Sashe 19
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni fa bana son gidadanci da rashin wayewa. Kina ganin abokaina sun zo, a madadin ki shiga ɗauki ki ɗauko mayafi mai kyau. Ki fito musha hira, amma sai kika saka wani zubbulelen hijabi, kamar wata matar liman."
Ba ta amsa masa ba, kamar yadda ya yi tunanin ba za ta amsa masa ba.
"Kuma ba zan ɗauki wannan shiru-shurin ba, domin buɗe baki za ki yi, in na yi magana ki amsa mini."
"To," Ta ce mishi tare da gyara zama.
"Yauwa kin ga kayan abinci na siyo, amma ban amince ki ɗauki komai ba, sai da izinin a, domin kulle ɗakin zan rinƙa yi innzan fita."
"To," Ta ƙara ce masa don ya daina ba ta mamaki.
Miƙewa ya yi tare da kashe fitila sai ya kuma kunna yana ƙare mata kallo.
"Nufin ki da wannan kayan za ki kwanta?"
"A,a." Ta ce a gajarce.
"Ta shi ki canza kaya bacci za mu yi." Ya ce tare da kwanciya kan gadon ya rungume filo yana mata kallon ƙurilla.
Kunyarsa take ji sosai duk da abin da ya faru a tsakaninsu, ba ta jin ta fara sakewa da shi, amma ba ta da wata mafita da ya wuce ta canza kayan.
Riga da wando ta ɗauka masu kyan gaske ta sanya. Sun yi mata matuƙar kyau, amma ta kasa haɗa ido da shi, ballantana ta taho kan gadon.
Ganin haka ya miƙe ya janyo ta, ta faɗa jikinsa."Wow! Kin ga yadda kika yi kyau? Kina da matukar kyau Nasreen. Da ace za ki tattala halittar ki, za mu ci duniyarmu da tsinke, don zan more wannan jikin na ki."
Ba ta ba shi amsa ba sai kallon gefe take yi cikin jin kunya.
Ganin ta yi shiru, ya sanya ya ƙara mannata a jikinsa tare da ɗauke numfashi. Bakinsu ya haɗe sannan ta jawo ta suka faɗa gadon.
Washegari da asuba jin kiran sallah, ya sanya ta miƙe zuwa bayi. Tun cikin daren ta buƙaci ta yi wankar tsarki, amma sai ya ƙi ya haɗata da jikinsa ko motsin kirki kasawa ta yi. A haka suka kwana har asuba.
Da ƙyar ta janye jikinta ta shige bayin. Bayan ta yi wanka, ta yi Raka'atul fijr ta zauna tana karatun Alkur'ani, cikin muryarta mai sanyi.
Karatun da take yi ya sanya shi miƙewa tare da jan tsuka ba don ya so ba.
Ɗaki da ya wuce ya yi wanka. Sallah a gida ya yi, sannan ya kwanta.
Bai tashi ba har zuwa tara da rabi. A lokacin Nasreen tana farko tana ta gyaran gidan, domin kamar yadda ya gaya mata ba ya son ƙazanta, so take ta kiyaye don su zauna lafiya, kuma ko ita ba mace bace mara tsafta.
Ganinta a falo tana gyara ya sanya sakin fuskarsa, tare da ƙara sawa inda take ya rungume ta. Kiss ya sakar mata a fuska.
"Ina kwana?" Ta ce mishi cikin murya mai sanyi, domin ta riga ta saki tun da har ya mayar da ita cikakkiyar 'ya mace. Ba ta da zaɓin da ya wuce ta aminta da aurensa su zauna lafiya.
"Lafiya lau, amma ni fa so na ke ki nuna wayewarki. Ki rinƙa nuna mini ƙauna da kulawa. Gaisuwar ina kwana ta 'yan kauye ne "
Ware hannunsa ya yi, yana kallon ta wanda babu musu ta shiga jikinsa cikin jin kunya. Sun daɗe a haka sannan ya sake ta bayan ya ba ta hot kiss.
