← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 92

Sashe 67

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasreen satan kallon idanunsa ta yi. Ganin kallon tuhuma yake mata a tunainta, aikin da bata yi masa ba ne zai yi ƙorafi kamar yadda ya saba."Am sorry Ya Damir aikin Ingawa ne ya ba ni, kwana biyu ban yi ba, kuma ya gaya mini a ranar yake so zai tura..."

Ransa ne ya ɓaci, jin abin da tace har da wani gulmar ce masa Yaya, saboda hakan yayan da ta ce masa bai zama unique a gurinsu ba, ganin ko wane karabiti yana samun matsayin yaya.

"Aikinsa yafi nawa ne?" Ya tsinci kansa yana tambayarta cikin daga murya

Da sauri ta cire ido ta kalle shi ganin ya yi fushi lokaci guda.

"A'a ka yi haƙuri." Ta furta da muryar da ya sauko da fushinsa.

"Daga yau duk wanda ya baki aiki, in har na kawo nawa a ranar kar ki sake yi, ki mayar mishi da aikin."

"Ok sir." Ta furta a hankali tana kallonsa.

Guntun tsaki ya ja, saboda sir da ta kira shi dashi ya ƙara ƙular da shi. So yake ya ji ta kira shi da sunan soyayya, sai kuma ya shafa kansa yana murmushi ganin ya cika zaƙewa.

Nasreen kuwa kallonsa ta yi, tana tunanin anya bai zare ba, saboda ganin lokaci guda ya yi fushi sai kuma ya yi murmushi.

Ɗan tsorata ya yi ganin yadda take kallonsa kamar xararrre. Shi kam ya manta da ita zuciyarsa ta faɗa kogin tunani.

"You can go I know what I will do." Ya ce mata ba tare da ya kalle ta ba.

Jin haka ta murɗa ƙofar ta fice tana mamakinsa.

Tana fita sai ya saki murmushi tare da buga hannunsa."Anya zan iya tunkararta da soyayya, ganin yadda na susuce na rikice kamar ba Damir wanda mata da yawa suke crushing ɗina ba?" Tambayar ya ƙarashe yana shafa kansa.
"Mai ya sa take mini kwarjini?" Ya kara furtawa yana kallon ƙofar da ta wuce.

Nasreen kuwa, tana fita ta je ta ji abinci hankalinta kwance batare da tunanin komai ba, sannann ta koma ofis ɗinta ta ci gaba da aiki.

Da ya koma gida, sai ya kasa sukuni kalmar ina wuni da ta furta masa yake ta masa kuwwa. Wanka ya yi sannan ya fito falo.

Marwana tana zaune tana waya da Ahmad, wacce take jin kamar yanzu a ɗaura. Ganin yana saukkowa ta yi masa sallama, tare da ije wayar, bayan ta sanar mishi da za ta kira shi.

"Sannu da saukkowa Ya Damir."Harararta ya yi, ganin tana soshe-soshe alamun bata da gaskiya. Ba tare da ya amsa ba ya zauna kusa da ita.

So yake ya samu numbar Nasreen a wayarta, amma ba ya son tambayarta. Yana zaune yana ta kallonta yana son ta ɗauki wayar ta fara dannawa, sai ya aike ta ya kwashe numbarta, amma sai ya ga ta riƙe wayar ta mayar da hankalinta kan tibi.

Sun daɗe a haka tana jiran ya tashi ta ci gaba da wayarta. Ganin ya zauna har da ɗora ƙafarsa kan stool sai ta gane ba yanzu zai tashi ba.

Wayarta ta ɗauka, ta buɗe data sannan ta fara yi wa Ahmad magana ganin yana kai.

"Go give me water." Ya furta da sauri yana kallonta.

"Ok," Ta ce tare da miƙewa za ta nufi kofin ta ɗauko kofi.

