← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 92

Sashe 75

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin ya tsaya a cikin motar ba tare da ya tafi ba, sai ta gane jira yake ya ga tafiyarta. Murmushi ta yi sannan ta ta fara jan motar. Sai da ya ga ta yi nisa sannan ya tayar da na shi.

A ranar babu wanda ya rintsa a tsakaninsu domin saboda abin da ya faru kasa bacci suka yi. Nasreen ta yi tunani har ta ji kanta ya fara ciwo, don haka ta tashi ta ɗauro alwala, ta yi sallah tare da yin istikhara neman zaɓin Allah.

Kamar yadda ta yi haka Damir ya raya daren da sallolin, yana fatan ta fara nuna mishi ƙauna. Ba su samu sun rintsa ba, sai da asuba bayan sun yi salla.

Da ta tashi da safe, sai ta ji hankalinta ya ƙara kwanciya da shi sosai. Har zumuɗin zuwa aiki ta ji tana yi don ta ganshi. Kamar yadda take cike da ɗokin ganinsa haka shi ma. Kuma cikin sa'a ta zo zata hau sama zai sauka ƙasa, don ya rigata zuwa.

"Ina kwana?" Ta ce masa cikin murya mai tashi.

"Da fatan kin tashi lafiya gimbiyar mata." Abin da ya ce sai ta haye sama da sauri tana murmushi. Shi ma murmushi ya yi yana waigenta.

A cikin kwanakin suka saki makamansu suka kama soyayya. Duk da cewar babu wani shaƙuwa a tsakaninsu, domin ko kiranta ya yi daga gaisuwa za su yi shiru, amma hankalinsa ya kwanta sosai. Kullum cikin tunainta da son ganinta.

A lokacin da ta sanar da Marwana ta yi murna sosai. Rungumeta ta yi cikin farinciki."Mun zama ahali ɗaya." Ta ce tana kallonta.

Mommy ma hankalinta ya kwanta haka Mama duk sun yi farinciki.

"Kai lamarin Ubangiji sai shi. Sai ya haɗa ka da mutumin da baka taɓa tsammani ba."

"Haka ne Ahmad shi ya sanya ba a son wulaƙanta mutum. Yai ga shi a dalilin Marwana muna shirin zama dangi ɗaya."

"Haka ne Mama na yadda domin a lokcin da na haɗu da ita, ban taɓa tunanin zamu ƙulla alaƙar da zai mayar da mu dangi ba." Cewar Nasreen cikin mamaki.

Gabakiɗaya Damir ya susuce mata tamkar ba shi ba. Sam ba ya jin kunyar nuna mata soyayya a gaban kowa, domin kallon ta kawai da yake yi, mutum zai gane akwai soyayya a tsakaninsu.

Kusan yawanci shi yake ɗauko su Little Marwana da Raihann makaranta, saboda ya fi samun lokaci, domin Zainab tana makaranta Ahmad gurin kasuwancinsa. Mama ce don haka yake hirar da ita, domin ya fi son ɗauki su kan masu keke ko acaɓa da ba sa gudu sosai.

Farouk ya shiga cikin damuwa, ganin babu wanda ya sanya masa hannu kan Nasreen ta dawo gidansa. Da fari gurin Anty Asiya ya je, amma sai ta katse shi ta ce,"Ba zan iya haɗa idanu da iyayen yarinyar nan ba, saboda abin da ka yi ba ka kyauta ba. Har na je na ce musu su yi haƙuri Nasreen ta dawo ɗakinta. Ka samu wata matar ka aura kawai, amma da wuya ta dawo gareka."

"Ba zan iya auren ko wace 'ya mace ba, saboda tsoron matan na ke yi. Nasreen kawai na ke so ita ce kawai na ke jin za ta iya jure halina, kuma walllahi na tuna na zan zame mata miji na gari. Ina son na rayu da yarana. Ji na ke yi kamar na kashe kaina, in na tuna Damir yana soyayya da ita."