"Bari na baki abin da za ki yi mana breakfast." Ya ce tare da juyawa cikin ɗakinsa.
Bayansa ta bi da kallo, tana son gane makusarsa da zuciyarta ba ta ƙaunarsa, amma ta kasa ganowa. Sai ta danganta ƙinsa da take yi da rashin kyawun halinsa.
Tana wannan tunanin ya ɗauki indomie gida uku da ƙwai uku."Ki soya mini ƙwai biyu, sai ki soya wa kanki ɗaya."
Karɓa ta yi har da rissinawa ta ce,"To," Cikin girmamawa sannan ta nufi kicin ɗin ba tare da ta ji wani abu ba.
Kamar yadda ya ce haka ta dafa masa. Da ta zo zuba masa abincin, sai ta kusa biye masa. Bayan ta kai mishi ta sanya ragowar indomie ta ci. Da ta ji ba ta ƙoshi ba, sai ta ɗumama ragowar abincin da ta girka jiya.
Bayan sun karya komawa suka yi suka kwanta bisa umurninsa. Duk yadda yake takura mata hakan nan take haƙura don zaman lafiya.
Sai kusan ƙarfe ɗaya da aka kira sallah ya yi wanka ya fita gidan a mota. Sosai ta ji daɗin fitarsa. Bayan ta ci kuskus ɗin da ta dafa ta koma ta kwanta kan gado.
Ba ta ji ma ba ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Tana don ta buɗe tana tsoron karya dawo. Da sauri ta miƙe ta je ta buɗe, saboda shawarar da zuciyarta ta bata.
Wata doguwar mata ta gani tsaye da yaranta biyu a ƙofar gidan. Murmushin ta sakar mata, tare da matsawa suka shiga ciki.
Bayan ta zauna a falo, ta kalli Nasreen da take wasa da ƙaramar 'yarta da ta ɗauka.
"Sunana Aisha, amma ana kirana da Maman Muwadda. Ni maƙociyarki ne, a unguwar nan na ke. Ga gidanmu nan mai mulki ɗin get, wanda katangar da yake kusa da na ku."
"Allah Sarki! Sannu da zuwa, ni kuma sunana Nasreen."
Murmushi suka sakar wa junansu. Nasreen ta kawo mata cincin da diblan da yawa. Suna ta hira, amma gabanta na faɗi.
Inda ta godewa Allah ba ta wani jima ba ta miƙe. "Bari na tafi na gode sai na ƙara shigowa."
"Ni ma na gode sai anjima kuma zan shigo."
"Shikenan, Allah ya ba ki iko."
"Amin," Ta amsa tare da rakata har bakin ƙofa.
Tana ƙoƙarin kulle ƙofar sai ga Fadila.Da sauri ta rungume ta har da hawayen murna.
"Dallah ni cika ni. Kina can naniƙe da miji na yi ta buga ƙofa da kiranki, amma kika shanya ni."
"Ki yi haƙuri ban ji ba." Ta furta cikin muryar kuka.
"To kukan me za ki yi don kin ganni? Kin ga yadda kika ƙara kyau? Gaskiya Faruk na kulawa dake."
"Hmmmmh!" Ta ce tare da kama hannunta suka shiga cikin gidan.
Abinci ta kawo mata da ruwa da diblan. Suna ta hira ji take kamar kar ta tafi.
"Ina angon na ki? Na tsokane shi."
Gabanta ne ya faɗi ta ce,"Baya nan, tun da ya fita sallah bai dawo ba."
Dirin motarsa da ta ji ya sanya ta ji gabanta ya faɗi.
"Kamar buɗe get za a yi?"
"Eh, shi ne ya dawo." Ta ce mata cikin fargaba.
Ganin fuskarta ya canza ba ta yi tunanin komai ba.
Ya shigo da siriyar sallama a bakinsa.
"Sannu da zuwa." Ta ce masa tare da ƙara sawa gurinsa da sauri za ta karɓi kayan hannunsa.
"Ango kasha ƙamshi." Ta ce tare da miƙewa tana dariya.
