Sashe 86
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"In ya warke daga haukan ba. Ai yanzu shi kansa ba shi da kuɗin da zai ci ko tsire ne, tun da ba lafiya ce da shi ba ya koma aiki."
Dariya suka kwashe dashi banda ita."Kai Faruk ya yi tsiya wallahi."
Suna zaune a a falo ya yi sallama ya shigo. Da sauri ta mike ta karɓi ledar hannunsa cikin jin kunya.
Cikin mutunci suka gaisa, sannan ya haye sama bayan sun ɗan taɓa hira, saboda yadda ya ga ta kasa sakin jiki ta tana ta wani sunne kai sai ya hau sama.
Bayan hawarsa sai Anty Sha'awa ta kalle ta.
"Nasreen kin shiga uku! Ni fa mamaki kike bani saboda kin cika kunya. Na samu irin wannan mijin wallahi agaban kowa zan nuna masa ƙauna, amma sai wani sunne kanki ki ke yi kin kore shi."
"Kai Anty Sha'awa hutawa zai yi."
"Ba wani nan mu bari mu tafi ki je gurin mijinki. Haba sai ka ce ba yar boko ba? Ki zauna kina jin kunya, wallahi wata ta yi wuf da shi yadda yake da kyau nan."
Nan take fuskanta ta canza, ita kanta ta yi mamakin haka.Kama ba ki suka yi suna dariya."Ai kuwa dole ki dage, don wallahi irin waɗannan mazan dole sai kin fetse don ki ɗauke hankalinsa."
Suna ƙoƙarin fita ya sauko. Gyaran murya ya yi suka kalle shi."Anty Sha'awa tafiya za ku yi?" Ya ce yana kallon su.
Ji ta yi kanta ya faɗi, har sai da ta kasa ɓoyewa, ganin mutum kamarsa ya kira ta da Anty.
"Eh wallahi ai mun daɗe."
"Ok bari na saya direba ya kaiku. Ga wannan mun gode da hidamar da kuka yi da biki, sai mun zo ban gajiya."
Baki suka washe cikin farinciki. Kalmar zai kawo ta abin ya ba su mamaki, domin har ta gama zama gidan Faruk ba sa tunanin ya san gidansu.
"Sai kun zo Allah ya kawo ku."
"Amin ku gaida hanya." Tare suka raka su harabar gidan har suka tafi. Nasreen sai ta ji wani sonsa ya ƙara mamaye ta. Ganin yadda ya daraja 'yan'uwanta. Suna tafiya ya kamo ta ya haɗa da jikinsa."Wato ke har a gaban mutane ba za ki iya ɓoye kunyata ba ko?"
"Akwai Baba maigadi fa." Ta ce za ta janye jikinta."
Wasu mazan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 45
"Yana ɗaƙinsa, kuma ni da gidana sai na kasa rungume matata, saboda masu aiki? Ya san dokar gidan in har zan fito yana ɗakinsa."
Shiru ta yi kawai, ganin haka suka shiga ciki tana jikinsa. Amarci ake ci sosai. Irin sosai ɗin nan, saboda duk yadda take jin kunyarsa kan dole take ɗan ɗaurewa. A wunin ranar dole ta saki da shi. Shi ya je ya ɗauko su Little Marwana da su Musaddik, suka wuni har dare, sannan ya mayar dasu. Su da tsohuwar mai aikin su sai Nasreen ta yi sati za su dawo.
A cikin satin ya koya mata sonsa na hauka. Gabakiɗaya jikinsa ne gurin zama ko kwanciya in har yana nan. Duk kunyar sa da take ji, a cikin satin ya cire sai wanda ba a rasa ba. Sosai ya yi ƙoƙarin cirewa, domin ta saba dashi kafin mai aiki da su Little Marwana su dawo.
Ranar da ta yi sati Damir ya kaita gidan Marwana. Saboda farinciki kuka suka saka. Ba tare da sun ƙara bi ta kansu ba, suka shige ciki har da kulle ƙofa.
Damir da ba ya iya zaman mintina bai ganta ba ya ce,"Sun shige ciki Allah ya sa ba gulmarmu suke yi ba?"
Dariya Ahmad ya yi domin ya san an gama komai."Allah ya kyau kawai." Ya ce sai suka kwashe da dariya.
"Dama ai kowa ya sai rariya, ya san za ta zubda ruwa." Cewar Damir.
"Sosai kuwa Marwana da Nasreen haɗin Allah ne."
Hira suke yi yawancin hirar kan business, da yada ƙasar mu ta zama. Ko abinci sai dai Ahmad ya ɗauko musu, amma tun da suka shiga suke ƙus-ƙus.
"Nasreen anya ba ki harbu? Dubi yadda kika koma, ke da nasan ba ki da haske sosai, amma kin dawo fara tass."
"Yayan na ki ne babu dama, in har na harbun ba zan musa ba."
"Sosai ni sheda ce Ya Damir akwai kula da mace. Shi ya sa tun lokacin da na haɗu dake naga Faruk yana wulaƙanta ki, sai na yi miki sha'awarsa, saboda mai irin halinsa zaki aura ki gane WASU MAZAN sun bambamta da wasu."
"Tabbas Marwana na sheda. Na gode da kika haɗani da jarumin na miji kuma gwarzo. Ina alhafari samun sa a matsayin miji."
