← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 92

Sashe 30

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da mijin ki zan yi ba da ke ba, saboda ke ban ɗauke ki da wata darajar da zan yi sa'insa da ke ba."

"Ba ka da abin cewa dai Faruk! In sha Allahu zalincin da ka yi wa Nasreen dai Allah ya saka mata. Sai ka zo da hawayenka kana dana sani."

Ba tare da ya kula da abin da ta ce ba ya bar ƙofar gidan. Gida ya koma ya tasa Rashida da masifa. Da fari ta yi banza da shi, amma ganin yadda yake gaya mata yake neman zaginta sai ta miƙe ta ce,"Tsaya Faruk! Na gaji da rashin mutuncin ka, ɗin ka saki matarka ba zan yarda ka ci kashin da kake ci a kanta ba. Haka kawai saboda wasu banzan yaranka da ka kasa kula da su, sai ka nemi zagina." Ta furta cikin murya mai ƙarfi.

"Ok, haka kika ce?"

"Eh, don wallahi ba a yi namijin da zan zauna yana mini ihu kamar wata 'yarda ba."

"Ihu yanzu na fara miki watarana fukanki zan yi za ta yi jini, matuƙar kika ce ba za ki bi umurnina ba."

"Heeee!" Ta yi shewa tana tafa hannayenta sannan ta ce,"Ashe watarana za mu daku, saboda wallahi ba a yi wani gardi da zan bari ya taɓa lafiyata ba."

Mamakin sunan da ta kira shi da shi ya yi, amma sai ya kasa ce mata komai, ganin yadda ta tsaya babu alamun tsoro a fuskarta. Ƙuta ya yi sai ya wuce cikin ɗakinta ya kwanta yana jin zuciyarsa babu daɗi, yana mamakin yadda take gaya masa magana, ya kasa ɗaukar mataki. Ya yi tunanin Baba zai dawo masa da yaran, amma dai ya ga har sun yi kwana biyu, ba su dawo ba. Hankalinsa ya kwanta ya ƙi zuwa don kar ya sanya dole ya dawo da su. Shi kansa zai fi samun natsuwa in suna can.

Nasreen ta samu kwanciyar hankali sosai, domin tun ranar da yaran suka dawo gurinta take ji kamar an zare mata ƙaya. Hankalinta a kwance, yake gudanar da shirin fara bautar ƙasar da za ta yin domin kira kawai take jira har an yi posting ɗin ta za ta je Maiduguri ta dawo, sai ta ci gaba da koyarwa a makarantar sakandiri babu nisa sosai a tsakaninsu.

A ranar da aka kira su ta shirya ya tafi duka sati ɗaya ta yi sannan ta dawo. Ji take yi rayuwarta kamar ba ita ba, ganin ta samu farinciki da kwanciyar hankali.

Bayan ta dawo ta fara koyarwa a makaranta. Sosai take jin rayuwarta ta canza. Inka ɗauke kwamacalar rayuwar zaman gidansu, babu abin da yake damunta. Dama kuma wannan ta saba. Jarrabar Baba ne ya zu ba ya ba ta tsoro. Haka sai yi ta surfa ma yaransa zagi yana tsine musu albarka. Shi da ya kamata ace ya tallafi rayuwarsu, amma kullum ba shi da aiki sai roƙon su kuɗin da zai ci abinci.

A ranar da aka yi musu biya cikin tsana farinciki ta wuce kasuwa. Siyayar abincinta yi musu sannan ta

Kafin a fara biyanta sha wuya sosai, domin kuɗin motar ma sai ta roƙa gurin ƙanninta. Kasancewar akwai tazara sai an hau napep. Ta ci gaba da kai Raihann makaranta a ranta ta sanya ko da Faruk ba zai biya ba, za ta ci gaba da biyan mata. Rayuwar haka take gwara musu yau fari gobe tsumma. A haka har aka fara biyansu. A ranar ta je ta shigo duk abin duk abin da suke buƙata, domin duka naira dubu goma ta shigo da shi cikin gida.

Baba ta ba wa naira dubu goma sai Mama ta cire dubu biyar ta bata na cefane. Sannan ta cire kuɗin mota da wanda za ta rinƙa siya wa Raihan biskit. Hankalinta kwance tana ta zuwa aikinta sati da lahadi islamiya. Kasancewar yadda yanayin rayuwar na su yake, sai kuɗin da take samu ba ya biya mata buƙatunka. A haka dai suke tafiya da rayuwar yau fari gobe tsumma, amma rayuwar da take yi yafi mata na gidan Faruk. A ranar da Maman Muwaddat ta zo ta kawo mata hijabai, ta yi farinciki sosai ta karɓa, kuma babu laifi yana shiga. Damuwarta ɗaya yadda Baba kullum yake isarta da bani-bani. In ta ce masa babu ya rinƙa tozarta yana ƙunduma wa yara ashar, tare da barazanar mayar da su. Wannan dalilin y sa ta gwammace ba ta a gidan da zama. In kuma tana nan za ka dame ta a cikin ɗaki da qur'ani a hannunta tana karantawa.

Damir da su Hajiya zaune a filin jirgi yana jiran fasinja su gama haɗuwa, don jirgin ya tashi zuwa Nigeria. Yana sanye da suit baƙaƙe sun yi matuƙar yi masa kyau. Ya murje ya yi kyau kamar bashi ba. Kullum yana yi mata addu'a, ganin ƙunci da shiga damuwa ba zai dawo masa da ita ba. Abu ɗaya zai yi ya tabbatar da yana ƙaunarta, ya ƙara sa rayuwarsa batare da ya yi aure ba. Tabbas duk barazanar da Hajiya take masa, ya sanya duk abin da za ta yi ba zai auri ko wace 'ya mace ba. Hannunsa riƙe da wayarsa yana tura message, chattin yake yi da Muhsin.

