata ƙawar su ta kawo musu abinci. Sam ba ta yi tunanin cin abinci ba, ta yi kwanciyarta musamman da ba ta sallah.
Farouk ya ɗauki tsananin fushi kan karatunta, domin har sai da suka shafe sati ɗaya babu magana a tsakaninsu.
Cikin kuka ta sa ta da Ahmad amma ya ƙarfafa mata gwiwa tare da tura mata kuɗin da za ta rinka siyan abinci.
Ganin ta ƙi haƙura da karatun, babu yadda zai yi, kan dole ya haƙura suka ci gaba da zama.
Da daddare tana kwance ya shigo cikin kayan bacci. Kallonsa ta yi tare da tashi ta zauna.
"Sannu da shigowa."
"Yauwa." Ya amsa a gajarce tare da miƙa mata ƙwayar magani a hannunta.
Karɓar maganin ta yi tana mamaki domin ba ta gaya masa ba ta da lafiya ba.
"Kisha maganin?"
"Saboda me, lafiya ƙalau?"
"Eh, na sani umurni na yi miki a matsayina na mijinki, in kuma ban isa dake ba to."
Sororo ta yi da maganin da ba ta san na mene ne ba tana juya shi. Ta san cewa ba zai bata maganin mutuwa ba, amma rashin sanin fa'idar shan maganin ya sanya ta ƙi sha.
"Maganin tsarin iyali ne, saboda na ga ya kamata kisha. Ba mu gama fahimtar juna ba, sannan ga karatunki."
"Ni bana buƙata don ba zan lalata mahaifa ta a banza ba." Ta ce tana tura masa baki.
"Ni kuma ban shirya haihuwa ba, don ko ɗa daya bana buƙata a halin ya zu da na ke cin ganiyar ƙuruciyata ba. Sam ba zan aminta ki tara mini 'ya'ya ba. Su zame mini wahala a rayuwa."
"Gaskiya ni ba zan sha ba, saboda ƙuruciyata ba zan cuci kaina ba."
"Ba za ki sha ba?"
"Eh," Ta ba shi amsa kai tsaye tare da kwanciyarta.
"Nasreen, ki karɓi maganin nan kisha tun kafin zuciyata ta sa ya na aikata miki abin da bana fata."
Jin yadda ya yi maganar tsoro ya kamata, amma sai ta daure ta ce,"Ka yi haƙuri kawai! In har ba ka buƙatar haihuwar sai abi wata hanyar, amma ba zan cuci kaina ba. Kuma ban gaya maka don ina karatu ba zan iya rainon yara ba."
"Bana son haihuwar ce gabakiɗaya, domin ban ƙi ba na ƙare rayuwata ba tare da na haihu ba. Ko kina son na tara 'ya'ya kamata yadda mahaifinku ya yi na kasa ciyar dasu? Sam haka ba zai yiwu ba, domin ina da planning a rayuwata."
Hawaye ya wanke mata fuska."Haihuwar ta yi maka rana tun da ka gani a cikin 'ya'yansa ka aura."
Mari ya kawo mata sai ta kauce tare da ƙwala ƙara za ta gudu.
Ganin yadda ta firgita ya sa shi sausautawa ya kamota.
"Please, kisha maganin nan. Bana son yanayin structure ɗin jikinki ya canza. Kina da kyau Nasreen, komai na ki ya yi mini, amma wallahi da zarar kin samu ciki kina haihuwa za ki ragwaɓe."
"Haihuwar shi ne ribar aure. Annabi ya ce mu yi aure ne don mu hayayyafa ranar gobe kiyama ya yi alfahari da mu. Kuma yaran da ba ka so sune gatanka. Matuƙar ka ba su tarbiyya watarana sune za su tallahi rayuwarka."
"Bana bukata a yadda na tsara wa kaina ba zan jira yarana ba, har su girma su tallafi rayuwata."
"Ubangiji na juya lamura ba ka son me gobe zata haifar ba."
"Ba za ki sha ba kenan?" Ya yi mata tambayar cikin ɓaci rai.
"Ka yi hakuri ba zan cuci kaina ba" Ta ce masa.
"Tashi kisha maganin nan!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka.
Nasarar ɗauka mata marin ya yi ninya ya yi, wanda ta canyara ƙara ta dafe da ƙuncinta.
Duk yadda ya so ta sha ta ƙi. Takaicin haka ya sanya ya yi mata duka, sannan ya fice daga cikin ɗakin.
Kuka take yi sosai domin a yau ta gane ya aureta ne ba don yana sonta ba, dai don kyawu da surar jikinta. Tsoro da tunanin makomar rayuwar ta ya kamata, domin a haka yana wulaƙanta ta, in kuma kyawu da surar ta ya gushe ya zaman aurensu zai kasance.
Kuka take yi sosai domin ta san cewa rayuwar aurenta na cikin halin gaba kura, baya siyaki. Sai dai, ko kasheta zai yi ba za ta ci kanta ba. Ta yi kuka tana mamakin irin WASU MAZAN masu mugun son zuciya, su hana matansu haihuwa Don kawai su more jikinsu. Sai daga baya in sun ɓata musu mahaifa su yi aurensu.
Cikin ikon Allah ana wannan rikicin sai Nasreen ta fara ciwo. Da fari tashin zuciya da zaɓan abinci take yi. Daga bisani dai amai da kuma zuba miyau. Ga shi ta yi wani irin kyau sosai kamar ka sa ce ta ka gudu. Jikinta ko ina ya ciko ga shi ta yi kyau har ɗaukar ido take yi.
Farouk ganin hakan hankalinsa ya tashi domin ko ba a gaya masa ba, ya san ciki ne da ita, ganin yadda halittunta suka canza. Tun lokacin da ya ji canji a jikinta ya zargi ciki ne da ita, wanda bisa wannan dalilin ya sa ya shi siyo maganin hana ɗaukar ciki. Dana-sani da takaicin yadda zuciyarsa ba ta fara ba shi shawara, tun farkon auren su ya ba ta maganin ba, domin ya san da a wannan lokacin ne da take matuƙar tsoronsa za ta sha. Yanzu kuwa ta ga gadon baccinsa sam ba ta shakkarsa sosai.
Cikin dare ta kasa bacci sai amai take yi ta kasa cin komai. Ganin halin da take ciki ya tabbatar wa kansa ciki ne da ita.
"Nasreen, ciki ne da ke?" Ya yi mata tambayar yana tsaye a kanta cikin bayi da take ta kwara amai.
Ɗago idanunta ta yi a galabaice tana kallonsa. Rashin imanin sa take mamaki, ganin tun safe bata da lafiya, amma ya kasa yi mata sannu. Ya tsare ta yana tambayarta.
"Farouk, ka tausaya mini ka kai ni asibiti, wallahi ba ni da lafiya sosai."