← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 92

Sashe 41

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariyar da ya gani a fuskar ta da yadda ta yi kyau ta ciko, ya sa shi jin haushi. Ganin tana cikin farinciki kenan? Bayan shi ta sanya shi cikin damuwar da ya kasa mantawa. Ransa ne ya yi ɓaki zuciyarsa na tafasa, sai ya ɗauki aniyar jefa ta cikin ƙunci kamar yadda yake yi. Zai takura rayuwarta kuma ya hana ta jin daɗi, ballanatana ta yi kyan da WASU MAZAN za su kalle ta su aureta. In har bai aure ba, shi kuma ba zai barta wani ya aure ta ba. Ruwan sanyi ya buɗe frij ya ɗauko tare da ɓalle gorar ya kafa kai. Sai da ya shanye ya yarda robar a trash.

Zagaye ofis ɗin ya yi, yana tunanin abin da zai rinƙa mata ya ƙuntata rayuwarta, ta ije aikin ba tare da Marwana ta zarge shi ba. Tun da Annur ya furta yana sonta ya san da gaske yake yi. Abun mamaki sai ya ji ya fara tsanarshi da raina ajinsa ganin ya rasa wacce yake so dai ita.

Saboda takaici kulle ofis ɗin ya yi, ya ce kar wanda ta shigo yana buƙatar hutu. Yana kwance yana ta ƙulla wulakancin da zai rinƙa mata, har bacci ya kwashe shi.

Nasreen zaune a ofis ɗinta hankalinta na kan wayarta. Idanunta sanye da gilas mai kyau. Hannayenta ƙunshi ne da Marwana ta kaisu aka yi musu, saboda bikin wata ƙawarsu da za su yi cikin satin.

Wayarta ce ta yi ƙara da sauri ta ɗauka ganin Mama ce. Jikinta har yana rawa ta ɗauka, saboda ta bar Raihan ba ta da lafiya."Hello Mama,"

"Nasreen ki dawo gida jikin Raihan ya rikice domin ya yi zafi sosai, yanzu na ƙara mata magani, ga shi babu kowa a gidan Zainab na makaranta da na kai ta asibiti."

"Subuhanallahi! Mama gani nan zuwa." Tana ƙoƙarin miƙewa bayan ta kashe wayar. Ɗaya daga cikin ma'aikacin mai suna Ingawa ya shigo da sallama.

Ɗan ƙaramin tsuka ta ɗan ja, saboda yana son takura wa rayuwarta. Tun da ta fara aiki yake shige mata da yawan zuwa ofis ɗin ta, amma sam ba ta son hakan, duk da cewar he is decent person kuma looking attractive, amma ita sam ba ta son wani namiji ya rinƙa shige mata, domin Faruk ya sanya ta tsani maza.

"Nasreen lafiya na ga damuwa ɗauke a fuskarki?" Ya tambaya da sauri ganin yadda innocent face ɗinta ya canza.

A hankali ta ɗago idanuta ta dora su a kansa jin tambayar da ya yi mata, sai kuma ta sauke su taka kallon wayarta"Ba wata damuwa bace, yarinyata ce ba ta da lafiya shi ne aka kira ni?"

Gabansa ne ya faɗi domin ya ɗauka budurwa ce, saboda jikinta babu inda ya nuna cewar ta taɓa aure."Are you married?" Ya yi mata tambayar cike da fargabar amsar da za ta ba shi, domin zuciyarsa ta gani kuma ta ƙyasa.

Kallonsa ta yi ganin yadda ya kashe ta da idanunsa. Wani iri ta ji game da hakan, amma sai ta yi saurin kawar da wannan tunanin ta ce masa,"Yes am married."

"Oh, sorry Allah ya ba ta lafiya." Ya ce tare da matsawa ya ba ta guri ta wuce .

"Amin,"Ta furta tana ƙoƙarin ɗaukar key ta kulle ofis.

