← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 92

Sashe 74

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ingawa kuwa fushi sosai ya ɗauka da ita, duk yadda ta so ta fahimtar da shi ta kasa, domin ta fahimci da gaske yake sonta. Fushi sosai yake yi da ita. Yanzu haka sun tashi daga meeting ɗin ta fito ita da Hajar da Khausar.

"Anty Nasreen ashe soyayya kuke yi da Ya Damir?"

Tambayar ya sanya ta gwalalo ido ta ce,"Ni?"

"Don Allah stop pretending, ki yi kamar ba ki sani ba, ko mahaukaci ya kalle ku ya san soyayya kuke yi."

Za ta ba wa Khausar amsa, sai ta kasa ganin Ingawa ya nufo su fuskarsa babu rahma.

"Ina taya ki murna sosai domin kin yi dace Nasreen, ba ni cikin masu miki baƙinciki Allah ya baku zaman lafiya." Khausar ta furta tana kallonta.

Kasa amsa ta yi, ta sauke numfashi daidai lokacin da ya ƙaraso."Ina son magana dake." Ya furta tare da matsawa gefe yana jiranta.

Kallonsa ta yi su kuma ta kalli su, Hajar da suka yi mata alama ta je. Bayan ta fara tafiya sai Khausar ta ce,"Ihu yake bayan hari. Irin su Ya Damir a guri sai ya ce dole sai ya soyayya? In dai ba so yake ya rasa aikinsa ba, ya kamata ya yi backup."

"Wallahi kuwa domin ina ganin irin mijin indiya mai zan yi da na Nigeria." Dariya suka kwashe da shi sannan suka fara tafiya.

"Nasreen mai ya sa za ki ɓoye mini gaskiya? Shin abin da idanuna suka gani a ɗakin taro gaskiya ne?" Ya yi mata tambayar cikin tsananin tashin hankali.

"Ya Ingawa, har yanzu ba soyayya muke yi kuma wallahi bai furta mini ba."

"Zan iya rantsuwa da Kur'ani, kuna son junanku ko da ace ba ku furtawa juna ba."

Shiru ta yi, ta kasa ce mishi komai ba."Nasreen ina sonki wallahi ina masifar sonki. Kar ki kalle ni a matsayin mai son kansa da na kasa haƙura, na bar masa domin ya cancanta ya aure ki. Don Allah ki aure ni wallahi za ba ki farinciki sosai."

Yana wannan maganar Damir ya zo zai wuce. Ganin haka sai ya ƙara murya yana faɗin kalamai na soyayya. Ransa ya ɓace jin abin da yake cewa.

"Ke Nasreen mu je ina son ganinki." Ya furta cikin ɓacin rai tare da tsayawa ba tare da ya tafi ba, yana yi masa mugun kallo sosai. Kishi ɗauke a idanunsu.

Ganin haka ya sanya ta kalle su, sai ta fara tafiya da sauri ofishinsa. Sai da ta wuce ya yi masa kallon gargaɗi ya wuce yana huci.

Tsayawa ta yi a ofishin na sa cikin damuwa. Sosai take tausayin sa domin ta gane da gaske yake sonta.

A birkice ya shigo idanunsa sun canza sosai. Tsanannin kishinta ya rufe masa ido. Sosai yake jin haushinta, domin abin da yake mata ya kamata ta daina kula kowa. Ko da ace ba gaya mata yana sonta ba, ya kamata ta gane mahaukaci ne a kan sonta.

Ganin yadda ya shigo yana numfarfashi, ya sanya ta ɗan razana tana matsawa, ganin yana matsota.

"Mai ya sa za ki zaɓi ki rinƙa hurting ɗina? Why ko kina nufin ba ki san halin da nake ciki ba?" Ya yi mata tambayar, lokacin da ya tsaya kusa da ita ta tamkar zai rungumeta.

Tsoro ya kamata sosai jikinta ya kama rawa, musamman ganin yadda ya ke huci. Da kusantarsu ta yi yawa, domin suna jin bugun numfashin juna. Kasa magana ta yi, saboda yadda ƙamshin turarensa ya cika hancinta.

"Ya Damir."

"Kina son kice mini baki gane abin da yake zuciyata bane?" Ya katseta da wannan tambayar. Ganin ba ta ce komai ba sai ya fara faɗin." Na yi tunanin saboda abin da ya faru tsakaninmu nake jin haushi ina ganki da wani, amma na gane tsananin kaunar da na ke miki. Ya sanya na ke jin kishin haka. In har kika ce za ki rinƙa kula su, ya za ki yi da ni da soyayyarki ta mayar da ni mahaukaci?"

Zare idanunta ta yi, ganin yadda ya cire girman kai yana ta sakin batun soyayya.

"Wallahi ina sonki na yi tunanin zan iya cikawa Batula alƙawarin, amma sai na gane zan iya hakanne kawai idan kina gidan mijinki. Tun ranar da aka sanya miki jinina in na tuna jinina yana yawo a jininki, sannan kina auren wani ji na ke kamar zan yi hauka. Ina son ki Nasreen kallon farko asibiti na ji abu da game dake, amma sai na basar domin matar wani kike. Ki ba ni dama na auren ki. Na nuna miki bambanci a tsakanina da WASU MAZAN domin na bambanta da su. Zan shayar dake kalar soyayyata. Zan mayar dake tauraruwa kuma zinariya a cikin mata. Ina buƙatar mace a rayuwata. Macen ma ke Nasreen zan canza duniyarki."

Yadda lokaci guda ya canza, ya dawo mata mutumin da bata sani ba,sai ta tsorata ta duƙa kasa don ta samu gudu ta tsakon hannunsa, amma sai ya duka shima ya ƙara kusancinsu.