"Ya za ka yi ka riga ka yi sake Faruk, da ma duk wanda bai ji bari ba, ya ji hoho."

"Ki bar tuna baya, don ji na ke yi kamar zan yi hauka in ba ta dawo gidana ba."

"Ka je ka gwada wataƙila ka dace." Ta ce mishi cikin takaici.

Shiru ya yi cikin nadama mata amfani. Ya daɗe zaune yana tunanin yadda zai shawo kanta ta mince, amma sai ya ga babu fuska domin da gaske yake yi. Jiki asanyaye ya miƙe ya fice cikin damuwa.

Rakashi da idanunta ta yi har ya fice. Takaici sosai yake ba ta, sai ta ji kamar za ta rufe shi da duka, in ta tuna lokacin da take ta gaya masa ya zuwan wannan ranar, amma ya yi kunnen uwar shegu tare da shafama idanunsa toka. Yanzu wa gari ya waya? Dama duk wanda ya ƙi ji, ba ya ƙi gani ba.

Daga gidanta gurin abokansa ya je yana roƙonsu, amma babu wanda ya saurare sa, domin su kansu bai ba su mahimmanci ba, duk yadda suka so ya daina cutar da ita, amma ya ƙi kula su.

Haka ya koma jiki a saɓule cikin tsanannin tashin hankali. Da ya koma zama ya yi a falo hawaye sosai yana bin ƙuncinta. A da abin da Rashida ta yi masa kawai yake sa ya sa zubar hawaye, amma a yanzu hawayen rashin matarsa da yaransa yake yi.

Miƙewa ya yi yana jin ba zai iya haƙura da ita ba. In har an ƙi taimaka masa zo je da kansa ya zamar mata mahaukaci har sai ta dawo gurbinsa.

Ba tare da ya ji gargaɗin da ta yi masa ba ya tafi campany. Can nesa da get ɗin ya yi parking yana jiran ta fito sai ya bita, domin ya san cewa ta hana securities su bar shi shiga.

Yana tsaye a gurin, ma'aikatan suka fara fitowa da motocin su suna tafiya.

A ranar Nasreen ta zo aiki sai morarta ta lalace. Kiran mai gyara ta yi ya ɗauka. Damir ya sanar mata in an tashi zai kaisu gida.

Sun fito tana gidan gaba Damir yana jan motar sai yaran a baya. Tuƙi yake wani lokacin yana waigowa yana watsa mata kallon da yake rikitar da ita. Ba wani hira suke yi ba, domin har yanzu babu shaƙuwa a tsakaninsu, ya rasa yadda zai yi ta sake da shi.

Sun fara tafiya kamar ance Faruk ya ɗaya kansa, kawai sai ya hango motar Damir yana tuƙi tana ciki da yaranta. Wani irin kishi ya turniƙe shi har ya kitsa masa matakin da ya kamata ya ɗauka.

Da sauri ya shiga cikin motar ya binsu a baya. Sai da suka yi nisa, sannan ya bugi motar ta baya! Sam idanunsa sun rufe ba tare da ya damu da yaransa da suke ciki ba.

Salati suka ɗauka jin abin da ya faru. Da sauri Damir ya taka burki hankalinsa na gurin yaran da duka fara ihu.

Nasreen ta tsorata sosai domin ta ɗauka hatsari za su yi. Ganin motar ta tsaya dai ta fito da sauri ta zaga ta buɗe su suka fito.

Damir ganin babu abin da ya faru sai ya zaga baya don ya ga mahaukacin da yake son kashe su."Amma kai dabba ne k...." Maganar ta maƙale mishi ganin Faruk ya fito yana huci.

"Har akwai dabban da ya fika? Mai bin matar wani tun kafin aurenta ya mutu. Har akwai wanda ya kamata a kira dabba kamar ka."

