Sashe 89
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun ɓata lokaci duka isa kampanin. Da kanshi ya zagaya, ya buɗe mata motar ta fito, sannan ya kama hannunta suka fara tafiya kamar za su shige jikin juna.
Nasreen ɗaurewa ta yi, domin ta gane mijinta haka kalar tsarinsa yake. Ba ya jin shakkar nuna mata soyayya ko a gaban mahaifiyarsa. Don haka ta yi namijin ƙoƙari ta rage kunyar tana biye mishi.
Sosai ake kawo gaisuwa yana amsawa. Kowa kallon su yake cikin tsananin sha'awa. Da masu kishi, da baƙinciki har ma da masu murna kallon su suke yi.
Ofis ɗinsa suka shiga. Har za ta juya ya riƙe mata ƙugu."Matata ki kula da sharaɗinmu, domin in har kika wahalar mini da baby. Ko kika kasa ba ni kula da daddare na soke aikin,saboda na fi buƙatar ki kula da yarona da ni."
"Ba ka da matsala mijina."Ta furta tare da yi mishi kiss.
Har ofishinta ya raka ta sannan ya zaunar da ita. Bakinta ya sumbata."Ki kula da kanki ina sonki." Murmushi ta saki tare da ɗaga masa kanta ta kuma kashe mata ido.
Gashin kansa ya shafa alamun tsakon ya isa.
Da ya shiga ofis, sai ya kasa aiki yana tunaninta yana murmushi. Miƙewa ya yi, ya tafi zuwa siyo mata kaya maƙulashe. A lokacin da ya kawo dai ta kalle shi ta karɓa."Da ba ka wahalar da kanka ba, domin akwai abin da zan ci har mu tafi."
"Ki cinye wannan ki ɗora da wannan."
Dariya ta saki jin abin da yace,"Na lura so kake in zan fita sai an rinƙa cire ƙofa."
"So na ke ki samu kulawa ke da yarona." Yana zaune har sai da ya tabbatar ta ci ya koma. Daga ƙarshe zuwa ya yi, ya tafi da ita ofis ɗinsa ya kwashi Laptop ɗinta, da sauran files ɗin da take cike wa. Aikin da ba a yi ba kenan, domin surutu suka fara ana hira ana soyewa, sannan suka tafi gidan Marwana, da ta kira ta gaya musu ba ta da lafiya don ita ma ta samu ciki.
Sun jima a gidan suna kula da ita. Ahmad shi ma murna kamar zai cinyeta. Sun kula da ita har dare, sannan suka yi musu sallama suka dawo. Da daddare tana kwance ya shigo da kayan bacci a jikinsa. Kan gadon ya hau tare da ɗora ƙafafuwanta kan jikinsa yana matsa mata.
"Babyna kin ga yadda kullum kike ƙara kyau, wai mene sirrin?"
Dariya ta yi ta watsa masa kallo sai ta ce,"Kai ne sirrin da yaronka."
"Ai to bari na zo na ƙara sirrin na kuma kula da shi." Ya ce tare da janyota jikinsa.
Da ƙyar ta samu ta rarrashe shi ya barta ta je zuwa aikin, domin washegari cewa ya yi ba za ta je ba.
In suka je aikin rabi soyayya rabi aiki. Sai da ya ga aiki na son cin karfin Muhsin, sannan yake ƙoƙari, amma da sai dai ya je ofishinta ko ya ɗauko ta zuwa na shi.
Ranar Monday sun je gurin aiki, misalin sha biyu tana zaune hankalinta na kan aiki ya shigo."Yau kin manta da mijinki." Ya ce tare da kissing ɗin ta ya zauna.
"An sorry babyna aiki ne ya riƙe ni, kuma kaima na ga kun fita da Muhsin."
"Haka ne akwai matsala fa."
Kallonsa ta yi, sai kuma ta basar domin ta gane matsala."Mai ya faru baby?"
"Yunwana ke ji."
"Ok, mu je na raka ka, ka ci abinci bana son kana zama da yunwa."
