← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 92

Sashe 13

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri suka tsaya inda suka ga Faruk, a tsaye da gilashi a idanunsa yana kallonsu. Fara tafiya suka yi wanda ya sanya ta ƙara sauri ya isa in da suke.

"Haba 'yan mata taimako zan yi fa. Ku kalli garin yadda hadari ya ƙara lulluɓe shi, kuma in kwana za ku yi da ƙarfi ku samu mota, don haka ku zo na rage muku hanya. Ni ma na tashi aiki zan koma gida." Ya ce yana kallon Nasreen da hasken mota yake gaskata.

"Karka damu za mu samu napep. Thanks for your help." Nasreen ta ce tare da kama hannun Fadila.

"Haba Nasreen, kina gani mun kusa awa ɗaya muna jiran napep babu. Don Allah ki zo kawai mu shiga."

Shiru ta yi tana kallonta don ko ita za ta so ta shiga.

"Ku shiga wallahi bani da nufin na cutar da ku. Ma'aika ci ne a makarantar." Ya faɗa tare da nuna musu identity card ɗin sa.

Za ta yi musu Fadila ta ja hannunta, tare da buɗe mata motar. Baya ta shige ta bar Fadila wacce dole ta shiga ciki.

Suna shiga aka cigaba da ruwan mai ƙarfi.

"Kun ga na taimak ko? Da yanzu ruwan sama ya yi muku dukan tsiya, kuma na san wacan mara ƙibar za ta fara ciwo. Kin san dogaye ba sa son ruwa." Ya faɗa cikin tsigar tsokana.

Fadila ta yi dariya, amma ita ƙara ɗaure fuska ta yi tana kallon hanya.

"Ko zan iya sanin sunanku?"

"Ni sunana Fadila ita kuma Nasreen."

"Wow, nice name." Ya ce yana girgiza kansa.

"Ni kuma sunana Faruk, ina zama a Zangon Shanu Hayin Jarumi.

"Allah Sarki. Mu kuma duk a samaru muke."

"Ni ma mahaifiyata a samaru take zama, amma yanzu tana Saudiyya. Samaru shi ne ainihin family house ɗinmu. Kwananan na gama ginin gida ina neman matar aure."

"Allah ya ba ka ta gari." Fadila ta ce masa cikin sakin fuska.

"Ai kamar na samu in har za ki bani ƙawarki, ko da yake kamar haushina take ji, kin ga tun da ta shiga cikin motar ba ta magana."

Dariya Fadila ta yi."Ikon Allah! Daga ganin Sarkin Fawa sai miya ta yi zaƙi?"

Shi ma dariya ya yi ba tare da ya ce komai ba.

Nasreen kuwa ƙara tsuke fuska ta yi don sam bai yi mata ba.

"Da gaske na ke yi za ki bani ita?"

"Allah zai ba ka in kuma ta amince."

"In Sha Allahu! Ai ba za ta watsa mini ƙasa a ido ba ko Nasreen?" Ya ja sunan yana tambayarta.

Ba ta tanka musu ba ta ci gaba da tunaninta.

"Amma kamar ba zan samu matsuguni ba? Duba ga yadda take haɗe rai?"

"Kar ka yi mata mummunar fahimta. Haka take ba ta cika magana ba, kuma bayan nan ka ga daga makaranta muke har da distress."

"Haka ne." Ya ce ba tare da ya ƙara cewa komai ba.

"Ka sauke mu a nan mun gode." Ta ce mishi tare da nuna gurin.

"Nan ne unguwarku?"

"Eh, amma unguwar da nake zaune. Ita na ta akwai nisa ba sosai ba." Cewar Fadila.

"Ok, bari na sauke ki sai na kaita."

"No, na gode bana buƙata." Ta faɗa da sauri tana ƙoƙarin buɗe motar.

"Kwantar da hankalinki bana cin mutane." Ya ce tare da fitowa.

"To 'yanmata tun da ruwa ake ba zamu iya magana ba. Don Allah ko zan samu numba?"

