← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 92

Sashe 76

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin ihun da yake yi yana kira musu mugun alkaba'i har da hawaye, sai wasu daga cikin mutanen suka yarda, yayin da wasu kuma suke kallon kima da kamalarsa suke tunanin ba zai iya aikatawa ba.

Damir duƙar da idanunta ƙasa ya yi, da jini yake ɗiga sama goshinsa. Ji ya yi ya muzanta sosai.

Anya Faruk! Ko dai ciwon haukar ya dawo me🙄🙄🙄🙄

WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 40

Damir duƙar da idanunta ƙasa ya yin da jini yake ɗiga sama goshinsa. Ji ya yi ya muzanta sosai. A zuciyarsa yana ganin anya yana da maƙiyi kamar Faruk?

Cece-kucen da mutane suke yi, suna la'antarsu ya sanya shi kasa cewa komai. Yana jin kukan Nasreen yana damunsa.

"Kawai a miƙa case ɗin nan zuwa gurin 'yan sanda, idan matarsa ce sai su ƙwatar masa ita." Cewar wani dattijo a gurin.

"Eh kuma haka ne bari na kira su." Wani ya ƙara cewa, sannan suka ci gaba da maganar lamarin suna tur da halin Damir.

Jin abin da suka ce har a ciro waya za a kira su, sai hankali Faruk ya tashi."Don Allah kar ku kai lamarin gurin 'yan sanda, yana da kuɗi sosai zai basu cin hanci. Kawai ku bani matata da yarana na gudu na bar garin da su "

"Mu je na yi alƙawarin tsaya maka acan, ɗan'uwana babban ɗan sanda ne." Cewar wani ya riƙe hannunsa.

Ganin 'yan sandar sun zo, sai hankalin Fatuk ya tashi. Ya rinƙa magana da ƙarfi yana kumfar baki kar aje gurin 'yan sanda.

Ganin sun iso sai Nasreen ta shiga mota ta ɗauko wayarta, numbar Ahmad ta kira. Yana ɗagawa ta fashe masa da kuka.

Ahmad da yake zaune a falo yana cin abinci. Jin ta fashe masa da kuka sai ya miƙe cikin tsananin razana.

"Lafiya Nasreen hatsari kuka yi ina yaran?" Ya yi mata tambayar hankalinsa a tashe.

Kuka ta ci gaba ta kasa ce masa komai.

"Please ki natsu ki gaya mini." Ya furta cikin damuwa daidai, lokacin da Mama ta zo ta tsaya cikin tashin hankali.

"Farouk ne ya buga mana mota, kuma ya fasawa Ya Damir kai, ya tara mana mutane yana faɗin matarsa ce ni. Zi.."

"Farouk ɗin?" Ya yi mata tambayar cikin tashin hankali.

Hawaye ta share, tana kallon Damir da yake ƙoƙarin shiga cikin mota.

"Eh shi yanzu an tura mu police station."

"Innnali wa inna ilahir raju'un! Farouk ɗin yana da hankali kuwa?" Ya furta cikin tsananin mamaki.

"Eh shi don Allah ka zo Ya Ahmad. Farouk ya tozartamu ya kira mu da mazinata."

"Ya Salam. Ga ni nan zuwa ki tambayi wane police station ne." Ya ce mata tare da kashe wayar cikin tashin hankali.

"Wallahi Mama saina wulaƙanta faruk." Ya furta cikin tsananin ɓacin rai.

"Mai ya faru?"

Gaya mata ya yi cikin ɓacin rai."Faruk ya haukace. Ka saki mace kuma ka koma kana bibiyarta da sharri?"

"Ki bari kawai bari na je sai na sanya ɗaure shi." Ya ƙarashe maganar tare da ɗaukar makullin motarsa.

"Ahmad kaje da takaddar sakin karya ƙaryata."

"Kuma fa haka ne Mama kin kawo shawara ɗauko mini."Ya ƙarashe maganar bayan ya zauna.

Shiga ciki ta yi sannan ɗauko masa ya karɓa ya fita bayan ya yi sallama.

Bayan ta gama waya da Ahmad, sai ta kira numbar Marwana. Tana kicin tana haɗawa ƙanin Babansu Alhaji Sani da ya zo ganin da Mommy yana jiran Damir ya dawo.

A lokacin da kiran ya shigo tana wanke hannunta. Murmushi ta yi ta ɗauki wayar. "Hello..."

"Marwana na shiga uku!" Ta furta tare da fashewa da kuka.

"Lafiya mai ya faru?" Ta yi tambayar cikin tsananin tashin hankali.

"Don Allah ki cewa Ya Muhsin ya zo asibiti, Faruk ne ya fasawa Ya Damir kai ya kuma yi mana ƙazafi. Yanzu za akai shi asibiti, mu kuma za mu je police statio.."

"Innalillahi wa inna ilahir raju'u! Farouk yana da hankali kuwa?" Ta furta cikin mamaki.

"Ki gaya wa Muhsin ya zo Ya Damir ya ji ciwo sosai. Kuma ya kafe matarsa ce ni alfasha muke aikatawa."

"Shikenan daina kuka bari na gaya wa Ya Muhsin." Ta ce tare da kashe wayar.

Falo ta shigo jikinta yana rawa ta sanar da su. Mamaki sosai ya kama su. Mommy ta miƙe cikin tsannanin tashin hankali.

"Yanzu Damir yana ina?"

"Asibiti Nasreen tana police station."

"Ikon Allah ka saki mata, kuma ka yi ta bibiyarta?" Mommy ta ce.

Muhsin ya miƙe ya ce,"Bari na je."

"Ai ni ma dole na je." Cewar Alhaji Sani.

