Sashe 63
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yauwa Ahmadu ɗan albarka, zo ka ga wannan ɗan iskan mijin Nasreen ada ya zo wai ganin yayansa."
Ahmad cikin taƙun kasaita ya ƙaraso. Jikin Baba har rawa yake yi lokacin da yake tahowa inda suke. Fuskarsa tsoronsa bayyane yana yi kamar zai ɗuka masa.
"Wane yara kake da shi a gidan nan?" Ahmad ya yi masa tambayar yana kallon sama da da kasa yana mamakin yadda ya rame.
Daurewa ya yi ya cire tsoro da firgicin da yake ciki, don kar Ahmad ya gane ya ce,"Please kar mu yi kamar bamu san juna ba, Raihann da Musaddik na zo ganinsu yarana da muka haifa da matata Nas...."
"Kul! Ka tofar da miyau bakinka, domin Nasreen ta wuce matsayin da zaka kira ta da matarka, da ma cewa ka yi ada zan iya saurarenka."
"Eh amma ina da..."
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Wh
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 33

"Eh amma ina da yara da ita ko, kuma ka san ina da haƙkina na matsayin uba? To su na zo gani a fito mini da su." Ya ƙarashe maganar, yana ɗan daga murya ganin kallon ƙaskancin da yake musu.
Ahmad kallon sa ya yi, duk da rayuwa ta canza masa, amma girman kansa da isa yana nan."Ba ka da yara a gidan nan, saboda wulaƙanta mahaifiyarsu da su da ka yi. Ba za ka gansu ba don baka cancanci zama ubansu ba."
"Wallahi karya kake yi, don in dai ni na yi silar zuwansu duniya, sai na gansu in ina buƙatarsu dole hukuma ta ƙwatar mini su."
"To shikenan na ga uban da zai karɓar maka su, mara mutunci tijararre kawai, saboda baka da kunya har ka iya takowa ka ce ka zo ganin yaranka?" Baba ya furta cikin tsawa yana zare masa ido.
Ahmad taku ya yi zuwa gabansa ya zare masa ido."A yanzu kasan ni ba sa'an yin ka bane Faruk.Idan a da ka yi mini abin da ka ga dama, yanzu kuwa zan rama, saboda daga kallona ka san Ubangiji ya yi mini arzikin da kake mini gorin shi. Ina da kuɗi in har ka ce zaka yi mini wulaƙanci, wallahi sai na sanya a ɗaure ka har igiya ta yi rara, ko da ace zan rasa abin da na mallaka ne."
Jikin Faruk ya yi sanyi tsananin tashin hankali ya kama shi. Ganin yadda suke masa musamman Baba. Kasa magana ya yi sai kawai ya fara tafiya ya shiga cikin motarsa.
Da ka tsaya, ka ga yadda zan wulaƙanta ka mara mutunci kawai, kana tunanin kai kaɗai Allah ya ke so."
Ahmad sai da ya ga bar kofar gidan, sannan ya kalli Baba da yake ta kumfar baki ya ja ƙaramin tsuka ya shige motarsa.
Faruk sai da ya bar kofar gidan sannan ya tsaya jiran yaron da ya rako shi. Kiransa ya yi sannan ciro naira ɗari ya ba shi."Mu je na mayar da kai." Ya furta cikin tashin hankali yana tuna Ahmad yadda ya koma.
Sai da yaron ya shigo sun fara tafiya ya kalle shi ya ce,"Ka san wa ya siya musu gidan nan?"
"Ahmad ne da ya dawo ance yana da rijiyar haƙo zinare, to sai dai kawai ya ibo ya siyar."
Tsaki ya ja jin abin da ya ce."Ina Nasreen ƙanwarsa?"
"Anty Nasreen ai tun kafin ya dawo ta samu aiki. Ance kamar ƙawarta na makarantarsu ta samar mata aikin, kampanin yayanta. Ba ka ga yadda ta yi kyau ba, domin tun kafin yayanta ya dawo ta canza."
Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi. Shi da yar tunanin zai zo ya gansu a cikin wulaƙantacciyar rayuwa, amma sai ya kurɓi ruwan mamaki. Hankalinsa ya tashi ya rasa wane tunani zai yi. Wani irin ƙaunarta da sonta ya ƙara bijiro masa tun kafin ta ganta. Yaransa da ya wulaƙanta su yake son gani.
"Fita ba hanyar ku zan yi ba." Ya furta wa yaron cikin ɓacin rai saboda labarin da ya gaya masa. Yaron ya fice tare da rugawa da gudu ba tare da ya fahimci halin da yake ciki ba.
A maimakon ya koma gida, sai ya wuce binciken inda Nasreen take aiki, saboda a ransa ya ji ba zai iya haƙura da ita ba, ya san tana da haƙuri za ta kula shi ko don su Raihann, musamman da in ya yi mata barazana da kwace su.
Bayan ya gama binciken, ransa ya ɓaci da ya ji a campanin su Damir take aiki. Wani irin ɓacin rai ya kama shi. Take kishi ya rufe masa idanu har ba ya iya ganin abin da ke gabansa.
Daga gurin binciken kasa koma gida ya yi gida. Kampanin ya je ya samu wani guri ya laɓe don ya ganta.