"Ba ta da waya sai dai na ba ka numbata."

"Kamar ki ba ki da waya?" Ya yi mata tambayar yana kallonta

Haushi ya sanya ba ta ba shi amsa ba, ta fara tafiya.

"Bari na ba ka yawa kusan tare muke in ka kira sai na haɗa ku."Ta ce tare da ciro wayarta tecno mai botira ta gaya masa ya kwashe.

"In ta amince zan siya mata wayar." Ya faɗa tare da kwashe numbar da ta ƙara to masa.

"Kyawawan 'yan mata mu tashi lafiya." Ya ƙarashe maganar yana murmushin sannan ya buɗe motarsa.

"Kin bani haushi haba ni ban san ba ki da aji ba, sai magana kike da shi kamar ba mace ba."

"Ya taimaka mana sai na wulaƙanta shi? Da bai ɗauke mu ba, wataƙila da yanzu muna can kan hanya ruwa ya cika mu, kuma kin ga kuɗin da na so na yi mana kudin napep gobe ko gurasa ma ci."

"Haka ne." Ta ce tana gyara jakarta.

"Amma gayen da motarsa har da ƙamshinsa sun yi."

"Ni kuma sam bai yi mini ba, saboda yana da arha da yawa ga surutun tsiya."

Ta buɗe baki za ta yi magana ta katse tare da rugawa da gudu.

"Kin ga ruwa ya fara dawowa sai gobe."

Murmushin ta yi tana kallon yadda take gudu har ta ɓule.

Nasreen har ta manta da zancen wani Faruk, tare da mayar da hankalinta kan karatun. Bayan kwana biyu da kaisu gida da ya yi.

Suna tafiya za su makaranta Fadila ta kalleta."Kin san ko wannan mutumin ya kira?"

"Wake nan?" Ta yi mata tambayar domin har cikin zuciyarta ta manta da shi.

"Ba na son wulakanci. Wannan mutumin da ya ɗauke mu, ko nifinki har kin manta alkhairi da?"

"Oh, wallahi na manta da shi. Gaye za ki ce mini. Ba ki ga shigarsa ta matsu bane?"

"Kai ke dai kin cika sa'ido wallahi. Ya kira ni yana son magana dake."

"Kin ga Fadila. Ya kamata ace kin gaya masa ni ban shirya aure ba, saboda ba zan watsa wa Ya Ahmad ƙasa a ido ba, na kasa ci gaba da karatuna."

"Karatu yana hana boko ne? Ni kawai ina miki sha'awar shi ne, saboda yana da abin yi, kuma yadda yake ɗan boko zai tallahi karatun ki, sannan Ya Ahmad zai samu sauƙi."

"Kawai bai yi mini ba don Allah ki sanar masa." Ta ce tare da yanke fuska tana kallonta.

Ganin yadda ta sha kunu ya sanya ta bar zancen, amma a ranta tana mata fatan ta aure shi, domin ta so ace ita ya ce yana so.

Faruk kuwa ya kasa sukuni saboda lokaci guda soyayyarta ya hana shi sukuni. Duk da lokacin ba wani fuskarta ya gani sosai ba, amma muryarta da natsuwarta sun tabbatar masa da kyakkyawan gaske ce. Da ma burinsa ya samu mace mai kyau kuma fara doguwa.

Duk yadda ya so Fadila ta haɗa su abin ya ci tura. Bisa umurni da ta ba ta. Cikin kwantar da murya ya, ya yi nasarar roƙon Fadila har ta amince za ta kai su gidansu.

Da bisa ni da ya ga gidan ransa ne ya ɓaci. Ya rinƙa kallon gidan a wulaƙance, wanda har Fadila ta so ta fahimci hakan.

"Bari na shiga na kira ta."

"Wai tsaya." Ya dakatar da ita yana faɗin haka tare da ma gidan wani irin kallo.

"Wai kina nufin Nasreen a wannan gidan take rayuwa?"