Bayan sun fita sai Mommy ta ce,"Marwana mu je asibitin ba zan iya zama ba."

Ɗaukar makullin mota ta yi suka bi su.

Ahmad ya fara isa police station ɗin. Tana tsaye tana kuka, ganinsa da gudu ta rugo ta faɗa jikin shi.

"Ki yi shiru ki daina kuka, wannan shi ne na ƙarshe da zai ƙara shiga rayuwarki."

"Ya tozarta mu ya ce mana zina muke yi, tsakanina da Faruk sai dai na barshi da Allah." Ta furta tana share hawaye

Hannunta ya kama, suka shiga cikin police station ɗin. Farouk yana ganinsa jikinsa ya kama rawa, musamman ganin yadda fuskarsa ta yi.

Kumfar baki yake yi yana borin ƙarya. Anty Asiya da mijinta sai Isma'il suka zo ta gurinsa.

A asibiti kuwa, ana dressing ciwon Muhsin da Alhaji Sani. Da sauri suka ƙarasa ganin bandeji a kansa ga kuma jini.

"Ya Damir sannu." Ya ce masa cikin damuwa.

"Please ka ce su sallame ni, Nasreen tana police station ina so zan je, tana cikin damuwa sosai."

"Y kamata a bashi bed rest ya zubar da jini. Ya kamata ya yi two days a asibiti." Cewar likita yana danna saman kansa da ya kumbura.

"No ko za a yi admiting ɗina a bari a kashe ces ɗin. Farouk ya tozarta mu ya wulaƙanta mu. Na tsane shi sosai bana son ganinsa." Ya furta cikin tsananin damuwa.

"Komai ya zo ƙarshe zan yi muku tsakani. Ya zama da sauƙi tun da an je gurin 'yan sanda."

"Please mu je in an gama sai na dawo."

"Ya Damir ka bari muje ni da Baba Sani kuma Ahmad yana can."

"No mu je ba zan iya zama ba alhalin tana can."

Ya furta tare da miƙewa yana rintse idanunsa, jiri yake gani don ya zubar da jini sosai.

"Ok mu je in an gama sai na ɗauko motarka."

"Ok,"Ya ce sannan suka shiga cikin mota.

Da suka isa suna zaune, suna jiran a gama ces ɗin wani sannan a shiga na su.

Ganinsa da sauri, tashi ta isa gurinsa hankalinta dama yana gurinsa tana tunanin halin da yake ciki.

Ba tare da jin kunya ba, ta ƙara da gurina idanunta yana kanshi.

"Ya jikin?" Ta furta muryarta da sanyi.

"Am ok Nasreen. Please stop crying." Ya ce mata yana kallonta da idanunsa da suka canza kalla.

Kallonsa sosai take yi, cikin tsananin ƙauna saboda ta ɗauka tozarcin da ya yi musu zai sanya ya janye aurenta, amma sai ta ga wani irin sonta ne ya ƙaru ganin kallon da yake mata. Ji ta yi ita ma ta ƙara jin sonsa har ba ta jin kunyar nunawa a gaban kowa.

Zama ya yi sai ta zauna a gefensa, ba tare da ta ji kunya ba. Kansa take kallo tana hawaye tuna awanni biyu kafin nan lafiya lau yake suna hira cikin farinciki, amma ga shi a sanadinta Faruk ya illanta shi.

Farouk kuwa sai zare ido yake yi. Ko da su Anty Asiya suka zo. Faɗa sosai suka haushi da shi kamar za su duke shi. Ganin haka ya fara hawaye."Don Allah ku taimake ni kuce matata ce, wallahi ina sonta ba zan iya bar masa ba."

"Ka san kana sonta ka wulaƙanta ta? Farouk gaskiya zan faɗi ba zan yi karya ba. " Ta furta masa cikin jin haushinsa.

"Ka ƙyale rayuwarta ka rasa ta har abada ba za ta dawo gurin ka ba, domin in har tana da ninya abin da ka yi mata ka ruguza ninyarta." Cewar Ismail ya dafa shi.

"Ya zan yi wallahi ina sonta." Ya furta cikin tsanannin tashin hankali.

Bayan an gama wannan ces ɗin suka shiga. Farouk ya fara magana sannan Damir sai Nasreen. Kansu ya kulle suka rasa gane zancen.

Ga shi ta ce ya sake ta har ta yi idda amma kuma ya rantse bai saki ba.

"Akwai shida ga shedar sakinta." Ahmad ya ce tare da miƙa musu takadda.

Mamaki ya ƙara kamasu sai suka lalle shi.

"Kai ka yi sakin?"

"Ban yi ba ita ce ta saki kanta don ta je ta aure shi, kuma ina son ta don Allah ka dawo mini da matata."

Kansa ya ƙara kullewa."Ina ga zamu miƙa ces ɗin nan zuwa kutu."

"Ba sai an shiga mutu ba yallaɓai. Farouk ƙanina ne kuma da gaske ya yi sakin. Zamansu ya cutar da ita na sha gaya masa dole zai yi nadama, amma bai ji ba yanzu nadamar ne ya yi a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada, domin ni da mahaifiyarmu da sauran ƙannina duk mun san da sakin...."

"Anty Asiya don Allah kar ki gaya musu gaskiya. Ni fa ban san na yi sakin ba, kuma idan na yi ai na mayar da ita kafin ta gama idda. Ku taimaka ku riƙe ta ta dawo hannunna." Ya furta kamar zarrare.

"Babu abin abin da za mu iya maka, tun da 'yan'uwanka sun bayar da sheda babu abin da za mu iya, don haka ka daina bibiyarta."
Chapter 76 · 0% Book details