"Nasreen ba wannan ba, Please kin san mai na ke nufi." Ya ce mata tare da kamo ta ya haɗata da jikinsa.
"A gurin aiki muke."
"Matata ce ke mu je ofis ɗin akwai komai."
"Don Allah k je ka yi aiki na lura rigima kake ji."
"Let's go home." Ya ce tare da kashe kayan wutan ofishin.
Kallonsa ta yi kawai ganin babu halin roƙon shi, domin tun da ya ce hakan ba ta da zaɓi.Soyayya suke sha sosai suna rainon cikinta.
Baba karayar da ya samu, ko da aka kwance ya samu naƙasa a ƙafarsa, domin ya zama gurgu da sanda yake tafiya yana jan ƙafar. Ganin lokaci guda halin da ya shiga sai ya fara nadama. Kuka sosai ya yi yana roƙon su yafiya, musamman Ahmad da duk abin da ya faru da shi, sam bai tausaya masa ba. Da ƙyar Damir da Marwana suka shawo kansa, amma har lokacin da ya yafe masa babu wannan soyayya tsakanin ɗa da mahaifi. Duk abin da zai yi, da Mama yake shawara sai dai ya ji a bakinsa.
Farouk ganin ya canza rayuwarsa, ta zama wani iri sai 'yan'uwan da mahaifiyarsa, suka fara ƙoƙarin nema mishi mata. Da farko funjire musu ya yi, sai da suka tabbatar masa da ya rasa Nasreen har abada, sannan ya amince, amma duk yarinyar da aka haɗasa da ita sai ya ce ba ta yi masa ba. Ko ya ce ba ta da haƙurin Nasreen.
Ganin suna ta haɗa shi da 'yan mata ya ƙi, kawai aka haɗa shi aure da Maimuna. Yarinyar ƙanwar Mamansa. Da fari ya ƙi kula yarinyar, amma haƙuri da ta yi dai ya ɗauki dangana ya rungumi matarsa, suna zaman lafiya.
Har yanzu ya kasa mantawa da ita. Ya san cewa yayi rashi na har abada, domin ba zai taɓa samun kamarta ba. Ko Maimuna da ya aura iya sakandiri ta yi, sannan ba ta da zurfin addini, amma tana da natsuwa. Natsuwarta ya ja hankalinsa har ya kula ta, saboda natsuwarta Nasreen da sanyinta yake son mace mai natsuwa.
Farouk ya canza domin Maimunatu na jin daɗin zama da shi. Sosai yake ƙoƙarin sauke haƙkinsa, domin har abinci yake ijewa a store kuma babu duka babu zagi, har zama yake yi suna hira kuma da ta samu ciki, duk abin da take so fito mata yake yi. A kodayaushe ƙoƙarin faranta mata yake yi, saboda Allah ya dubi zuciyarsa ya tuna ya yafe masa cutar da Nasreen daya yi. Yana son zuwa gurin yaransa kuma ya nemi yafiyarta, amma yana tsoron hukuncin da Damir zai ɗauka tun da an yi musu tsakani.. Yana dai zaman aure da ita, amma har yau babu macen da zai so kamar Nasreen. Ƙoƙarin neman cajin aiki ya yi, don ya bar garin na wasu shekaru ya manta da ita, kuma cikin ikon Allah ya samu suka tattara suka bar garin.
Nasreen cikinta ya girma sosai, don har ya shiga watan haihuwa. Ita kuma Marwana yana wata takwas. Nasreen cikin ta sanya ta yi ƙiba, sannan ya yi girma sosai. Tun yana wata bakwai ganin girman shi, suka yi scanning aka tabbatar musu da 'ya'ya biyu za ta haifa.
"Murna gurin Damir kamar zai yi hauka. Tun daga ranar ya sanya ta daina komai, kuma ta daina zuwa aiki. Sosai yake kula da ita.
