← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 92

Sashe 27

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farouk da ya bita bai dawo ba sai cikin dare. Da ya dawo ya buɗe gidan ya shiga. Har ya dumfari ɗakinsa sai ya tuna da su. Da sauri ya shiga cikin ɗakin ganin babu haske. A tujaninsa ba su a ciki, amma dai ya ji ƙunkunan Musaddik da sauri ya hana shi bacci.

"Raihan," Ya kira sunanta cikin tashin hankali tare da kunna fitilar wayarsa.

"Na'am," Ta amsa cikin muryar kuka.

Hankalinsa ya tashi sosai. Da sauri ya ƙarasa yana kallon abincin dake gabansu."Ba ku ci abincin ba, kuma mai ya sa kuka zauna sauro yana cizon ku?"

"Abincin da yaji ba zamu iya ci ba, kuma Anty ce ta ce mu shiga ciki."

Ransa ne ya ɓaci jin abin da ta ce.

Hannunsu ya kama su ka fita waje. Bai taɓa tunanin yana son yarana ba, sai a yanzu da ya ji ransa ya ɓaci game da abin da ta yi musu.

Cikin fusata ya tura ƙofar yana huci kamar mesa."Saboda uban me za ki barsu a cikin duhu?" Ya yi mata tambayar yana kallon ta.

"So kake na kai musu wayata su kunna da ita? Tun da tsabar maƙo ya hana ka ko ɗan solar ka sanya mana. Kana ganin ko wane gida an sanya, amma kai ko maganar ban taba jin ka yi b.."

"Ba zan sanya ba in da uban da zai sa.."

"Farouk na gaya maka ka daina zagina.."

"Ramawa za ki yi?"

"Wallahi tsaf zan iya saboda uba bai fi uba ba" Ta ce masa tana aika masa da mugun kallo.

Mamaki da takaici suka hana shi magana sai kuma ya yi ƙuta ya ce,"Na gaya miki ba ki isa ki canza tsarin da nake rayuwata ba, kuma wallahi a kan yaronnan za mu yi mummunar saɓawa."

"Ka mayar da su gurin uwarsu ba zan iya ba." Ta ce tare da jan tsaki ta juya masa baya.

Shi ma tsaki ya yi ya kama hannunta suka fita. A falo ya zaunar da su sannan ya shiga cikin ɗakinsa. Indomie ya ya dafa musu ya bawa Raihan. Ita ta bawa Musaddik har ya ɗan ci ya kwanta.

Ɗaki ya shiga ya yi wanka, sannan ya zauna a gefen gado, yana tunanin yadda zai yi da ita ta karɓi yaran. Sai da ya gama abin da zai yi sannan ya fita daga cikin ɗakin.

Ɗaki ya kai su bayan ya sanya musu maganin, sauro ya fito ya ja musu ƙofar. Tana tsaye a cikin ɗakinta ya shigo. Ganinsa ta ja tsuka ta mayar da kanta ta kwanta.

Ba tare da ya ce mata komai ba ya kwanta. Kusan minti biyu babu wanda ya yi wa juna magana. Hannunsa ya sanya ya rungumeta.

Da sauri ta ture hannunsa."Ka cika ni matuƙar ba za ka mayar da yarannan ba, ni kuma babu ruwan da kai."

Kallonta ya yi sai kuma ya ce,"So kike na watsar da su a titi? Tun da ubanta ya dawo mini da su ya zan yi? In dai ba gidan marayu kike so na kai su ba."

"Ni fa ban damu ba, saboda in har za ka hana ni haihuwa, ba zan zauna na yi wahala da su ba."

Jan bargo ya yi ba tare da ya ƙara kulata ba ya yi kwanciyarsa. Gajiya ta yi da mita ta kwanta.

Cikin dare Musaddik ya kasa bacci sai kuka yake yi. Ganin haka Raihan ta saka kuka suka cika gidan. Duk rarrashin da ya yi musu sun ƙi yin shiru, har sai da ya yi musu tsawa. Musaddik kuwa har dukansa ya yi, sannan ya yi shiru bacci ya kwashe shi. Ɗaki ya koma ya kwanta, zuciyarsa na ba shi shawarar ya kai mata yaran ko ba za su karɓa ba.

Washegari duk yadda yake son ya yi bacci, kan dole ya tashi zuwa ɗakin Nasreen. Bayan Raihan ta sanya shi a fo. Ta kama hannunsa suka fito. Shi ya dafa musu ruwan wanka ya yi musu, sannan ya shirya Raihan makaranta.

Ya shiga ɗaki da nufin ya ɗan rintsa. Bacci mai nauyi ya ɗauke shi bai farka ba, sai takwas har da rabi. Kallonta ya yi cikin takaici."Saboda ba yaranki zan kai ba, shi ne za ki ƙi tashina?"

"Dama ka aure ni ne don na rinƙa tsaronka, ina tashin ka don ka kai 'ya'yanka makaranta?"

Ganin yadda ta yi masa tambayar sai bai ce komai ba. A gauguace ya shirya ya same su a falo."Abba na yi latti ina ta jiran ka, har ƙofar ɗakinka na zo Anty ta kore ni."

"Wuce muje." Ya ce na tare da ya amsa mata ba tare da ɗaukar Musaddik. Ranar kuwa sun sha latti don sai ƙarfe tara ya kaita makarantar. Da ya dawo da Musaddik, wanda fuskarsa a kyaɓe jira yake yi a taɓa shi ya saka kuka.

