Sashe 29
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Raihan ta miƙe da sauri saboda tsananin tsoronta da take yi, amma sai ta kasa jiri ya ibeta ta faɗi. Idanunta ya ƙaƙƙafe ganin haka hankalin ta ya tashi sosai. Da sauri ta inda abincin tana faɗin,"Ke kar ki jaza mini bala'i ki mutu a yaɗa ni a duniya na kashe 'yar kishiya." Ta ce tare da watsa mata ruwa, amma ko motsi ba ta yi ba. Ganin haka ya sanya ta ɗauke ta tasa ihu za ta fita maƙota.
Maman Muwaddat tana zaune tana tunanin rayuwar Nasreen. Bayan sun gana waya ta ƙara kwantar mata da hankali. Roƙon da ta yi mata kanta je ta duba mata yaran, take jin kamar ba za ta iya cikawa ba. Ta san halin Faruk tijararre ne, ba ta son ya yi mata rashin mutunci, duk da cewar tana tunanin ba za'a same shi a gidan ba.
Jikinta a sanyaye ta ɗauki hijabinta ta shiga cikin gidan, daidai lokacin da ta fito da Raihan a sume.
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Mai ya faru?" Ta yi mata tambayar tare da karɓarta.
"Ba ta da lafiya ne ta sume." Ta ce a firgice.
Bata jira abin da zata ce ba ta shiga cikin gida. Motar mijinta ta ɗauka suka kaita asibiti. Da ƙyar suka yi nasarar dawo da numfashinta. Bayan likitan ya gama bincike ya kira ta.
"Saboda me za ku bari maleriya ya kama yarinyarki haka? Bayan akwai net ko kuma maganin sauro ga kuma yunwa?"
Shiru ta yi cikin tausayi ba tare da ta ce komai ba.
Ganin haka mijinta ya ce." In sha Allahu za mu kiyaye."
"Ya zama dole saboda yana shirin taɓa ƙwaƙwalwarta. Don Allah ka kula in mahaifiyarta ba ta nan kai uba ne a gareta." Ya ce yana kallon Maman Muwaddat a tunanin sa ba mahaifiyarta ba ce.
"Shikenan mun gode."
"Zan kira Nasreen ta zo asibitin nan, yanzu zan koma na ɗauko mata Musaddik na sanya Amina ta ɗauki shi. Ta karɓi yaranta in mahaifinta zai kore ta, sai dai ya kore ta amma kar ta bar haramta su mutu." Ta ce tare da danna mata kira.
Nasreen tana zaune a tsakar gida kan turmi ta zabga tagimi. Hira mutanen gidan suke yi, amma gabakiɗaya hankalinta ba shi kan hirar. Sai kallon wayarta take yi tana jiran kiran Maman Muwaddat ta gaya mata yadda yaran suke.
Ganin kiran har sai da ta miƙe."Hello ya yarana suke?" Ta yi mata tambayar cikin rawar murya.
"Ki zo asibin Almadina muna can da Raihann ba...."
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta furta tare da yanke wayar ta saka kuka.
"Lafiya Nasreen?" Mama ta yi mata tambayar cikin ruɗani.
"Raihann ba ta da lafiya tana asibiti. Na shiga uku dama na san Faruk ba zai iya rike mini yarana ba. Wallahi zan kawo su gidan nan, in Baba zai kore su sai dai ya haɗa da ni." Ta ce tana kuka.
"Ki natsu mu je asibiti..."
Ko kafin Mama ta gama magana har ta kai baƙin ƙofa. Ganin yadda ta ruɗe ya sanya ta rinƙa ba ta baki, amma ba ta jin bin da take cewa. Burinta kawai ta yi toxali da yaranta.
A ƙofar shiga asibitin ta haɗu da Maman Muwaddat da suka je ɗauko. Musaddik. Da sauri ta ƙara da ta karɓe shi wanda tun da ya ganta ya fara miƙa mata hannu sai ya saka kuka.
"Na shiga uku Musaddik ne ya dawo haka?" Ta yi mata tambayar cikin kuka.
"Yaranki suna buƙatar ki, duk abin da Baba zai yi miki karki rabu da su. Ban taɓa ganin mugun uba ba irin sa."
Kuka take yi sosai tana tausayinsu. Da suka shiga cikin ɗakin da aka kwantar da ita. Rungumeta ta yi tana kuka sosai har sai da suka rarrasheta
"Wallahi ko kashe kin zai yi ba zan yarda ya ƙara raba ni da yarana ba, Faruk mugu ne Allah ka saka mini yarana."
"Umma, don Allah kar ki tafi ki barmu Abba ba ya sonmu." Raihan ta ce cikin sanyin murya na masu ciwo, sai kuma ta fara tari alamun yunwa ta kamata.
Kamata ta yi ta rungume tana hawaye. A ranar wuni suka yi a asibitin sannan aka ba su sallama. Da ga asibitin gida suka wuce. A ranta ta shirya duk abin da Baba zai yi mata sai dai ya yi, amma ba za ta bari su koma gidannan ba."
Da ya shigo ya gansu, Raiha tana kwance a tsakar gida, an shinfiɗa mata tarbarma tana sha iska
Barka da sallah fans ɗina ina yi muku Barka da sallah tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. Sai na zo muku yawon sallah. Tamu Jamila lawal Zango Jamsy❤️❤️❤️❤️❤️🙏🙏🙏💃💃 Nasreen, Damir, Marwana, har ma da Faruk capacity yana muku barka da sallah.
