← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 92

Sashe 2

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tun da ba ta da mutunci babu ruwan da ita in kaso ka kasheta."

"Na gaya miki Nasreen ba ta ji yarinya ce mara kunya da ɗa'a."

Harararsa ta yi jin abin da ya ce, ta ci gaba da cin abinta don ba ta da lokacinsa.

Hannu Rashida ta sanya ta ƙwace abincin tana faɗin,"Wallahi ba ki isa na yi girki ki ci ba, saboda ba ki da wannan darajar mijina na dafawa."

"Ki barta daga yau ita za ta rinka mana girki." Ya ce saboda sam girkinta ba ya mishi daɗi. Kafin ya aure ta yana tunanin akwai macen da ta fita iya girki, amma da suka yi auren girkinta ba ya yi masa test irin nata.

"An gaya maka abinci na dawo na rinƙa dafa muku?"

"No, ba zan yi miki dole ba, saboda kin san halina na ba ki girki sau ɗaya, in har ba za ki rinƙa yi ba, ba sake saninsa ta yi ba."

"In ka ga dama ƙarka bani abincin ka ga inshi zai sanya na mutu." Ta ce masa tare da miƙewa za ta bar falon. Galala ya yi yana kallonta. Tun da ta dawo take ba shi matuƙar mamaki. A zuciyarsa ya lailayo ashar ya dannawa Marwana, domin ita ta shigo rayuwarsu har take kwaɗaita mata kuɗi. Tana ganin cewa in ya rabu da ita, za su taimake ta. Ko da wuƙa za sanya kishi a maƙoshinta rantse ba zai sake ta.

Kallon Rashida ya yi da fuskarta yake a tamke. "Ki barta ta yi mana girki yamma bari na je na fito da abin da za a dafa." Ya faɗa yana ƙoƙarin juyawa. Wani banzan kallo ta watsa ma a lokacin da ya juya baya. Haushin yake ba ta sosai. Don bala'i da masifa gida daga ita sai shi, amma a ce kayan abinci a ɗaki da zai ije. Komawa ta yi ta zauna tana cika tana batsewa.

Da ya fito da taliya da makaroni ganin yadda ta canza fuska, sai ya wuce ɗakin Nasreen. Babu sallama ya tura ƙofar ya shiga. Kallonsa ta yi a sakarce ta mayar kan Musaddik da take shinfiɗar da shi.

"Ga shi ki kirga mana, kuma wallahi in har ba ki yi ba, ba za ki ci abinci ba."

Bata daga kanta ba ballantana ya yi tunanin za ta amsa. Ganin haka ya ja tsuka yana duba agogonsa."Lallai Nasreen ashe kwananan za ki koma ba haƙora." Ya ce tare da shiga cikin motarsa. Har ya fita sai kuma ya dawo tunawa da ita take buɗe masa get. Da fari hon ya rinƙa sakin mata, domin in har yana son ta buɗe masa jin yake mata.

Tana jin sa ta yi banza da shi, har ya gaji ya fito.

"Sai na ga uban da zai buɗe maka." Ta ce tare da zama kan stool ta ɗora ƙafarta ɗaya kan ɗaya.

Tura ƙofar ya yi cikin fusata."Saboda iskanci ina hon ba za ki zo ki buɗe mini get ba?"

Dariyar takaici ta saki tana kallonsa."Na ga yanzu mu biyu ne, kuma yau na dawo, ita take da girki ka je ta buɗe maka ranar girkina sai na buɗe maka."

"Yaushe kika samun ƙarin gwiyar mayar mini da magana? Ada akwai Ahmad wani lokacin ina shakkarsa, amma yanzu wallahi babu shi. Zan yi miki raunin da sai kin kwanta asibiti."

"Allah ya ba ka sa'a. Babu Yaya Ahmad, amma ni zan ƙwaci yancin kaina."

Har ya buɗe baki zai tursasata sai kuka ya fasa ya juya zuwa ɗakin Rashida. A ransa ya ji ya kamata ita ma ta rinƙa buɗe masa, kamar yadda take yi masa.

Tana riƙe da waya tana kiran Malam. Wayar ta shiga kenan ya amsa da sallama, sai ya tura ɗakin ya shigo. Da sauri ta kashe wayar ba tare ta yi amsa sallamar da malam ya yi mata ba.

"Haba Faruk what's this nonsense? Na gaya maka ka rinƙa sallama in za ka shigo."

"Ke!" Ya faɗa yana zare mata idanu jin abin da ta ce cikin tsawa."Ni da gidana sai an bani izinin shiga? Ban yi sallama ba da uban da ya..."

"No Faruk! Karka sake ka zagi ubana saboda ba zan ɗauki cin kashin da kake yi wa matarka ba, domin in ita shashasha ce ta zubar da kanta na san darajar kaina." Ta furta da muryar da bai taɓa tunanin tana da shi ba.

Kallonta ya yi cikin tsananin mamaki."Rashida! Ni kike gaya wa magana?"

"To sai na zauna ka zagar mini iyaye? Na lura kwanakin nan tun da muka yi watanni ka fara canza mini." Ta faɗa cikin kissa.

"Saboda na ina ɓoye abinci a ɗakina ko?"

"Eh, ai ka san hakan babu kyau, in har matarka tana sata sai aka ce maka ni ma sata zan yi?" Ta ba shi amsa a gatsale.

