Sashe 60
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da aka shiga satin bikin gidan ya fara kacamewa. Su Marwana babu zama kullum sai sun fita. Anko ta yi musu kusan kala biyar, duk wani events sai da suka yi ankon shi.
Ana saura kwana uku bikin, ta shirya ta zo gidan Mama ta roƙe ta ta bar Nasreen, ta koma gidan su har a gama biki.
Tana zaune a falo da Mama suna hira Nasreen ta dawo daga aiki. Tare suka shigo da Ahmad da ya dawo daga unguwarsu, duba gyaran da ake yi wa tsohon gidansu.
Ganinta da sauri Nasreen ta ƙarasa tana murmushi, ta kama hannunta tare da zama kusa da ita. Shi ma cikin murmushi ya zauna gefen Mama, yana kallon Marwana, da shigowarsa ya sanya ta ije ɗanwaken da take ci.
Ahmad kallonta ya yi, cikin wani kalan yanayi ya riga ya gama yarda tsananin ƙaunar da take yi wa ahalinsa ya sanya mishi matsanancin sonta kamar zai haɗiye ta. Wani irin sonta ya kamu da shi, mai kashe jiki da saukar da tsaƙo a ƙwaƙwalwa.
"Sannu da shigowa Ya Ahmad." Ta ce masa cikin murya mai taushi.
"Ƙanwata kina lafiya?" Tambayar da ya yi mata ya sanya ta ɗago idanunta, cikin jin kunya ta saci kallon sa, ganin ita yake kallo sai ta ƙara takura.
"Ɗanwake ake ci babu ta yi?" Jin abin da ya ce sai ta miƙa masa filet ɗin ta ce,"Mama, ta iya girki sosai musamman dambu da ɗanwake, har da abin da kika yi nayi ta santi Mama, mene ma sunan shi?" Murmushi ta yi tana kallonta cikin tsanannin ƙaunarta kamar Nasreen take jinta, a ranta so take ta yi wa Ahmad umurnin aurenta ko da ace baya sonta, ballantana ta san babu wanda zai ƙi ta.
"Ɗangauda."
"Yauwa Mama shi ina son shi sosai. Da na koma har Mommy na gaya mata ina ta santi."
"Allah ya sa sun yi miki waigi ba ki faɗi ba."
Dariya ta yi tare da rufe idanunta jin abin da Ahmad ya ce.
"Aiko zan yi miki da wara na sanya ki kaiwa Hajiya." Mama ta ce tana kallonta.
"Mama don Allah na zo roƙonki, kan Nasreen ta ce gidanmu akwai bikin yarinyar ƙanin mahaifinmu da za ayi, da zarar an gama bikin za ta dawo."
"Kai haba ai mun zama ɗaya, Ubangiji ya ba da zaman lafiya ya nuna mana naku, ni ma in sha Allahu zan leko."
Shiru ta yi ta kasa cewa komai.
Hira suke yi, amma sai duk ta takura ganin yadda Ahmad ke kashe ta idanu. Mama ce ta miƙe ta ba su guri, suka ci gaba da hira su uku. Nasreen ta miƙe,"Bari na rage kayan jkina yunwa na ke ji."
"Ma za ƙanwata grabs something to eat."
Tana miƙewa Ahmad ya bi Marwana da kallo. Ji ta yi kaman yana kallonta ta ɗaga idanunta. Da sauri ta sauke nata."Marwana ni ba za a gayyace ni ba?" Ya furta cikin sanyin murya yana shafa kansa.
"Kai Yaya, in na gayyaci Nasreen ai dukanku nagayyata. Ba ka ji Mama ta ce za ta zo ba sai ku zo tare."
"Na ƙi wayon nawa gayyatar na musamman na ke so."
"To shikenan you are invited."
"Good sis ki ba ni contact naki sai na kira ki, saboda ke zan zo ma bikin bana son Nasreen ta sani."
Da sauri ta ɗago idanunta tana kallon sa jin abin da ya ce."Yes laifi ne ina zo gurin ki ba ta sani ba?" Ya ƙarashe maganar yana shafa suman kansa idanunsa a kanta.
"A'a." Ta ce a hankali saboda wani irin kunyarsa da take ji.
"To a bani numba."
Babu musu ta karanta masa ya sanya a wayarsa."Thanks, bari na kira ki sai ki yi saving nawa ko."
Ɗaga masa kanta ta yi daidai lokacin da kiran ya shigo. "Sai na zo bikin." Ya ce tare da miƙewa da sauri jin Nasreen za ta shigo falon.
Kallo ta bishi da shi tana jin yadda gabata yake faɗi.
"Sorry na barki ke kaɗai." Nasreen ta furta lokacin da ta shigo falon. Hira suka ci gaba da shi, daga nan ta kwashi kayanta suka tafi.
A lokacin da suka isa gidan sai gabanta ya rinƙa faɗuwa, tuna ranar da ta shige shi da kuma dalilin shigar.
Cikin sanyin jiki ta shiga cikin ɗakin da yake da mutane ana hayaniya. Sallama suka yi Marwana ta ja hannunta suka ƙarasa gurin Mommy.
Duƙawa tayi cikin girmama ta ce,"Ina wuni Momi?"
Fuskarta a sake ta amsa, sannan suka shiga cikin ɗakin Marwana. Sun jima a ɗakin suna duba ɗinkunan da ta yi musu. Cikin farinciki take duba kayan tana mata godiya.
Nasreen kwanciya ta yi saboda ta gaji ga kuma kunyar Mommy da take ji. Ko da aka yi sallah a cikin ɗaki ta yi sannan ta kwanta ta ja wayarta tana ta chatting abin ta. Aka yi ishata yi sallah sannan ta kwanta.