"Kina lafiya?" Tambayar da ya yi mata kenan, ya shige ɗakinsa bayan ya kira Nasreen.
Cikin jin kunya Nasreen ta kalle ta.
"Farouk ni zai yi wa haka?"
Narai-narai ta yi kamar za ta yi kuka."Ki yi haƙuri abin da na guda kenan, amma Allah ya riga ya zaɓa mini shi a matsayin miji, tun ranar da aka kawo ni ya gaya mini baya son mutane. Ke ƙawata ce ba zan ɓoye mini komai ba."
"Ikon Allah! Ba komai ki je kiran da yake miki bari na tafi." Ta ce tana mamakinsa.
"Don Allah ki yi haƙuri."Ta furta tare da kama hannunta.
"Wallahi babu komai ba zai raba mu ba, matuƙar ba cewa ya yi karna ƙara shigo masa gida..."
"Nasreen, ba na son wulakanci na kira ki za ki shanya ni. Ko ƙawarki tafi mijinki daraja?" Ta ji yana ƙoƙarin buɗe ƙofa tare da faɗin haka.
Da sauri ta ƙarasa ƙofar ɗakin, tana ɗaga wa Fadila hannu da ta cika da mamaki, domin ta ɗauka ko zai yi wa kowa haka ban da ita.
Jakarta ta ɗauka gwiwa a dage ta fice gidan.
"Mai na gaya miki?" Ya furta tare da kama kunnenta da ƙarfi.
Cikin tsananin mamaki ta kalle shi yayin da hawaye suka wanke masa fuska.
"Eh, kalle ni da kyau, saboda wallahi in har ba za ki bi umurnina ba, sam ba za ki ji daɗi a hannuna ba. Zamanki lafiya a gidan nan duk abin da na ce bana so ki kiyaye."
"Ka yi haƙuri ba zan iya wulakanta ya ba."Ta ce tana matsawa jin kamar zai cire mata kunnen.
"Kin san ƙanwar uwarki ce." Ya faɗa cikin ɓacin rai tare da ture ta ta bugu da bango.
Kuka ta fashe da shi cikin mamakin abin da ya yi mata.
"Wallahi ba ki ga komai ba, domin ba ni da kirki in har zan sanya kara ki tsallaka, saboda iskanci na kashe maƙudan kuɗi na aure ki, amma kawai mutane ne bana so sai ki kasa bin umurnina, ina matsayin mijinki."
Kuka sosai take amma bai kula ba ya shige bayi yana faɗin,"Ki je ki kawo mini abinci."
Da ta fita daga cikin ɗakin ta shiga kicin. Jingina da ƙofar ta yi bayan ta kulle, tare da fashewa da kuka.
"Allah na gode bisa jarrabtar da ka yi mini na miji irin Faruk. Allah ka bani ikon cinye wa."
Gyaran muryar da ya yi a falo, ya sanya ta goge hawaye tare da fitowa bayan ta haɗa masa abinci.
"Tun da kika ba ta abinci yau sai dai ki kwana da yunwa." Ya ce mata cikin ɓacin rai.
Ta ɗauka wasa yake, amma bai ba ta abin da za ta girka ba. Ba wani yunwa take ji ba, amma ranta ya ɓaci sosai.
Bayan ta yi sallah ta kwanta tana ta jan carbi a hannunta.
Shigowa ɗakin ya yi, tare da tsayawa a bakin ƙofa.
"Ke fa ba yarinya na ce, da sai na rinƙa binki, kuma ina koya mini yadda ake zama da miji. Ko ba ki san matan aure gayu suke ɗauka da kayan bacci masu ɗaukar hankali ba, suna zuwa turakar miji?"
Shiru ta yi ba ta ce masa komai ba. Ganin haka ya ɗora da ce wa,"Ki shigo ɗakina ina jiran ki, kuma in har kika taho da hijabi wallahi dai kin raina kanki, don ban ga uban da kike ɓoyewa ba, wanda ban gani ba."