Marwana take gefensa da ƙatuwar teddy na Little Marwana da ta ba ta ijiya, tana cinyar Hajiya bacci ya kwashe ta. Sosai take jin daɗin za su dawo gida. Damuwarta ɗaya ita dawo ba za ta iya zuwa ta ga Nasreen ba, saboda baƙi da Hajiya ta yi mata. Sosai take kewarta har yau tana jin sonta, babu abin da ya ragu. Ta san cewa a wannan lokacin ta rabu da mugu FARUK, wataƙila ta canza ta yi kyau kamar ba ita ba. Tana son ta je gidansu ta ganta, sannan ta yi wa Ya Ahmad godiya na zama mata bango da ya yi, sai dai mugayen kalaman da Hajiyar ta yi mata ya sanya ta kasa kiranta ko da a waya ne.

Damir ya miƙe tare da ɗaukar Little Marwana da ta farka tana goge idanunta. Kiss ya sakarwa yarinyar yana murmushi. My little angel ta tashi, daidai da lokacin da jirginsu yake shirin tashi ku zo mu shiga." Ya ce masu yana kallonta. A yanzu bashi da abin so kamarta. Duk son da yake wa mahaifiyarta ya ɗaura shi kanta. Yana dinga fiye da kansa. Tun da ya saki ya fara rage damuwa. Shi yake mata wanka da komai na ta. Ji suke yi da yarinyar sosai, suna tausayin za ta tashi cikin maraici.

Bayan sun shiga direban jirgin ya fara tuƙawa. Addu'a suke yi Allah ya sauke su lafiya. Bayan wasu awanni jirginsu ya iso Nigeria. Kasancewar da daddare suka dawo, kowa ɗakinsa ya wuce ya yi wankan sannan suka kwanta. Da safe ko da suka yi sallah baccin gajiya suka yi.

Marwana ta fara tashi sai Hajiya. Dama tuni sun sanar da mai aikinsu za su dawo. Ta zo ta gyara gidan kuma ta yi musu abinci, sannan ta fara aikinta tun kafin su dawo, domin a gidan ta kwana.

Kicin suka nufa don su samarwa little Marwana abinci da take musu ƙorafin yunwa. Marwana na ƙoƙarin ba ta abinci a baki Damir ya shigo falon. Ganinsa ya sanya ta rungume shi.

"Angel kin tashi?"

"Yes daddy ina kwana?"

"Lafiya lau." Ya ce tare da jan kumatunta.

"Ina kwana Ya Damir?" Marwana ta ce tana kallon sa ganin yadda ya yi kyau.

"Lafiya lau sis." Ya ce ba tare da ya kalle ta ba, bayan ya ja filet ɗin abincin da za ta bawa Marwana ya fara bata.

Hajiya ce ta fito tana tafiya da kyar saboda ƙafafunta, tun a jirgi take korafi. Gabakiɗaya suka kalleta daidai lokacin da Muhsin shi ma ya shigo.

"Ina ga fa sai kin je clinic ko?" Ya yi mata tambayar yana kallon ta.

"Man zafi na shafa tsufa ce kawai kafar zai saki." Ta ce nushi tare da zama gefensa.

"Allah ya ƙara sauƙi ni da Muhsin za mu je campany in na gama zan biya na suyi miki wani maganin."

"Ok, sai kun dawo Allah ya tsare Please ku mayar da hankalinku."

"In sha Allahu." Ya ce sai kuma ya kalli Marwana.

"Ke ma sai ki shirya ki koma makaranta kin san duka bai fi 2weeks ku zama exam fa, don kin yi deffering semester da ba za su bar ki ba."

"Haka ne Ya Damir da kuma taimakon amininka."

"Ki mayar da hankali ban da wasa." Muhsin ya ce mata.

"In sha Allahu Yaya You know me."

Kansa ya ɗaga mata jin abin da ta ce.

"Wallahi Marwana kika koma makaranta kika kula wannan yarinyar sai ka matuƙar bata miki rai, innhar ni na haife ki ban aminta ki yi hurɗa da ita ba." Ta ce cikin kakkausar murya.

"Mommy ba zan ga Nasreen ba, saboda ta kammala karatunta, sannan ban taɓa zuwa gidan iyayenta ba, yanzu dai na san ta rabu da mijinta Faruk."

"Ko ma dai mene ne na hana ki hurɗa da ita." Ta ce mata tare da miƙa ta isa dining.

Damir gabansa ya faɗi sosai jin an yi maganarta. Tun da ya bar Nigeria ya fara ƙoƙarin manta komai ya yi ƙoƙarin mantawa da ita, ya ɗauki mutuwar Batula a matsayin lokacin ta ne ya yi, domin ta hakan ne kawai zai iya mantawa da ita. Da sauri ya fice ba tare da ya ji abin da Hajiya ta ce ba.

Da suka je campany ma'aikatan sun yi matuƙar farincikin ganin ya yawo sai Damir ɗin da, abin da kawai ya rage yawan ɗaure fuska. Duk da cewar Muhsin ya yi ƙoƙari, amma ya samu aiki sosai har sai da ya gaji. Ba tare da ya kammala aikin ba suka dawo gida. Wanka ya yi sannan ya wuce masallaci. Bayan sun yi sallah ya shigo cikin gidan.

Bayan sati ɗaya da dawowarsu hankalin Hajiya ya kwanta sosai, ganin yadda ya kwantar da hankalinsa.
Chapter 30 · 0% Book details