Jin muryar Faruk, cikin tsananin fushi sai hankalinta ya tashi. Da sauri ta saki yaran ta ƙarasa gurin motarsa."Kana da hankali kuwa? Ninyar kashe mu ka yi?" Ta yi masa tambayar ciki tsanannin mamakinsa.

"Nasreen zan iya abin da yafi haka matuƙar ba za ki dawo gare ni ba."

"Ban taɓa sanin mahaukaci ne kai ba sai yau. Farouk har da yaranka a ciki kishi hauka ne?"

"Don Allah, ki rabu da wannan mara mutuncin ki dawo gare ni. " Ya furta a maimakon amsar tambayar da ta yi masa.

"Wallahi ko maza sun ƙare ba zan zauna da kai ba, domin na gwammace na ƙarashe rayuwata a matsayin bazawara da na koma gidanka."

"Au haka kika ce? Saboda wannan ɗan iskan za ki guji uban yayanki?" To bari na nuna miki zallar haukar da kike ce wa na yi." Kawai sai ya ɗauki dutse ya nufi kansu.

"Da na rasa ki gara na kashe ki kuma na kashe shi. Na zaɓi na kashe kaina ko kuma a kai ni prison." Kansu ya yi gadan-gadan fuskarsa babu rahma

Ganin haka ta ƙwala ƙara ta razana sosai. Ganin abin da yake yi Damir ya shiga tashin hankali. Da sauri ya tureta ya ƙwala masa dutsen iya shi kaɗai, amma cikin sa'a sai bai same shi sosai ba saboda tureta da ya yi suka faɗi.

A kansa ya same sa ta gefe nan take jini ya fara zuba. Rintse idanunsa ya yi cikin tsananin tashin hankali, sosai yake jin zafin ciwon.

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Don Allah ku kawo mana ɗauki zai yi kisa." Nasreen ta furta cikin ƙaraji ganin babu imani ya ƙara nufe su. Ganin haka yaran suka sanya kuka.

"Gara na kashe ku na rama cin ma'anar da kika yi mini. Soyayya kuka ƙulla da aurena kanki." Ya furta yana kumfar baki kamar taɓaɓɓe.

Da sauri mutane suka farka da bin da ke faruwa, jin ihunta suka zo suka riƙe Faruk.

"Farouk ya haukace kashe mu zai yi." Damir ya ce tare da dafe inda jini yake zuba.

"Na shiga uku Ya Damir don Allah ka yi haƙuri." Ta ce ganin jinin yana zuba sosai. Da sauri ta cire ɗankwalinta na rigar atamfa da sanya. Danne masa gurin ta yi ganin yawan jinin da yake zuba. Ganin ya ƙi tsayawa sai ta ɗaure masa gurin cikin tashin hankali.

"Kai Mahaukacin ina ne? Za ka ga mata da miji da yaransu ka kai musu farmaki?" Wani ya furta zai kai mishi duka.

"Wallahi ba ma'aurata bane, matata ce yake son raba ni da ita, yaran nan gida biyu ni da ita muka haifa. Da aurena a kanta ya ƙalla soyayya da ita."

Kallonsu mutane suke yi, cikin mamaki suna son gane gaskiyar zancen.

"Kai matarka ka ce?" Suka tambayi Damir da yake cikin damuwa ganin tozarcin da yake musu.

"Ba matata ba ce, a.."

"Yauwa kun ji, wallahi da aurenta ya rinƙa bibiyarta ya raba ni da ita." Ya faɗa cikin ɗaga murya.

"Tur da irin masu kuɗi irin ku, saboda ka ga matarsa tana da kyau shi ne ka yi amfani da kuɗinka ka ɗauke masa ita? Haka al'umma suka lalace babu tsoron Allah. Matarsa har da yara dai ka raba su?" Ya yi masa tambayar cikin kallon ƙaskamci.
Chapter 75 · 0% Book details