Marwana da ta zo bacci kasa bacci ta yi, da ta rufe idanunta sai fuskar Ahmad ke mata gizo. Numbarsa ta lalubo da ta yi saving da Ya Ahmad tana gani. Da sauri ta kalli wayar ganin kiransa na shigowa. Kasa ɗauka ta yi domin a tunaninta ko flashing ta yi masa, ba tare da ta sani ba, amma da ya gama kiran ta duba, sai ta ga don ra'ayin kansa ya kira ta.
Kallon Nasreen ta yi, da take bacci saboda tsoron ko ba ta yi bacci ba, sai ta miƙe zuwa falo ta zauna. Ɗaukar wayar ta yi, tare da kangawa a kunninta ta yi sallama cikin sanyin murya.
Daga can ɓangarensa ajiyar zuciya ya saki."Da fatan ban tashe ki daga bacci ba?"
"A'a Nasreen ce ta yi bacci dai ƙila ka kira ne tana bacci."
"Kiran na ki ne ba ita ba, saboda mun yi waya kafin ta yi bacci na tambaye ta ke ta ce kina ɗakin Mommy."
"Ok, ina wuni?" Ta furta tana juyawa kan kujerar.
"Kina lafiya ya hidimar biki?"
"Alhamdulillah Yaya Ahmad."
Shiru ya yi yana tunanin abin da zai ce mata."Kin ɗauke mini kanwa shi ya sa na kira ki don mu yi hira." Ya furta haka ba tare da shiri ba, domin ya rasa mai zai ce mata.
"Kai Yaya kwana uku za ta yi fa?"
"Haka ne don kene kawai. In na zo bikin me za ki bani?"
"Duk abin da kake so Ya Ahmad ai ka wuce ƙarfin komai a gurina?"
"Har da zuciyarki?" Ya yi mata tambayar da sai da ta zauna.
Jin ta yi shiru sai ya sake ajiyar zuciya ya ce,"Marwana ina sonk za ki bani zuciyarki? Tun ranar da kika yi wa Nasreen kyautar lapton ki samu matsayi sosai a zuciyata, a lokacin ban yi wani tunani ba, saboda na san cewa babban goro sai magogin ƙarfe, amma ga shi yau Allah ya canza komai. Ina da dukiyar da zan iya aurenki, sannan ina yin digiri a online."
Tsintar kanta ta yi da kashe wayar, domin ta kasa ba shi amsa. murmushi ta saki sai kuma ta rungume wayar tare da ba ta kiss."Ya Ahmad yana sona? Allah na gode maka ashe ni rabonsa ne shi yasa ka raba ni da Ya Ashaman?" Ta yi tambayar cikin farinciki tare da miƙewa ta shige daki.
Kasa bacci ta yi, don haka ta hau online. Ahmad da yake kan online ɗin yanar dariyar abin da ta yi. Fatan shi ta Gandi yi maganar tun da ta kasa bashi amsa. Ganin ta hau ya yi mata magana. Sai ta ɗan saki suka ci gaba da hira ba tare da ta amsa mishi ba.
Murna sosai yake yi, domin ganin yadda ta saki da shi suna hira ya san ta aminta da shi. In har ya same ta zai yi murna, saboda ya san ba shi da matsala tsakaninta da danginsa.
Numbarta ya duba sannan ya tura mata da alert na kuɗi, musu yawa ta opay ɗinta."Ayi mini kitso da ƙunshi sai na zo biki."
Cikin farikciki ta karanta tsakon tana murmushi. Da kyar ta samu bacci ya kwashe ta da tunanin sun yi aure.
Washegari da safe da suka tashi bayan sun yi sallah da azkar. Da gari ya sha sai suka miƙe don su haɗa breakfast. Ita da Nasreen suka shiga kicin. Suna aikin Nasreen tana kallonta da kusan hankalinta yana kan wayarta. Da ta fara fere ɗankalin turawa sai ta saki ta duba wayarta."Wai hala kuɗi za a tura miki?" Ta yi mata tambayar tana kallonta.
"A'a mai kika gani?"
"Ban yadda ba saboda tun ɗazu kike ya kallon waya, ko kin fara soyayya ne?"
"Wataƙila hakanne I'm in love with extraordinary guy." Ta furta tana murmushi.
"Ai to, kuma sai ba za ki gaya mini ba?"
"Akan me? Na ga lokacin da kika fara soyayya da Ingawa babu labari sai dai na gane, don haka yanzu sai ki gano da kanki."
"Shikenan idan ta yi wari za mu ji, amma shi kuwa wane mai sa'an ne ya dace zuciyarki? Bayan kin rasa Ashman na ga mutane da dama suna ta kawo ƙoƙon bara, amma ba a basu dama ba?"
"Saboda wannan daban yake a cikin maza, kuma na san na yi dace zai kula da ni."
Baki ta kama cikin tsanannin mamaki."Yaushe kika haɗu da shi har kika yi masa wannan shedar?"
"Ban sani ba daga ganin farko na sheda daban yake cikin maza."
"Hmmmmh!" Kawai ta ce tana mamakinta a ranta ta yi mata farinciki duk da ta so ta haɗata da Ahmad, amma ganin ta samu wanda yake sanya farinciki sai ta daure abin ta ce,"Lallai kin zurma da yawa."
"Sosai kuwa. Bari na je na tambayi abin da Mommy za ta yi break da shi."
"To," Ta masa sannan ta fita daga kicin ɗin. Hankalinta ya ɗauki gurin suyan tana ta juyawa.
Damir ne da kayan ɓacci ya sauko kasan yana hamma, saboda tunani bacci bai ishe shi juya ba. So yake yashi'a coffee na shi na ƙa'ida sannan ya ya yi exercise.
Tura kicin ɗin ya yi yana faɗin."Marwana Please coffee ki haɗa...."