Ya daɗe a gurin yana jiran su tashi. Da lokacin tashi ya yi. Duk motar da ta wuce sai ya kalle ta. A lokacin da ta fito da motar. Har ta fara tafiya sai ta tuna ta yi mantuwa. Da sauri ta yi parking ta fito daga cikin motar.
Tafiya take cikin yauƙi, tana karkaɗa makullin mota har ta shige ciki. Farouk da ya yi toxali da ita ji ya yi kamar zai yi hauka. Da fari sam bai gane ta ba, domin gani ya yi kama ita kamar ba ita ba. Mace ya gani mai jiki kalar wacce yake so. Abaya data sanya ya ƙara rikitar da shi. Ga takalminta da jakarta ma kyau. Tamkar balarabiya haka ya gata koma, bambancin su kawai ita ba ta da haske sosai.
Ji ya yi ƙasa ba zata iya ɗaukarsa ba, har sai da ya jingina yana jin wani irin tashin hankali mara muslatuwa. Ya goge idanunsa ya fi sau nawa don ya tabbatar da ita ce.
Yana gurin cikin tsanannin tashin hankali, har ta dawo ta shiga cikin motarta. Ji ya yi kamar ya bita, domin har ya fara taku sai kuma ya ja ya tsaya.
"Nasreen ce haka?" Ya yi ma kansa tamabayar yana mamakin abin da ya canza ta. "Ko dai supplements da nayi ta kawo mata don ta sha, ta ƙi sha ne yanzu ya sha ta yi kyau don ta burge Damir ya so ta?" Ya yi wa kansa tambayar cikin rashin hayyaci. Idanunsa suka rufe saboda tsananin kishinta. Ji ya yi kamar ya buɗe idanunsa ya ga bashi a cikin duniyar. Da ƙyar ya samu ya shiga cikin motar ya bar gurin.
A ranar sai dai bacci ɓarawo ya ɗauke shi domin kasa bacci ya yi. Daya rufe idanunsa, ita yake hangowa cikin shiga ta alfarma. A ransa ya gama yanke shawarar ba zai taba yarda Damir ya aureta ba matuƙar yana raye. Ya sanya wa kanshi zai je ya fafata don ya dawo da matarsa. Sai ya yi na'am da hakan musamman da zuciyarsa take karfafa mishi, dole ta dawo in ya yi mata barazana da raba ta da su Raihan. Sosai yake son ganinsu ya ga yadda suka koma.
Washegari da safe, da ya tashi gidan abokinsa ya wuce ya nemi ya ba shi aron kuɗi. Babu musu ya ba shi sannan ya wuce kasuwa. Kaya sosai ya siyawa kansa da turare na fara zuwa biko, saboda yadda ya ga Nasreen ta koma dole yana buƙatar ya yi updating kansa.
Da ya dawo daga siyayyar, ya zauna yana dubawa sai abin ya ba shi mamaki, cewar yau shi ne yake siyayyan kayan don ya burge Nasreen. Ya tuna da yadda take son ya yi kwalliya ya zauna a gida. Wasu hawayen nadama duk gangaro masa da ya yi wautan sakinta, ina ma ace ba sakinta yayi ba, kawai ya tura ta gidansu. Tashi ya yi ya shigar da kayan, sannan ya zauna ya shiga kogin tunanin, yadda zai fara shawo kanta.
Nasreen ta dawo aiki yana bakin get tana yin hon. Maigadi ya taso ya buɗe mata shiga da motar bayan ta gushe shi. Data fito daga motar ta yi sallama cikin falon. Raihann da Musaddik suka rugo suna mata oyoyo.
Mama da Ahmad suna zaune, tun da yazo suke mamakin zuwansa da abin da ya ce.
"Babu haddar yamma na ganku a gida?"
"Umma, malamin haddar babansa ya rasu shi ne ba a yi ba." Raihann ta ce tare da karɓar jakarta.
"Allah Sarki! Ubangiji ya jikansa." Tare suka haɗa bakin gurin amsawa da Amin.
Sai da ta zauna ta natsu, har ta ci abinci mama ta kalle ta. "Kin san yau Faruk ya zo gidan na..."
Da sauri ta miƙe jin sunan wanda aka kira."Ya zo yin me?" Ta zare idanu tana kallonsa.
"Ya zo ganin yayansa."
"Gaskiya Faruk ba shi da kunya." Ta ce sai hawaye ya zubo mata, take gani tsoron karya raba ta da yaran.
Hannunta Ahmad ya kama ya zaunar ganin yadda ta razana. "Ni kaina abin ya bani mamaki, sai bayan ya tafi na sanya ayi mini bincike, ashe matar da ya aura ta gudu bayan ta fasa mishi kai ta kwashe dukiyarsa."
Zaro idanunta ta yi, cikin tsananin mamaki da firgici. "Ikon Allah Rashida ta yi masa haka?" Ta yi tambayar cikin mamaki tana tuna irin zama da suke yi.
"Farouk ya ga bala'i, ance har da kuɗin wani da ya tura masa zai shi masa gida, hauka tuburan ya yi fa, har sai da aka kai shi gidan mahaukata, da ya dawo mai kuɗin ya kulle shi."
"Sakayyar Ubangiji ne ai ya zalinci Nasreen sosai, musamman dukan da ya yi mata ranar da zai saketa, kamar ya kuma ɓarawo." Mama ta ce tana kallonsu.