Tambayar ya yi matuƙar ba ta mamaki."Eh, ko na fasa kiranta ne?" Ta tambaye shi tare da canza fuska ganin lamarinsa da rainin wayo.

"No, ba haka nake nufi ba, amma don Allah ɗan bari sai gobe." Ya ce yana sosai kansa da makullin mota.

"Ok, ba damuwa." Ta ce za ta shige cikin gidan.

Har ya fara taki sai ya ja ya tsaya saboda sonta da ya ji ba zai haƙura da shi ba.

"Fadila," Ya kira sunanta da sauri ganin za ta shige.

Fasa shigar ta yi ta ja ta tsaya, tare da juyowa tana kallonsa, sai kuma ta dawo gabansa ta tsaya tare da tamke fuska.

"Kira mini ita Please." Ya ce tare da haɗa hannunsa.

"Ok," Ta amsa sannan ta shige cikin gidan.

'
"Yanzu yarinyar wannan gidan zan nema da aure? Kai impossible!" Ya bawa kansa amsa.

"Mai za su kawo mini kuma abin kunya ne ace kamata Ummar Faruk zan auri 'yar gidan nan, amma dai bari ta fito." Ya furta a ransa idanunsa ƙyar a bakin ƙofa, burinsa kawai ta fito.

Fadila ta shiga gidan da sallama. Babu wanda ya amsa mata, domin kowa harkar gabansa yake yi. Ganin haka ya sa ta nufi ɗakin su Nasreen.

Tana zaune a falon da babu komai sai siminti. Shi ma duk ya gyabure. Ganinta ya sanya da ta kai ƙarshen ayar ta tsaya tana murmushi.

"Sahiba."

"Na'am, da baƙo ki ka yi a waje."

"Baƙo?" Ta yi mata tambayar cikin mamaki.

"Eh, Ummar Faruk ne. Wallahi ya hana ni sukuni dole sai na kawo shi gidanku, wai yana son ya yi maganar ƙarshe da ke."

"Kuma sai ki jawo shi har ƙofar gidanmu? Kin taɓa ganin na yi zance? Ko so kike ran Ya Ahmad ya ɓaci?"

"Don Allah ki yi haƙuri ki zo ku yi magana kawai ni ma ya daina mini naci." Ta ce tare da miƙewa tana jan hannunta.

Ƙwace hannun ta yi." Ki je ki ce masa ba zan zo ba."

"Haba ke kuwa. " Ganin da gaske ba za ta je ba ya sanya ta shiga ciki inda Mama take ninke kayanta.

"Don Allah Mama, ki ce Nasreen ta fita ta gaya mata ɓakonta ba yanzu za ta yi aure ba." Ta faɗin haka bayan ta gaishe ta.

Murmushin ta yi."In ban da abinki zama za ki yi ta yi a gida? Ma za tashi ki je, kuma kika yi masa wulakanci ni da ke ne."

Zuɓɓura baki ta yi tare da miƙewa tana hararar Fadila.

Hijabinta ta janyo suka fita."Zan gaya masa ya fita harkana, in kuma ya ƙi zan shuka masa rashin mutunci."

"Eh, gara ki yi masa ni ma ya shafa mini lafiya." Fadila ta furta haka.

Nasreen ja ta yi ta tsaya gefensa can nesa da shi.

"Assalamu alaikum." Ta yi masa sallamar cikin ɗaure fuska.

Juyowa ya yi da sauri yana kallonta. Dama ya ƙosa da kuma ɓacin rai ganin sun shanya shi kamar kayan wanki. Shi mutum ne wanda sam ya tsani jira.

Idanu ya zuba mata yana kallonta kamar zai cinyeta.

"Eh, tabbas kyakkyawar gaske ce. Sam ba ta dace a ce daga gidan nan ta fito ba." Ya furta hakan yana mata kallon tun daga sama har ƙasa.

Ranta ne ya ɓaci ganin kallon up and down da yake mata."Ina wuni?" Ta furta tare da cuno baki.
Chapter 13 · 0% Book details