"Zo ki ije wayar nan, saboda in kika tafi ban san lokacin da za ki dawo ba. Na lura kwana biyu gabakiɗaya hankalinki na kan waya."

Da sauri ta ije ba tare da ta ce masa komai ba. Tana fita ya ɗauki wayar. Saboda kar ta kama shi da wayarta, so ya duba numbar ya ga an sanya mu sister tare da heart na stikers. Da sauri ya tura a Whatsapp ɗinsa, ya yi maza goge tare da gogewa ya ije wayar.

Marwana har ta shigo sai ta ganshi da wayar yana dannawa, ganin bai ganta ba ya sanya ta koma baya sannan ta yi masa sallama yadda zai ji ta shigo. Mamaki sosai ta yi, tare da tunanin dalilin da ya sanya shi ɗaukar wayar. "Ga ruwan." Ta ce mushi tare da ije wa kan stool tana masa kallon tuhuma.

"Ok," Ya ce tare da tsare gida ganin kallon da take masa.

Mantawa da an kawo masa ruwan ya yi, yana ta tunanin yadda zai fara mata magana."Na kira ta ne ko na yi chatting ɗinta?" Ya furta cikin ransa.

"To ina kirata na ce mata me?" Ya kara yi wa kasa tambayar.

Miƙewa ya yi cikin damuwar rashin abin da zai ce mata. Mamaki sosai ta yi, ganin ya ƙi shan ruwan har ya fara hawa stairs ta ce,"Your water."

"Oh!" Ya ce tare da dawowa ya ɗauki bottle ɗin.

Idanu ta raka shi da shi har ya shige."Something is definitely fishy." Ta ce tana mamakin canzawar da ya yi. Wayarta ta ɗauka ta shige ɗakinta don kar ya zo ya ƙara takura mata.

Damir bayan ya shiga cikin ɗakinsa ya kulle tare da sanya ɗan makulli. Safa da marwa yake yi, yana tunanin mai zai ce mata in ya kirata. Ije wayar ya yi cikin damuwa, rashin abin da zai ce yana kallon numbarta da ya haddace a yanzu.

"Your numbers is special as you are special too." Ya ce ganin numbobin ba su da wuyan haddacewa.

Kwanciya ya yi, tare da ɗora wayar a ƙirjinsa yana ji tamkar ita ya rungume. Ya daɗe a haka yana tunanin mafita, sannan ya ake waya ya fasa kira dai dare.

Kafin ya samu courage, na kiranta zuciyarsa ta gama azabtar da shi da tunaninta. Da ya rintse idanunsa ita yake kallo more especially wannan kissable lips ɗinta.

Sosai ya yi mamakin kasa ganin tunaninsa na son haukatar da shi.

Kafin dare yayi, duk ya ƙosa saboda ji yake kamar ya jawo kiran sallar magariba. Ya rinƙa kallon agogo yana jan tsuka, tare da jin haushin ladanin ganin ya ƙi kiran sallar da wuri.

Ana kiran magariba ya fice masallaci. Zama ya yi yana ta lazimin nasara har aka kira Isha yi sannan ya yi.

Ko da aka yi masa maganar abinci kasa ci ya yi, saboda ji yake ba ya son cin komai. Burinsa kawai ya ji zazzaƙar muryarta ta doki kunninsa.

Sai dai abin takaici, duk wannan ɗokin yana hawa gadon ya rungume filo, sosai a ƙirjinsa yana jin kamar ita ya rungume.

Layinta ya kira zuciyarsa na bugu, amma sai yar baturiya ta fara masa turanci tana gaya masa tana another call. Saboda takaici da kishi da suka rufe masa ido,har ya ɗaga wayar zai buga da ƙasa, sai ya fasa tuna maƙudan kuɗin da ya siya, da kuma abubuwa masu mahimmanci da suke ciki.

Tsaki ya yi, tare da jifa da filon amaimakon wayar. Ransa ya ɓace hankalinsa ya tashi.