"Ni ma godiya zan yi miki Babyna akwai kula."
Dariya suka yi a tare. Damir ya ɗaga waya ya kira ta, saboda in har ya ƙyale su, ƙila ba su da ninyar fitowa.
Suna fitowa ya harareta."Da ba za ku fito bane?"
"Za mu fito Ya Damir muna hira ne."
"Nasreen ce ta tsareta da surutu saboda hira ne da ita, amma babyna babu ruwanta ko?"Ya ƙarashe maganar yana kallonta"
"Kai Ya Ahmad wato har ka manta da ni ka daina siding ɗina?"
"Saboda yanzu kina da wanda zai tsaya miki. Kin samu bango abin jingina."
"Ƙyale shi babyna. Matarsa ce mai surutu ni sheda ce. Wataƙila har labarin yarinyarta sai da ta baki."
Dariya suka ƙara sannan suka yi sallama suka tafi. Daga gidan sai ya wuce da ita gidansu. Murna sosai ta yi don bai gaya mata ba. Rungume su Musaddik ta yi kamar zata cinye su.
Cikin jin kunya suka gaisa da Mama."Mijin ki ya kira Zainab ta haɗa kayansu Raihan zai riƙe su?"
"Ai ya kira ku?"
"Na ɗauka kun zo ɗaukar su ne?" Ta yi mata tambayar a maimakon amsa.
"A'a bai gaya mini ba, amma na san ya ce za su dawo."
"Aiko ɗaukar su kuka zo yi, saboda har an haɗa musu kaya."
Murna sosai ta yi cikin farinciki. Mama ta yi mata nasiha sannan ta ƙarashe da cewa,"Yanzu kika yi aure mijin ki ɗan albarka ne, ki yi masa biyayya."
"In sha Allahu Mama."
Sai da za su tafi, sannan ta ga an fito musu da kaya. Kallon sa ta yi, ya ɗauke kansa. Sosai kullum yake ƙara mata sonsa. Ko yanzu sai da ya yi wa mutanen gidan kyautar kuɗi.
Su Raihann daɗi sosai suke yi ganin za su koma gurinta.
Gidan Mommy suka wuce, wacce ta yi kamar za ta goya ta. Kunyarta take ji sosai. Little Marwana murna take yi, za ta koma gidan daddy da sabuwar Umma, sannan ga 'yan'uwa da aka kawo mata.
Sun daɗe a gidan Mommy har dare ya yi, sannan suka yi mata sallama suka tafi. Saboda sun yi dinner wanka ta yi wa yaran Damir ya shirya su suka kwanta.
Tana zaune a falonsa ya shigo ya zauna a gefenta."Zo muje mu kwanta baby ina son na je campany, saboda na dan yi aiki za mu je honeymoon."
Dariyar jin daɗi ta yi, sannan ta miƙa masa hannu ya miƙar da ita. "Ina sonka mijina." Ta ce masa cikin shaukin so bayan ta rungume shi.
"Da gaske kina so na?" Ya yi mata tambayar kamar bai yarda ba.
"Eh Husband babu abin da nake so kamarka."
"Ni fa ban yarda ba." Ya ce tare da ture ta cikin wasa.
"Allah da gaske kai ne duniyata." Ta ce masa tana ƙoƙarin haɗa bakinsu.
"Da gaske?" Ya tambaye ta cikin shaukin so ganin abin da take shirin yi.
Ba ta ba shi amsa da baki ba, sai dai ta ɗaga masa kai, sakamakon haɗa bakinsu da yi.
"To ki nuna mini yau Please ki cire kunyata kin ji?"
"Tom haskena." Ta ce har cikin zuciyarta domin ta shirya kyautata masa.
"To shikenan bari na tabbatar." Ya ce tare da ɗaukar ta kamar wata baby zuwa ɗaki.
Tabbas ta shayar da shi mamaki, domin ta nuna masa ita mata iya soyyayya. Sun shayar da junansu farinciki.
Washegari da safe, shi ya tashi ya shirya yaran sannan ya haɗa musu breakfast suka ci. A lokacin da ta fito mamaki ya kamata sosai.
"Morning baby?" Ya ce mata yana ɗure da Apron.
"Husband..."
"Kar ki yi ƙorafi domin na saba taimakawa matata. Wani lokacin ni nake yin komai, duk da cewar muna da mai aiki. Ina da sha'awar taimakawa matata. Na yi wa yaran breakfast yanzu na mu na ke haɗawa."
Hawayen farinciki ya wanke mata fuska."Don't cry just smile you deserve it."
"I love you mijina." Ta ce tare da rungume shi ta baya.
Duk yadda ta so su yi aikin tare ya ki, sai dai ya ja mata stool ta zauna tana zuba masa surutu. Yana ta murmushi yana kallonta har ya gama.
Da kansa ya ciyar da ita, sannan suka saukko falon ƙasa inda su Little Marwana suke wasa. Shiga cikin su ya yi yana taya su, musamman Musaddik da bai gama saki da gidan ba.
Tana zaune tana kallo. Sallama ya yi mata zai fita. Ita da yaran suka fito suka rako shi. A gurin motar sun daɗe ana hira sannan ya yi musu sallama ya tafi.