"I dore You Nasreen! Will you marry me?"

Tambayar da ya yi mata, sai da ta ji kamar duniya za ta faɗo mata. Yau ita ce Damir yake roƙonta ta aure shi. Tsaddaden mutum ɗan gayu kamar sa. Yau shi ne a duƙe a gabanta cikin yanayi na shauki yana gaya mata ta aure shi. Rayuwa ta canza mata haƙika ta ba ta zaɓi mai kyawu. Tana cikin wannan tunanin sai ta ji ya kama hannunta. Da sauri ta kalle shi cikin tsananin razana.

Ba tare da ya kula da furgicinta ba ya ce,"Wannan zoben a ranar da zan auri batula na siya mata, da shi na tambaye ta in tana sona. In har kina sona ki amince na sanya miki a yatsunki." Ya ƙarashe maganar yana ƙoƙarin sanya mata.

Ta kasa cewa komai sai ta kalle shi cikin mamaki. Yana shirin zura mata aka turo ƙofa. Da sauri ta ture shi tare da janye hannunta.

Muhsin da ya shigo da sallama, sai ya yi dana sani ganin lamarin da yake faruwa. Cikin tsananin jin kunya ya koma yana faɗin,"Subuhanallahi! Am so sorry." Ya juya zai fita.

Kafin ya fice Nasreen da take jin kamar za ta nitse saboda kunya ta yi waje.

"Ya Damir don Allah ka..."

"Is ok, karka damu." Ya ce cikin jin kunya yana shafa kansa tare da jan tsaki.

Ganin yadda ya yi sai ya koma cikin takaici, domin shi kansa ya ji haushin ɓata musu show da ya yi. Sai kuma ya fara dariya ganin yadda ya yi mata rumfa."Hummmm su yaya baban soyayya tun kafin auren har an fara wannan."

Nasreen kuwa, da ƙyar ta samu ta kai kanta zuwa ofis ɗin ta. Tana shiga ta sanya makulli tare da jingina da ƙofar tana ganin abin da ya faru kamar a mafarki. Ƙamshin jikinsa da take ji a kayanta ya tabbatar mata da ba mafarki take yi ba. Mamaki sosai take yi, domin furta mata yana sonta ya zaman mata bazata.

Zama ta yi kan kujerar, tare da rintse idanunta tana son tuna lamarin da ya faru. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta saki, sai ta lumshe idanunta ta buɗe.

"Ashe haka ya ke. Dama akwai maza da suka ɗauki mace zinariya? Idan har na ce bana sonsa na yi wa kaina ƙarya, to amma ya zan iya kallon tsabar idanunsa na gaya masa ina sonsa? Yana da sexy eyes da kuma ƙwarjinin sosai. Ya Damir ya haɗu ta ko wace sigar da zai dace a soshi." A zuciyarta take ta wannan tunanin. Da sauri ta koma ƙara duba wa ko ta sanya ɗan makulli, jin kamar ina tahowa ofishinta domin a halin da take ciki ba kowa zai iya gane wa.

Ta daɗe a gurin kafin ta saita natsuwarta, har ta samu ta saita natsuwarta. Zama ta yi ta fara aiki zuciyarta cike da shaukin ƙaunarsa.

A ranar saboda kunya ka sa fita zuwa cin abinci ta yi, domin ta san zai iya zuwa gurin. Ko da su Hajar da Ingawa suke kiranta, sai ta yi musu ƙaryar azumi take yi. Tana zaune har aka fita break suka dawo.

Damir haka shi ma ya wuni sukuku. Yaso ya ji ra'ayinta game da soyayyarshi, domin in har tana son shi ba za a ɗauki lokaci ba, za a yi aurensu. Ya huta da su Ingawa da suke son haukatar da shi.

Yana ta dakon ya ga ta fito, amma har aka gama break ba ta fito. Wayarsa ya janyo yana murmushi ya danna layin ta. A ƙalla sai da ta yi ringing sau biyu, sannan ta yi namijin ɗauka tare da sallama.

"Na je ɗauko Raihan Zainab ta kaisu gida."

"Eh ni ma sun kira ni sun gaya mini." Ta furta mishi maganar cikin sanyi.

"Ok," Ya ce don bai yarda ba, ya san cewa ta sanya su ɗauke ta don kar su haɗu.

"Ya maganarmu saboda da gaske na yi. A shirye na ke da na aure ki in har za ki amince." Kasa ce masa komai ta yi zuciyarta na bugu tamkar ana buga ganga.

A lokacin da aka tashi dai da aka gama tafiya sannan ta fito. Damir kuwa da ya fita sai ya tsaya a waje, domin ya san cewa ba za ta fito ba in har bai tafi ba.

Yana ganin ta fito, ta tafi sai ya bi bayanta a hankali sai da suka yi nisa ya fara mata hon. Jikinta ne ya kama rawa ganin motarsa yana binta. Ta rasa yadda za ta yi kan dole ta gangara ta yi parking, ganin haka ya yi parking na shi motar.

Kashewa ya yi sannan ya fito yana taku har ya ƙaraso gareta. Da sauri ta ɗauke kanta da suka haɗa idanu.

"Nasreen," Ya kira sunanta yana ƙoƙarin haɗa ido da ita."Ki bani amsar tambayar da na yi miki."

Ta kasa ce musu komai kuma ta kasa amsa mishi.Ganin haka ya ɗube ta ya ce,"Shurin yana nufin kin amince?"

Tambayar da idanunsa da ya kafe ta da su ya sanya ta ƙara jin kunyarsa sosai. Gane da ya yi tana cikin mata sosai masu kunya, sai kawai ya buɗe motar ya fita yana murmushi.
Chapter 74 · 0% Book details