"Da wa take waya? Tsohon mijinta ko wannan mayun Annur da Ingawa?" Ya tambayi kansa cikin takaici.

Kashe wayar tasa ya yi, sannan ya koma gadon ya kwanta, kamar wani marayan zaki. A ranar sai dai bacci ɓarawo ya ɗauke shi, domin ya kasa ba ci ga shi ya kasa ƙara kiran layin, yana tsoron kar ya kara jin tana wayar har zuwa lokacin, saboda a yadda yake ƙunsa zuciyarsa za ta iya bugawa.

Da ƙyar ya samu ya rintsa shi ma, don daa ya yi ta sallah yana karatun Alqur'ani, sannan ya samu bacci mai nauyi ya ɗauke shi, da tunanin sun yi auren suna cikin rayuwar su na soyayya har ta haifa masa yara.

Da ya farka rintse idanunsa ya yi don ya koma, domin ya ci gaba da mafarkin hugging ɗin ta da ya yi, amma iya ƙoƙarin da ya kasa, sai ma jikinsa da ya fara ciwo. Yana nan yana tunani aka kira sallah, sannan ya miƙe zuwa bayi don ya yi wanka ya fita Masallaci

A maimakon ya ji haushi, ta fita a ransa sai ya ƙara jin mugun ƙaunarta, tare da jin ƙarfi da jarumtar fitowa a fafata da shi don ya ɗauke abarsa.

Tunanin inda zai samu hotonta ya fara yi, saboda idanunsa da suke masa ƙaikayin son ganinta. So take da ya yi aiki ya kalle ta don ta ji ƙarfi a jikinsa.

Tunawa da Marwana ya san tana ta hotunanta sosai. Da sauri ya sanya jallabiya ya fito saɓanin da yake zaune da gajeren wando iya gwiwa.

Tana ɗakin momi da waya a hannunta ya shigo."Wai ke uban me kike yi kullum da waya a hannu?" Ya daka mata tsawar da ya firgitata, domin ba ta san ya shigo ba.

"Babu komai." Ta ce masa tare da aje wayar.

"Ba ni in duba saboda ban yarda dake ba."

"Saboda me Damir? Na ga tana da kula kuma sam ba ta kula samarin shaho?"

"Mommy kar ki yabe ta ki bari kawai na duba, kin san ba a yabon ɗan kuturu..." Ya ce mata tare da amshe wayar yana harararta.

"Ai na yi tunanin kamar ta ƙara samo mini suruki ne, saboda yadda na ga tana murmushi. In dai kin samu wanda kike so ne sai ku je ku yi gwaji jini kar yi na Ashaman.

"Ai tun da Allah ya kawo mini wannan da shi za a yi in sha Allah." Ta furta a ranta amma a fili sunkuyar da ka ta ta yi cikin kunya, wanda ya ƙara tabbatar wa Mommy da zarginta har ta yi murmushi.

Amaimakon ya duba, sai ya sanya wayar a silent ya kunna data. Gallary na ta ya shiga, inda ya ci karo sosai da hotunnanta. Da sauri ya tura da yawa, sannan ya goge ya miƙa mata. Ba tare da ya ce komai ba ya fice. Kallo suka bi shi da shi har ya fice.

"Anya Ya Damir ba satan mini kuɗi yake yi ba?" Ta yi tambayar daidai lokacin da Muhsin ya shigo.

"Ke! Ya Damir kike zargi da sata, uban me zai yi da kuɗin ki?"

"Abin ne da mamaki wai yaro ya tsinci haƙori. Jiya na kama shi yana duba mini waya bayan ya aike ni. Yau kuma ya karɓa amma bai ce komai ba."

"Amma kin san babu abin da zai ci da wasu yan ƙalilan kuɗinki? Ko kin ga an cire miki kuɗi ne?"

"Zargi na ke yi bari na duba alert." Ta ce tana ƙoƙarin checking balance."
Chapter 67 · 0% Book details