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 15
Da ya shigo ya gansu Raihan tana kwance a tsakar gida, an shinfiɗa mata tarbarma tana sha iska.
"Waɗannan kuma fa?" Ya tambaya tana nuna su.
"Haba kai kuwa, kamata ya yi ka tambayi mai ke damunta, amma ba wai daga ganinsu ka tambayi abin da suka zo yi ba." Mama ta ce cikin sanyin murya.
Nasreen kuwa hawaye ta goge jin ya ɗaga kafaɗa ya ce,"Ba wannan ya dame ni ba, kawai so na ke na san abin da 'ya'yan Faruk su ke mini a gida."
"Ka zauna na yi maka bayani." Ta ce cikin takaici.
Zama ya yi yana faɗin,"Duk abin da za ki faɗa, ba zan yarda su zauna mini a gida ba."
Bayan ta gama gaya masa abin da ya faru, sai ya kalle yaran da fuskar ko in kula ya ce,"Ya kashe su mana ai yaransa ne. Shi ya kasa tausayinsu sai ni? Dole su koma gidan ubansu, yadda ya kasa riƙe mini 'yata don ubansa ba zan riƙe na sa ba."
"Baba, ba zan iya barin yaraba ba, in har ka tilasta mini dole su koma ni kuma zan bar gidan dasu. Zan je na samu inda zan zauna na kula dasu."
"Allah ya ba ki sa'a in kin so ki tafi bangon duniya, amma ba za su zauna ba." Ya ce tare da wucewa fuu kamar kububuwa.
Rungume su ta yi a ranta tana jin babu abin da zai raba ta da su. Duk bala'in da ya rinƙa yi sun shanye, saboda babu wanda yake tanka masa har ya gaji ya gama. Gabakiɗaya suka ɗaure mata gindi har da yaran gidan, sun rantse in har ya kori 'ya'yan Nasreen, sai su ma sun bar masa gidan, kuma daga ranar sisi ba za su ƙara taimaka masa ba. Goggo da Mama kuwa kowa ce ta haɗa kayanta jira suke ya kwashi yaran ya mayar, kamar yadda ya ce, su kuma su bar masa gidansa. Ganin haka sai hankalinsa ya tashi sosai, saboda ko kallonsa ba sa yi, jira kawai su ke yi ya mayar da su, ya ga aiki da cikawa. Ranar duk wacce ta yi girki babu wacce ta ba shi, haka ya wuni yana hamma tun da haka yake yi, sai dai in sun samu su sam mishi, ranar da yake da shi ba ya ma wuni a gidan. Wannan abu da suka yi masa ya sanya jikinsa ya yi sanyi, har ya kasa mayar da su. Sai dai ya rinƙa tsiya yana zage-zage sun raina shi, babu wanda yake kula shi. Ya yi bala'i ya yi masifa da tijara, ko kofi ya gani a tsakar gida, in ya yi ball da shi ya fara tsiya, sai dai su yi mishi shiru kawai. Ganin faɗan shi a banza har ya gaji ya haƙura, amma kullum sai ya gaya mata tana gama idda a za ta yi aure, ta mayar masa da yaransa. Ita dai shiru kawai take yi masa tana addu'ar Allah ya kai ta lokacin. Auren fari dai ya yi mata dole, amma a wannan karon ba ta tunanin zuciyarta za ta iya aminta da wani ɗa na miji. In ya matsa mata da zancen aure za ta je ta kama haya ta raini yaranta.
Farouk da ya dawo gida bai ga yaran ba kallonta ya yi da take ta zare idanu alamun rashin gaskiya."Ina su Raihan na duba ɗakinsu ban gan su ba?"
Jin tambayar da ya yi mata sai da hantar cikinta ya kaɗa."Mahaifiyarsu ta turo an..."
Ganin yadda ya zare idanunsa yana kallon ta cikin ɓacin rai, sai ta fasa ƙaryar da za ta yi masa ta ce,"Ta tashi ba ta da lafiya ta sume shi ne na ruɗe na fita ina neman taimako, sai na ci karo da Maman Muwaddat ƙawar Nasreen ta karɓe ta..."
"Uban me ya sa ba ki kira ni ba, kika bata ita?" Ya furta yana huci.
"To ka ije ni na yi maka gadinsu ne, ina laifina don na yi taimako?" Ta mayar masa da tambaya a maimakon amsa.
Mugun kallo ya watsa mata ya fice daga gidan. Cikin isa ya rinƙa doka sallama a gidan. Kasancewar mijinta ba ya nan, sai ta sanya hijabi ta leƙa wajen domin da ma tana addu'ar ranar da za su haɗu."Ina yarana?" Ya ce mata babu sallama bare gaisuwa.
"Ka bani ajiyarsu ne?" Ta furta tana harararsa.
"Babu ruwan ki da rayuwar gidana, saboda har da ke ku ka zuga Nasreen take mini rashin kunya. Ki bani bani yarana na wuce, don ba ni da lokacinki."
"Ko kuma ni ne ba ni da lokacinka domin ba ka cika namijin da zan yi sa'insa da shi ba. Wanda ya kasa riƙe matarsa ya zama mugu azzalumi hatta yaranka ba ka daga..."