"Na ga kin tayar da hankali ki ina mahaifinta ba sai ki kira shi ba?" Ya ce mata domin bai yarda da cewar tana da aure ba, domin kamar ya ji Khausar ta gaya masa ba matar aure bace.

"Baya nan ya yi tafiya." Ta furta cikin sanyin murya ganin yana son mata ƙure.

"In babu damuwa bari na kai ki tun da emergency ne."

"No, ka bar shi na gode." Ta ce masa tare da fita tana jiran ya fito

Kasheta da idanunsa ya yi, har sai da ta tsargu, sai ta kauda idanunta zuciyarta na tabbatar da zarginta.

Bayan ya fita ta kulle ofis ɗin ta je gurin Khausar."Please, ina son na je gida zan kai yarinyata asibiti."

Khausar ta kalleta fuskarta ɗauke da damuwar ciwon."Allah ya ba ta lafiya, amma ba zan iya ba ki permission ba, sai dai ki je gurin oga Muhsin ko Damir, saboda jiya ya sanar za a yi meeting akwai sabon system da zai kawo a ma'aikatar.

Gabanta ne ya yi wani irin bugawa tana kallonta."Na haƙura zan jira in an tashi na kaita." Ta furta cikin damuwa za ta fita.

"Nasreen, saboda me? Zai fahimce ki rashin lafiya ne."

"No, kar ki damu bar shi kawai." Ta ce tare da juyawa za ta fita.

Mamakin canzawar fuskarta da yanayin da ta nuna ya kamata.

"Ok, wallahi shi ya hana wannan meeting ɗin da za mu yi, na tabbata wani tsaurin zai tsaurara."

Ba tare da ta ce komai ba ta koma ofis ɗinta cikin damuwa. Ingawa da ya ga dawowarta ya shigo."Lafiya kin fasa zuwa ne?"

Ɗan firgita ta yi domin ba ta san ya shigo ba."Am sorry." Ya ce mata ganin yadda ta razana.

Da fari watsa masa kallon da ya rikita tunaninsa ta yi, ba tare da ta tanka masa ba, amma kuma sai ta buɗe bakinta cikin sanyin murya ta ce,"Na fasa zuwa sai an tashi zan kaita."

"Why yarinyar ki ba lafiya kuma mijinki baya nan, za ki ce sai an tashi? Aikin yafi miki yarinyar ne?"

Kasa amsa mishi tambayar ta yi domin tana cikin damuwa, sai kuma ta ce,"Na je na gaya wa Khausar ta sanar da ni oga Damir ya hana fita, dole da an nemi izininsa." Ta ƙarashe maganar tare da kiran sunan kamar an mata dole.

"Ki je ki yi masa magana ai ba zai hana ki ba, wani lokacin ne kawai yake very strict."

Girgiza kanta ta yi alamun a'a.

"Ok, tun da ba za ki iya ba, zan je na tambayar miki sai na kai ki gida ki ɗauko ta."

Zare idanunta ta yi tare da miƙewa ganin ya murɗa ƙafa zai je."Please, Ingawa don Allah kar ka je." Ta yi maganar kamar tana son kuka.

Kallon yake yadda ta bata fuskasai ta ƙara masa kyau sosai"Yarinyar ki ta fi aikinki mahaimmaci. Kin gani in har mahaifinta, ya ji kin kasa zuwa kaita asibiti ba za ku samu matsala ba?"

"Na fahhmce ka zan je da kaina." Ta furta cikin sauri da in'ina.

"Ok, mu je sai na ga kin shiga ofis ɗin."

Wani birkitaccen kallo ta yi masa, ganin yana son takurawa rayuwarta.

Hannunsa ya watsa yana faɗin,"Am just trying to help."

Fita ta yi daga ofishin zuciyarta na bugawa, ganin yadda ya takurawa rayuwarta.

Tana fita ya bi bayanta, saboda tsoron da ta nuna sai ya bi bayanta da murmushi yana kallonta.

