Sashe 65
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wallahi ba haka bane kina raina, kawai rashin mutuncin da Faruk ya yi mini ya sanya na yi nesa dake, kuma kin san matan sojoji kullum cikin yawo muke."
"Duk wannan ba hujja bace na kare kanki. Tun lokacin da kika karɓi tranfer kika daina kirana ko a waya."
"Mu bar wannan tashin-tashin yanzu nadawo gareki. Waje Baban Sayyid ya fita, shi ne na dawo gida zan yi masters Mamana take gaya mini ai kun rabu da Faruk."
"Wallahi kuwa ke dai bayan ba ki na shiga jarrabawa." Kwashe duk abin da ya faru ta yi ta gaya mata.
"Kai Faruk dan iskan duniya ne, mugu shi ne yanzu har yana da idanun da zai ƙara kallonki."
"Hmmmmh! Ni ma na yi mamaki sosai ba ki ga yadda ya dawo ba."
"Aini wallahi matarsa ta yi mini da zan gaya sai nayi mata kyauta, saboda abin da ya yi ya cancanci fiye da haka. Kiriƙiri ya raba tsakaninmu bayan ni ya sanya na yi masa hanya, wallahi in na tuna hakan da halin da kike ciki sai kaji kamar zan haɗiye kaina na mutu, saboda har da hakan ya sanya na fita daga rayuwarki."
"Allah ya kawo mini ƙarshe ai na huta da azabarsa."
"Amma ya kamata ki auri Damir ɗin nan, saboda yana sonki kuma ki sakawa Marwana."
"Ina mamakin yadda ake cewa yana sona. Ya Damir ya tsane ni sosai in ya gani kinga yadda yake mazurai yana bata fuska?"
"Zafin kishi ne da kuma irin tasa kalar soyayyar kenan."
Shiru kawai ta yi ba ta ce komai ba. Hira sosai suka yi suna tuna rayuwar baya da irin wahalar da suka sha. Sun jima suna hira, sannan ta yi mata sallama ta tafi bayan ta yi mata alkawarin zuwa gidansu.
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 34
Shiru kawai ta yi ba ta ce komai ba. Hira sosai suka yi suna tuna rayuwar baya da irin wahalar da suka sha. Sun jima suna hira, sannan ta yi mata sallama ta tafi, bayan ta yi mata alƙawarin zuwa gidansu.
Washegarin ranar Monday Damir yana zaune a falo Muhsin ya shigo. Turus ya yi ganinsa yana kallon news ba tare da ya shirya zuwa gurin aiki ba.
"Ya Damir ba za ka je aiki bane?"
Ɗaga masa kansa ya yi hankalinsa naka tibin."Maganar kayan nan fa za ka sanya hannu..."
"Please ka kula da komai daga yau, saboda ina son zan yi tafiya zuwa Dubai."
Mamakin abin daya faɗa ya kama shi."Amma kuma baka gaya mini ba? Kuma na ga tafiyar ni zan yisai kuma nan da wata biyu."
"Ba wancan tafiyar bane, ina son na yi nesa da gida ina buƙatar na saita kaina. Zan je in sha Allahu da daddare jirgin mu zai tashi, kuma ban san lokacin da zan dawo ba, domin zan iya wata goma shekara ko fiye..."
"Haba Yaya saboda me za ka je waje ka yi wannan daɗewar, wa zai kula da campanin?" Ya masa tambayar yana zare ido cikin mamaki.
"Kai za ka kula da kampanin, ya kamata ka saba da kulawa da shi kai kaɗan, saboda watarana zai iya kasancewa babu ni, kasancewar ba a san gawar fari ba."
"God forbid Ya Damir in sha Allah ni zan riga ka mutuwa."
Murmushi ya yi, tare da dafa shi yana jin tafiyar ita ce mafita, saboda in har zai zauna watarana sai dai su ga ya yi bunga.
"Ka daure ka kula Marwana ma za ta iya tayaka kulawar. Ta girma yanzu tun da har tana ba da zaɓin waɗanda za a ɗauka."
"Waye zai yi tafiya kuma saboda me?" Hajiya da ta shigo, tana sauraren abin da suke cewa ta yi musu wanan tambayar.
"Ya Damir ne kuma wai bai san lokacin dawowarsa ba, domin ya ce he might stay long."
"Saboda me zai tafi wata ƙasa ya bar campany?"
"I don't know Mommy you can ask him." Ya ce yana watsa hanunnsa cikin damuwa.
"Ina son na je na huta ne, sam bana jin daɗin Najeriya kuma na riga na gama komai yau in sha Allahu zan tafi." Ya ce bata amsa ba tare da ya ji mai da za ce ba ya haye sama.
Kallon juna suka yi Muhsin ya bi shi sama. Tura ƙofar ya yi tare da shiga ya hange sa a gurin kayansa, ya haɗa kai da wadrop ɗinsa hawaye yana bin fuskarsa.
"Saboda Nasreen za ka bar ƙasar?"
Da sauri ya ɗago, cikin razana yana ƙoƙarin goge hawayen da ke fuskarsa ba ya son ya gani.
"Saboda me zan bar ƙasata, kan wata mace wacce ta ruguza farincikina?"