Ranar safiyar Alhamis ta tashi da naƙuda. Cikin tashin hankali suka nufi asibiti. Tun suna sanya ran za ta haihu da kanta har suka cire, ganin wahalar da take sha. Damir sai hankalinsa ya tashi. Ciki ya shiga ya kama hannunta.
"Wash! Ya Damirr zan mutu ka yafe mini ka yi mini addu'a."
Jin abin da ta ce da ganin halin da take ci, sai hankalinsa ya tashi ya ce, "Ke ma tafiya za ki yi ki barni? Don Allah kar ki tafi ki barni kamar yadda Batula tayi."
"Please ka sanya hannu ayi mata aiki." Likitan ta ce tare da miƙa masa takkadda.
Hannu ya sanya jikinsa a mace. Mommy ta dafa shi suka fita. Marwana hankalinta ya tashi. Kuka take yi sosai, ganin wahalar da Nasreen take sha. Ahmad shi kansa da Mama jikinsu ya yi sanyi.
Addu'a sosai suke yi mata. Har an shiga da ita ɗakin tiyata Allah ya sauke ta lafiya, ta haifi mace da namiji.
Sosai likitocin suka yi murna. Gyara yaran aka yi, sannan aka fito da su.
Damir ba tare daya kalli yaran ba ya shiga cikin ɗakin."Sannu jarumtar matata." Ya ce mata tare da share mata zufan goshinta.
"Ya Damir." Ta kira sunan shi tana mika masa hannu cikin wahala, saboda ko haihuwan Raihann da yake na farko ba ta sha wahala haka ba.
Rungume ta ya yi, tare da manna mata kiss."Allah ya albarkanci yaran da kika haifa."
"Amin." Ta amsa hawaye yana ganganrowa.
Kwana biyu suka yi aka ba su sallama. Tun da ta haihu ya hana kowa ganinta, saboda ana buƙatar ta samu hutu kumburin ya sauka. Jariran kawai ake gani. Ko da aka sallame su gida babu wanda yake ganinta, domin suna ma ɗagawa ya yi, sai ta samu lafiya. Nasreen ta ga gata, don siyayyar da ya yi mata da yaran kamar ba shi cikin hayyacinsa.
Kowa a dangi dai kawo mata alkhari yake yi, yaran sun yi mata goshi sosai. Ita kanta Mommy kaka akwati guda ta yi. Su Mama da sauran dangi ba a barsu a baya ba, don Ahmad da Marwana kam sun yi bajinta suma. Tun da akayi haihuwar Marwana ta tare a gidan. Duk da cikinta ya tsufa, amma sosai take bawa yaran kulawa. Yara sun ga soyayya ta ko'ina. An yi musu huɗuba da sunan Moomy da mahaifinsu ana kiransu namiji Ubaidullahi mace Ubaidah. An ci an sha ranar suna. Maijego ta yi shiga na kece reni. Su Maman Muwaddat da Fadila an sha suna. Bayan mai aiki sai da ya ɗaukar mata wata.
Haihuwar Nasreen da wata ɗaya, ita ma ta haifo 'yarta mace bayan tasha baƙar wuya. Yarinyar kyakyawa sosai. Sunan Mama ta ci, ana kiranta da Sabrin. An ci ansha sosai Ahmad shi mata yi bajinta. Kaya kuwa har rasa inda za a sanya saka yi, domin kayan da Damir da Nasreen suka siya sun isa.
Sosai suke kulawa da yaran, da suke girma suna kiɓa ga su kyawawa.Suna da wata uku amma kamar sun yi wata biyar.
Cikin kula take rainon yaran ita da mahaifinsu. A lokacin da suka yi shekara kuwa babu inda basa zuwa. Shekarar su biyu ta yaye su, da yarinyar Marwana da kusan a gidanta take rayuwa, saboda yaran da take gani. Ta so ta yi hutu, amma ogan na ta babu wasa. Wata ɗaya da yaye ta samu wani cikin. Sosai ya nuna farincikinsa, don haka ta ci gaba da rainon cikin.