A hankali take tafiyar, cikin tashin hankali da ta kai ofis ɗin har ta murda sai ta fasa, saboda rashin ƙwarin gwiya ofis ɗin Muhsin ta je, duk da shi ma tsoronsa take jii, amma ba kamar Damir da take hango tsanarta ƙarara.

Namijin ƙoƙari ta yi ganin in har ba ta daure ba, zuciyarta da take cike da tsoro ba ta za ƙarfafafa ta ba.

Da siririyar sallama ta shiga zuciyarta na bugu, yayin da bakinta ke ɗauke fatan Allah ya sa ba ya ciki, sai dai fatanta ba ta karɓu ba, domin shi ya fara juyowa yana kallonta, da hankalinsa yake kan tarin takaddun da suke cikawa.

Ji ta yi tsoronta ya nunku idanunta suka firfito, musamman kallon da ya watsa mata.

Muhsin jin ya yi shiru ba tare da ya amsa sallamar ba, sai ya kalli wacce take sallama. Shi ma fuskarsa babu yabo babu fallasa ya amsa.

Kasa ƙarasawa ta yi kuma ta kasa fita."Akwai sa'onki a ciki da za ki tsaya mana a kai?"

Damir ya furta zuciyarsa na harbawa. Ya rasa duk lokacin da ya ganta sai ya ji ya rikice numfashinsa yana sauka da sauri. Danganta hakan da tsanarta da ya yi, da kuma abin da ta yi masa na raba shi da wacce yake so.

"Um..eh..ina.." Ta fara in'ina ta kasa maganar

"Get out stupid!" Ya daka mata tsara yana faɗin haka.

Da sauri ta fice cikin hawaye. Ganin ta fita ya saki tsaki ya miƙe."I think I need to rest, mu bar aikin wani lokacin."

"To," Ya ce tare da fara tattara takaddun.

Nasreen cikin hawaye ta fita tare da jingina da ƙofar tana hawaye. Ga mamakinta sai ta ga Ingawa yana tsaye kusa da ƙofar yana kallonta. Ganin yadda ta fito dai ya fara tahowa gurinta.

Haushi da takaici ya cika mata zuciya ganin yana son ya takurata. Da sauri ta fara taku za ta bar gurin, amma sai ya tari gabata ya ce,"Nasreen, ba dai hana ki ya yi ba? Saboda na san yadda yake son 'yarsa, ba zai hana ki kula da ta ki ba?"

Tambayar da ya yi mata ya sa ta kalle shi kamar za ta kifa masa mari. Fara tafiya ta yi ganin yana son takura mata.

"Ok, tun da kin ƙi ba ni amsa bari na tambaye shi da kai..." Ya ce tare da buga kofar ofis ɗin.

Da sauri ta tare shi ta hanyar tokare ƙofar tana kallonsa."Don Allah kar ka je, na san cewa ba zai bar ni ba." Ta yi masa maganar cikin muryar shagwaɓa kamar za ta yi kuka.

Yadda ta yi maganar ya tafi da tunaninsa."Saboda me, akwai wani abu tsakaninku ne?"

Jin tambayar ya sa ta girgiza kansa da sauri."A'a babu saboda ban san shi ba sai anan, wataƙila akwai abin da yake damunsa ne ya sanya..." Sai ta yi shiru ta kasa ƙarashewa don ba ta san me za ta ce masa ba, tun da ba ta samu damar tambayar sa ba.

Kallon rashin yarda ya bita da shi, ganin haka dai ta juya za ta tafi."Nasreen," Ya kira sunanta da muryar da ya sanya ta juyo da sauri babu shiri.

"I found out that you are divorcee it either ki bari na yi masa magana, ko kuma ki ba ni address na gidanku na kaita."

Jin zaɓi da ya ba ta, ya burkita tunanin ta har ta kasa zaɓar ko ɗaya, amma daga ƙarshe sai ta zabi ta ba shi address."
Chapter 41 · 0% Book details