Sashe 45
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya musu cikin farin ciki. Ƙwasam Rashida ta samu ciki ta fara ciwo amai da laulayi. Nan take Faruk ya daka tsalle ya ce sai da a zubar, yayin da ta kafe kan baza ta zubar ba. Rigima sosai suke yi da shi, saboda cikin, suka rasa zaman lafiyar da suke yi. Tuni ya canza mata babu tausayi sai ma kyamarta da yake yi. Ga shi irin laulayin ta mai zafi ɗin nan, saboda tun da ta samu cikin ta daina wanka in har ta yi wanka ranar ba za ta kwana lafiya ba. Wani irin miyau take tarawa sosai a bakinta, saboda miyau ƙatuwar roba ta samu take tarawa. Idan ta zuba miyau Faruk dai ya ji kamar zai yi amai, domin sai gabakiɗaya kayan hajinnsa sun motsa. Ya san Nasreen tana laulayi har da amai, amma ba ya wuce sau biyu ko ɗaya. Ita kuwa tun da ta fara laulayin kullum da safe kafin ta ci komai sai ta yi amai, don ya zame mata ƙa'ida. Sabida aman datake yi ko cokali ta ɗauka baya iya taɓawa. Duk iƙirarin son da yake ma jikinta baya iya zuwa kasa da ita, domin ji yake tana wani irin wari kama da na albasa. Farouk duk ya takura kansa ko gidan zai shigo gabansa sai ya faɗi. Babu irin rarrashin da bai yi mata ba, kan a zubar da cikin, amma ta rantse sai ya fito duniya.
Tun daga lokacin ya ɗauke mata wuta, kullum cikin fada da jaraba yake yi. Ƙanwarta kuwa ya rantse sai ta mayar da ita. Tun tana tunanin wasa ne har ta ɗauka da gaske. Magani kuwa kullum dai an ba shi, amma a banza domin rashin mutunci yake mata gane da cikin. Mamakinsa sosai ta yi, saboda ya kamata ya tausaya mata halin da take ciki.
Ganin daga samun cikin, yadda ta koma sai ya yanke shawarar zubar da ciki. Ba tare da ta sani ba ya siyo maganin zubda ciki ya bata. Cikin dare ta tashi da wani irin azzabben ciwon ciki. Ihun da ta kurma ta ɗaka masa duka ya sanya shi zabura da sauri.
"Farouk zan mutu cikina marata."
Hankalinsa ya kwanta ganin cikin zai zuba. Da sauri ya kwashe ta sai sibiti. Ganin jini tun a hanya take ihu tana ƙunduma masa ashar, saboda ta san shi ya zubar da ciki. A ranar kuwa tasha kuka don azaba, saboda sai da aka yi mata wankin ciki. Ga shi cikin ya fara girma har ya kai wata huɗu.
Da suka dawo babu irin kalar zagin da ba ta yi masa ba, amma ya ji kuma ya shanye tun da burinsa ya cika.
Tun da ta warke ta hana shi kanta, saboda ta fahimci jikinta kawai yake buƙata. Tana kwance da daddare ya shigo bayan ya yi wanka ya kwanta a bayanta. Wani irin zagi da yarensu ta ƙunduma ta tashi zaune jin ya rungumota.
"Wallahi ka daina taɓa jikina, saboda babu amfanin zama da mijin da ba zai bar matarsa ta haihu ba."
"Tun da na zo da maganar aure na gaya miki ba na son yara. In har za ki samu ciki suka ɗari sai na zubar, saboda ina son Nasreen kafiyar da ta yi mini ya sa na yi mata wulanƙanci, in har kika kafe rayuwar da zamu yi sai ta fi nata wulanci."
"A shirye na ke duk abin da za kayi, saboda wallahi bazan zauna da kai sai da ka more jikina ba, ina gani na mutu ba tare da samu magaji ba, kuma dukiyar da kake tarawa, wa kake son inka mutu ya gada?"
Tambayar ya fusata shi cikin zafi ya kalle ta."Ok, dama kin aure ni don ki haihu ina mutu ku gaji dukiyar? To wallahi ba za ki haihu ba."
"Sake ni Faruk ba zan iya zama da kai ba." Ta ce masa cikin zafi.
Wata yar iskan dariya ya saki."Ai aurenmu babu daki dole kuma ki bi umurnina."
"Wallahi in har ba ka sake ni ba, sai na yi maka abin da b za ka taɓa mantawa da ni ba, sai na zame maka ƙadangaren bakin tulu!"
"Ni ma ƙwallon shege ne mu zuba mu gani." Ya ce tare da ficewa daga ɗakin
Tun daga ranar zamansu ya canza. Kowa ƙoƙarin ya cusgunawa junansu suke. Soyayya da zaman lafiya duk sai aka daina. Da ya shigo sai faɗa da zagi. Ganin haka Faruk ya daina bata abinci sai ya ga dama. Kamar yadda ya yi rayuwa da Nasreen ya so ya yi mata, amma sai ta nuna ba za ta saɓu ba. Da zarar ya fita za ta shiga ɗaki makullin da ta ɗauke ɗaya na sa ta ibi abin da take so ta dafa. In ya dawo ya yi ta bala'i da zage-zage. Gidan sun mai da shi na faɗa, kullum maƙota suna jin su su yi ta tsiya. Ga shi Rashida akwai murya in ta danna masa ashar sai anji. Gabakiɗaya rayuwarsu babu tsari.A haka suka ci gaba da rayuwar. Ganin ya canza makullin ɗaƙinsa sai ta saci ATM ɗin da ta cire naira dubu ɗari.