Rasa yadda zai yi da shi ya yi, don ya san Rashida ba za ta kula da shi ba. A ranar dai fasa zuwa aiki ya yi. Lokacin ɗauko Raihan ya yi, ya ɗauko ta. Shi da kansa ya haɗa musu a binci. Wuni ranar ya yi aikin kula da su. Kafin dare ya gani sosai don har ya ƙosa.

Da daddare ya samu suka yi bacci. Wanka ya yi sannan ya kwanta.

Nasreen ta shiga damuwa sosai na rashin yaranta, amma sai dai duk yadda take roƙon Baba ya kafe ba za su zauna ba. Ganin ya ƙi amincewa kuma kuma ba shi ne magani ba sai ta haƙura, amma a cikin zuciyarta Allah kaɗai ya san halin da take ciki. Ko ruwa ta ɗauko za ta sha, sai sun faɗo mata a cikin ranta. Wunin ranar har ta zurma sai ɗan wuya. Da rana tana zaune sai ga Maman Muwaddat. Ganin ta ta rungumeta ta fashe da kuka.

"Abin da nake gudu ya faru. Baba ya mayar masa da su Raihan." Ta ce tana share hawaye.

"Ki yi haƙuri ki bar shi da yaran, wallahi ba zai iya kula da su ba. Kina ganin matarsa za ta riƙe masa su?"

Barka da sallah fans ɗina ina yi muku Barka da sallah tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. Sai na zo muku yawon sallah. Tamu Jamila lawal Zango Jamsy❤️❤️❤️❤️❤️🙏🙏🙏💃💃 Nasreen, Damir, Marwana, har ma da Faruk capacity yana muku barka da sallah.
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 14

Abin da nake gudu ya faru. Baba ya mayar masa da su Raihan." Ta ce tana share hawaye.

"Ki yi haƙuri ki bar shi da yaran, wallahi ba zai iya kula da su ba. Kina ganin matarsa za ta riƙe masa su?"

"Halin da za su shiga nake tunani, ina son yarana ina jin babu daɗi."

"Za su dawo gare ki in har kika ɗan yi haƙuri na ɗan lokaci."

"Bana jin zan iya."

"Daurewa za ki yi, ko wace uwa ba da sonnta rabu da yaranta, duk wacce kika ga ta yi nesa da su, babu yadda za ta yi ne."

"Haka ne Allah ya ba ni ikon jurewa, amma Baba bai yi mini adalci ba da ya raba ni da su."

Haƙuri da rarrashi ta yi ta mata har ta ji sanyi a zuciyarta. Ta jima sannan ta yi mata sallama.

"Don Allah ki rinƙa duba mini su." Ta ce tana share hawaye.

"Zan yi iyakan ƙoƙarina, amma kin san ganinsu da wuya, saboda Yasir ya ce mini ba ta je makaranta ba sai da rana ta yi."

"Kin ji ko? Dama na gaya miki ba zai iya kula da su ba."

"Komai zai wuce ki yi haƙuri wahala ba ya kisa. In mutuwa kika yi dole za ki tafi ki barsu."

"Haka ne." Ta ce tana jin kewar yaran. Da daddare ta kasa bacci, har sai da ta ɗauki maganin damuwarta, sannan ta samu ta yi bacci mai cike da kewarsu.

A tunanin Faruk zai iya rarrashinta ta riƙe mishi su, amma sai ya ga ta funjire ta shafawa idanunta toka. Babu rarrashin da bai yi mata ba, amma ta ƙi daga baya ta ƙi, daga baya sai ta ce masa za ta iya rike su a bisa sharaɗi ɗaya.

Kallonta ya yi yana mamakin kafiyarta."Ina jin ki." Ya ce cikin rashin dubara, domin ko sati ba a yi ba, ya gaji matuƙar gaske. Babu abin da yake damunsa fiye da kukan Musaddik. Sannan shi bai iya rainon yara ba. Ko lokacin da yana yaro tsakaninsa da yara sai kallo.

"Ka ba ni dama na haihu da kai. In har ka yi mini haka zan iya tausasa zuciyata na ga ko zan riƙe su."

Tsaki ya yi jin abin da ta ce,"Ba zan amince ba, saboda ban aure ki don ki tara mini yara ba. Jikinki ya burge ni na sanya kuɗina na aura."

Mamakin abin da ya ce ya kamata, sai ta kalle shi cikin mamaki ta ce,"Ai wallahi tun da haka ka ce, sai dai ka nemi inda za ka kai su."

Banza ya yi da ita ya juya mata baya. Shawara ya yanke ya kai su gurin Yaya Asiya. Da safe ya haɗa musu kaya ya kaisu.

Tana zaune a falo ya shigo da jakarsu yana rungume da Musaddik.

"Lafiya Faruk, na gan ka da yara haka?" Ta ce masa tana kallon sa.

Ba tare da ya amsa mata ba ya ƙara sa kan kujerar ya zauna."Na kawo su nan ne." Ya ce yana kallonta.

"Hutu za su yi mini ina uwarsu?"

"Mun rabu na sake ka..."

"Ka yi me? Anya kana da hankali kuwa?" Ta yi mishi tambayar cikin tsananin razana.
Chapter 27 · 0% Book details