Nasreen ba ta taɓa satar mini abinci ba, saboda bana son albazaranci ya sa nake ɓoyewa, domin kuɗina ba kuɗin lukudu bane, da zan sayi abinci ki wulaƙanta. Na gaya miki gidana bana son baƙi, amma daga aurenmu mata nawa suka zo gidannan? Ga su tiƙa-tiƙa da su, so kike su cinye abincin da na siya."

Mamakin abin da ya ce sai ta kalle shi a birkice."Faruk yan'uwana kake zagi?"

"Ƙarya na yi ba tiƙa-tiƙa bane?"

"Lailai Faruk ban taɓa tunanin haka kake ba...."

"Ke bani da wannan lokacin zan fita ke ki buɗe mini get. Tun da kika tare nake tunanin za ki fara, amma da yake ba ki san abin da ke miki ciwo bai, sai kika bar ki ina wahala." Ya furta yana nuna mata hanyar fita.

"You are seriously jorking ko? Ni ce zan buɗe maka get? You must be jork." Ta ce masa cikin zallar mamaki tana kallon sa.

"Wasa nake yi miki in kin ɗauke ni abokin wasanni, ko kuma mahaukaci." Ya ba ta amsa fuska a ɗauke.

"Dole na yi maka tambayar, saboda na kasa gane zaman aure zan yi ko mai gadi ka ɗauko." Ta ce masa tana watsa masa kallon raini.

"Matata Nasreen ita take buɗe mini mota har ta wanke, in na dawo ta kwaso kayan, saboda ban ce ki fara ba sai yanzu?"

"Kace 'yar aiki take a gurinka. For God sake ina matarsa zan buɗe maka get na wanke maka mota? Da ma kana mini duk abin da na ke so ne, sai na yi maka don na faranta maka, Wallahi ba zan yi ba. Sam ba ka da sakin hannu dubi irin cimar da ake yi a gidanka."

Kallonta ya bita da shi, yadda take ɗaya masa murya, kamar ba ita da ya sani tana masa magana cikin taushi ba.

"Dole ki yi in ba haka ba za mu samu saɓa ni dake." Ya ce tare da juyawa zai koma gurin Nasreen ta buɗe masa.

"Faruk!" Ta kira sunan shi cikin ƙaraji, wanda ya sanya shi juyowa babu shiri.

"Look, let's face the reality. Ina son na yi magana da kai. Tsawon lokacin da muka yi aure, amma ban ji ka yi maganar za ka bani kuɗi na fara business ba."

Wata bazawara dariya ya saki tare da dawowa gabanta ya tsaya."Rashida ni zan ba ki jari ki yi sana'a? Kin san wa kike aure kuwa? To sana'ar ma ba zan amince ba, ballantana na ɗauki kuɗina na baki."

"Aikuwa ba za ta saɓu ɓa, saboda ka san matan yare, dole da sana'a muke rayuwa. Sam na tsari rashin kuɗi kuma kai komai na ka a maƙe..."

"Ok ruwan kuɗi zan rinƙa miki tun da magana nake suna zuba? Ki cire wannan a ranki."

"Ka san Allah dole sai na fita na nemi kuɗi, ko ka bani jari na yi sana'a ko kuma ka samar mini aiki."

"Duka ba zan yarda ba, aure kike yi don haka ba zan aminta."

"Wasa kake yi Faruk." Ta ce masa tana harararsa.

Mamaki ya kama shi tsayawa ya yi yana kallon ta. Ganin yadda ya tsaya sai ta matsa kusa da shi, ta marairaice fuska ta kamo sa."Faruk, don Allah mu tsaya mu fahimci juna. Gaskiya rayuwar da kake yi ba ta yi mini ba, ka bukatar hanyar da zan samu kuɗi. Ko namar miya ka siya sai ka faɗa mini kwanakin da zai yi..."

"A haka na ke rayuwata in kin ga za ki iya shikenan." Ya ce mata tare da juyawa zai fita.

"Ba zan iya ba gaskiya, you need to adjust." Ta ce masa tare da juya masa baya.

"To sai na ga uban da zai sanya na gyara." Ya bata amsa tare da juyawa zai fita.

Saboda takaici daƙuwa ta yi masa ta baya. A ranta tana jin in har ya cigaba da haka, za a haifi ɗa mata ido. Mamaki take yi yadda Nasreen ta iya zaman aure da shi har suka haifi yara biyu. A yadda take ji ba za ta iya komawa a gidansa ba. Mutum sai shegen maƙo da iya bakar magana.

Yana fita ta janyo wayarta Malam ta kira. Bugu ɗaya ya ɗauka."Wallahi mutun nan yana da taurin kai da maƙon tsiya. Sai ka yi mini babban aiki a kansa." Ta faɗa cikin takaici.

"Ƙarki damu kanki ki samu lokaci ki zo akwai aikin da zan yi miki mai ƙarfi a kansa."

"Yauwa Malam yana da makon tsiyar wallahi baya don fitar da kuɗi sai kace tare aka haife su."

"Ki dai zo kawai."

*_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 2

Yauwa Malam yana da maƙon tsiya, wallahi ba ya son fitar da kuɗi sai kace tare aka haife su."

"Ki dai zo kawai."

"To," Ta amsa tare da katse wayar tana takaicinsa.
Chapter 2 · 0% Book details