A lokacin da ya ga an yi debeting ɗinsa, tamkar mahaukaci ya dawo gida, da ya tabbatar da ita ta cire kuɗin. Yana zuwa tana kicin tana soya nama da ta siyo. Tana ƙoƙarin fitowa ya riga ta shiga. Idanu ya bi kayan da ta suyi da kallo.
"Da izinin uban wa kika cire kuɗin da kika yi siyayya?"
"Da izinin uban da ya aje ni, saboda wallahi ba zan zauna ka mayar da ki akuya, ba sai lokacin da ka ga damar ba n..."
Marin da ya kawo mata ya hana ta ƙarashe maganar. Ba tare da jinkiri ba ta wanka masa ita ma."Ke don ubanki ni za ki za ki mara?"
"Na rama nan gaba duka zan yi maka abin da ba za ka manta ba, domin wallahi in har na sanya karfi ba ka fi..."
"To shikenan bari mu gwada ƙarfin." Ya ce tare da kai mata hauri ya fara dukanta. Ba tare da jinkiri ba ta fara mayar masa. Da yake karfin namiji da mace ba daya ba. Ganin yana shirin illantata sai kawai ta wawuri abin tibi da aka yi kwalliya ta maka masa iya ƙarfinta.
Wani irin gigitaccen ƙara ya saki dai ga shi a ƙasa kwance jini yana zuba."Yau na yi maganin dukan mata da yake yi. Na kassara idanun sai na ga idanun, da za ka ƙara gani har ka duki wata mace." Ta furta tana haki domin ita ma ta ji jiki.
Taɓa shi ta yi ganin baya numfashi. Da sauri ta ƙara girgiza shi. "Kai kar ya zo ya mutu!" Ta ce cikin tsananin tashin hankali.
Da sauri ta ibo ruwa ta watsa masa, amma ko motsi bai ba. Ganin haka xuciyarta ta ayyana mata lokaci ya yi da ita za ta tsotsee ƙwallon mangwaro ta huta da ƙuda. Yana cikin jinin ta sanya hannu ta ɗauki ɗan makullinsa ta shiga ɗakinsa. Duk wata ƙaddara ta shi su da ta ɗauke takaddun. Hatta ATM dinsa duka ta kwashe tun da ta san pin. Babu tausayi ta barshi cikin jini ta gudu. Bayan ta rubutawa ƙaninsa Usman text ya zo ya taimaka masa.
A lokacin da ta tura bata hannunsa. Har sai da aka kira sallar magariba sannan ya ga tsakon. Cikin tsananin tashin hankali ya nufi gidan nasa.
Tun da ya get ɗin gidan a buɗe gabansa ya faɗi. Da sauri ya shiga cikin gidan tana kiran sunansa.
Jin shiru babu wanda ya amsa hankalinsa ya tashi. Yana ƙoƙarin shiga cikin dakinsa, da ya ga komai an bincike sai ya ji yayi tuntuɓe da abu. Duk juriyarda sai da ya tsorata. Da sauri ya kalli gurin.
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Ya Farouk!"Ya duƙa yana girgiza shi cikin tsananin tashin hankali. Ganin baya numfashi, ga jini sosai a gurin har ya daskare, ya sanya shi kurma ihu yana neman taimako.
Jin ihun maƙota suka fito zuwa cikin gidan."Mai ya faru da shi anya bai mutu ba, ina matarsa?" Tambayar da mutane suka rinƙa yi kenan. Ganin tambayar ba ita ce mafita ba, da sauri aka kwashe shi zuwa asibiti.
Ko da aka kai shi sun ɗauka ya mutu, amma sai suka gane yana numfashi. Da kyar suka samu ya farfaɗo sannan aka bukaci jini, saboda ya zubar da jini da yawa.
Ɗinkin gurin da ya ji ciwonka yi masa. A lokacin ya farfaɗo, amma ba shi cikin hayyacinsa sai surutu yake yi. Allah ne ya taimake shi saura kaɗan idanunsa su taɓu, domin sun yi wani irin na kamar jan gauta saboda dukansa maka masa abin da ta yi a gurin.
Sai da ya kwana ya wuni sannan ya san inda yake. Yana dawowa hayyacinsa ya fara kiran sunanta yana zaginta."Ni za ki kashe? Wallahi in har na warke sai na yi ajalinki." Ya ce cikin ƙara yana son ya tashi.
"Ahalin yanzu ka kula da lafiyarka ba ka ganin ɗinkin da aka yi maka?"
"Ina Rashida?" Ya tambaye shi cikin zafi.
Yaya Asiya da take gefensa tana share hawaye ta ce,"Ta gudu bayan ta kwashe komai na dukiyarsa, motarka kawai ta bar maka."
Zare idanunsa ya yi kamar zarrare. "Ina wayana kuɗin da yake account ɗina wayyo miliyoyina."
Ƙarar da ya saki ya sanya na zabura cikin tsananin razana. To fa Faruk Capacity yau dai ranar babu sa'a . Rashida ina soyayyar za ki yi masa haka. Kin san dai yadda Faruk yake da kudi.
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 24