Ba tare da ya amsa mishi ba, ya ƙaraso kusa da shi, sannan ya kai hannu ya dafa kafaɗunsa."You love the girl. Da gaske kana mata mahaukacin so, ba ka sani ba ya kamata ka sani. Ya Damir kana sonta sosai and you have to go to her. Swallow you pride and seek love. Na gane kana sonta sosai, kuma kishi ya sa za ka gudu ka bar ƙasar ka. A maimakon ka tsaya, ka shiga cikin manema a fafata da kai har ka yi nasara."
"I didn't tell you that I love her k...."
Stop pretending Ya Damir! Wallahi babu kaffara sonta yake ɗawainiya da kai da kuma kishin ta. Tun ranar da ta fara aiki a campaninnu na gane kana sonta, soyayya sosai wannan dalilin ya sa kake shiga tashin hankali in har ka ganta da wani. Kana son abu amma kana nisanta kanka da shi? Sai yaushe za ka cire girman kai da izza ka gaya mata that you adore her, or are you going to hide it until when she got married. Is that what your intention?"
Kasa magana ya yi, domin ya san cewa duk bin da ya faɗa gaskiya ne. Juyowa ya yi, da idanunsa da suka rine suka yi jajir ya kalle shi, ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya kasa.
"You love her, amma kana ganin kamar furta mata zai zubar da ƙimarka? Ya Damir saboda me za ka yadda zuciyarka ta cutar da kai saboda tunanin ka mara tushe. Eh komai ya faru ta sanadinta, amma kuma ka tuna mutum bai isa ya kashe wani ba. Nasreen tana da hankali da natsuwa sannan da ilmi. Ba ta da hayaniya irin kalar macen da kake so, ka kuma samu sai girman kai ya hana ka furta mata?"
"Da gaske ina shiga ciki tashin hankali da firgici duk lokacin da na ganta da wani. Tun ranar da na ganta kwance a gadon asibiti na ji wani lamari dangane da ita, amma sai na danganta jin da tausayi. Bayan lamarin ya faru dai na ke jin ƙunci in na tuna tana gidan wani da jinina a jikinta. A tunanina abin da ya faru ya sanya nake jin haushinta, ashe kishinta na ke yi. Sai dai bani da courage da za iya tunkararta."
Kallon mamaki ya yi masa."Ya Damir kamar ba ɗan boko ba? Ina wannan hot kalamai da kake gayawa Anty Batula? Shi za ka yi amfani da su ka sace zuciyarta, kuma na tabbata za ta kauda kowa ta zaɓe ka, saboda halaccin da Marwana ta yi mata, don haka kar don tsohon mijinta ya dawo ka yi zuciya ka bar ƙasar. Kaura da kasar ba na ka bane, saboda ko da ka je dole zuciyarka za ta hana ka zukuni ka dawo."
Shiru ya yi cikin tunanin, yadda zai iya kallon ta ya gaya mata ƙauna. To amma kuma in ya rasata zai yi da ƙaunarta da yake yi. Wata zuciya ta ba shi shawarar gwadawa.
"Go for her adore her and pampered her."
Kalaman da gaya masa, sai ya ji wani ƙwarin gwiya har zai iya fara tunkararsa. Ganin ya yi shiru sai ya karɓi jakar kayan da yake haɗawa."Please ka samu soyayyarka da kanka kar ka bari su Mommy su sani ballanatana ka ci arzikin Marwana. Nasreen za ta iya mallaka maka zuciyarta saboda Marwana, amma bana son haka ya faru. Ka tsaya ka zama namiji samu ƙaunarta sannan ka aure ta."
Kama shi ya yi ya rungume yana faɗin."Na gode da ka gane bin da yake damuna, kuma ka bani shawara in sha Allahu zan yi matuƙar ƙoƙarina don na mallake ta."
"I wishe you all the best." Ya ce tare da ɗaga masa hannu alamun fatan nasara.
Murmushi ya yi tare da shafa bayansa. Ya daɗe sosai a cikin ɗakin yana ƙarfafa shi, har sai da zuciyarsa ta samu kwarin gwiya sannan ya fita.
Da ya fita kwanciya ya yi a kan gado, tare lumshe idanu yana tunanin yadda zai fara tunkararta da soyayya. Duba ga yadda yake ɗaure mata idanu yana mazurai. Shafa kansa yayi cikin jin kunya tun kafin ya fara.
Yana zaune ya yi oder na kaya masu kyau, da yawa da takalma hatta agogo dai da ya siya da kuma turare, domin so yake ya je da mutuncinsa, kallo ɗaya ta faɗa tarkon ƙaunarsa ba tare da ya sha wahala ba.
Mamaki sosai suka yi, a lokacin da Muhsin ya sanar musu da ya fasa tafiya. Sai dai, duk tambayar da suka yi masa bai gaya musu dalilin fasa tafiyar ba. Duk da haka sun ji daɗi duk da cewar Mommy ba ta shiga sabgarshi saboda kafiyarshi.
Da safe bayan ya yi wanka, ya daɗe yana ƙyalƙyale jikinsa kamar mace. Dama Damir akwai iya ɗaukan wanka, tun lokacin da Batula ta rasu ya daina gayu sai dai ya sanya kaya ya fesa turare.