Sashe 87
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Komawa ciki suka yi suna kallo. Wayarta ta ɗauko za ta karanta wani littafi, da Maman Muwaddat ta tura mata mai suna "ƘIYYAYYAR JINI". Sabon littafin Jamila Lawal Zango. Tun kafin ta yi nisa a labarin ta fara cin dariya da ganin wautar Jimmalo. Tun da take ba ta taɓa ganin ƙazamiya kuma ballagaza irin ta ba, sannan kuma ba ta taɓa ganin namiji mai izza irin Captain Aliyu ba. Duk yadda Ya Damir yake da shan ƙamshi da class ya shanye shi. Ga rashin haƙuri da zuciya kamar kuturu. Ƙosawa ta yi ta yi nisa cikin labarin don ta ga inda za a yi zaman doya da manja a rayuwar aurensu, saboda ta san babu yadda za a yi a haɗa zuma da maɗaci. Captain Aliyu da yake da ciwon tsafta da kuma amaryarsa Jimmalo. Lubaynah za ta zuba idanu kenan ya cuci rayuwarta? Gaskiya Captain Aliyu fuska biyu ne da shi, wanda ya sanya rushe yardar dake tsakaninsa da iyayen sa, kuma ya zama silar canzawar ƙaddarar rayuwarsa. Sosai ta zaƙu, ta ga yadda za a kwashe a ƙarshen labarin.
Baba rayuwa ta canza duk da Ahmad baya taimaka masa, amma ya canza ya yi ƙiba ya yi kyau, saboda cimar da yake yi. Nasreen yake tursasawa ta yi mishi kaya, don ko da bikinta sai da ta yi mishi kala uku, har da takalmi da hula.
Ɗaya daga cikin yaransa mai suna Aminu, amma ba haka ake kiransa ba, saboda ya canza suna tun da ya shiga harkar shaye-shayen da dabanci, domin farauta yana yi. Ya koma suna Goje. Sosai yake hurɗa da 'yan daba, sam ba shi da mutunci, domin shi ya yi ƙaura da gidan. In ya nausa ya bar gari ba a kara jin duriyarsa sai ya dawo.
Ko da Ahmad ya dawo. Ya yi da shi ya canza rayuwarsa, amma ya ƙi kan dole ya haƙura ya na masa addu'a, domin ya yi nisa ba ya jin kira.
Watarana faɗa ya shiga tsakanin su, a dalilin ƙanwar abokinsu da shi Goje yake so, amma mahaifin su ya yi musu zagin fitar arziki har ya kira shi da ɗan daba, sannan ya sanya manemin aurenta ya fito aka sanya rana.
Takaicin abin da ya yi ma abokinsa, suka je suka yi masa duka shi da mabiya bayansa, sannan suka gudu domin sun san dole su ɗau fansa.
Hankalin iyalansa ya tashi, ganin har sun ji masa ciwo sun karya shi. Cikin ɓacin rai suka neme su, amma sun gudu. Kai tsaye suka je suka samu Baba, yana zaune yana shan rediyo suka fara dukansa.
"Kawai tun da ya gudu ga ubansa nan, ai dama ni ma mai dadtin hula ya taɓa. Wallahi mu karya shi sai na bi iyayen sauran na yi musu dukan mutuwa." Ɗansa Baushe ya ƙarashe maganar tare saukar masa da naushi a baki. Jini ya fara zuba yana ihu yana ba su haƙuri, amma ba su kula ba, har sai da suka yi masa karaya biyu. Hannu da kafa sannan suka farfasa masa jiki.
Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka je suka sanar da iyalansa. Ko da akwa washe shi zuwa asibiti ya riga ya suma.
Sai da ya daɗe, sannan ta farfaɗo da ihu yana tsine musu albarka.
"Maman Ahmad, kina ganin yadda su ka yi mini wallahi sun kashe ni, saboda hatta gabana sai da suka illanta. Wayyo na mutu na lalace."
"Fansa suka ɗauka Baba Aminu ya ja maka. Kana da labarin dukan da suka yi wa ubansu."
"To ni na duke shi da za su kashe ni? Su je can su kama shi mana?"
"In baka duke shi ba, ai kai ka haife shi ka kasa bashi tarbiyyar da zai girmama uban wani. Abin da na ke yi maka kuka kenan, yau ga shi ka haifi ɗan kuka. Da ace ka inganta rayuwarsa duk haka ba zai faru ba." Mama ta ce tana kallon sa cikin rashin tausaya.
"Wayyo abin da za ki ce kenan? ba kyau tausaya mini kalli yadda suka ƙassara ni."
"Allah ya ba ka lafiya, amma duk abin da ya faru da laifinka."
Ihu yake yi yana kuka, saboda ko ina na jikinsa ciwo suke mishi. A lokacin da za a yi gyara karayar har fitsari a wando ya yi. Ya yi ihu har muryarsa ta dusashe. Duk halin da yake ciki har aka wuni Ahmad bai zo ba. Hankalinsa kwance yana naniƙe da matarsa. Ko da ta ji labarin sai ta ji tausayinsa, amma tana buɗe baki ya dakatar da ita cikin tsawa.
"Kin san yadda na tsane shi? Haihuwarmu kawai ya yi, ya barmu muna garari. Ba tare da ya bamu abinci da ilimi ba. Duk abin da ya faru da shi babyna ya cancanta, don haka kar ya dame ki."Ya ce tare da jawota ya ya haɗa da jikinsa ganin yadda ta tsorata.
"Na san komai kuma ya cancanta, amma ka yi haƙuri ya ci albarkacin haihuwarka da ya yi."
"Wane albarkaci zai ci? In da ace ban jajirce ba. Ni da Nasreen mun inganta rayuwarmu da na 'yan'uwanmu a haka za ta wulaƙanta. Baba ya cancanta ki barshi ya ɗanɗani halin da ya sanya mu."
Shiru kawai ta yi, amma ba ta ji daɗi ba, duk da ta san cewa ya cancanta.
Wayarta ta daga ta kira Nasreen. Bayan sun gaisa sai ta ce,"Kin ji labarin ne Baba ba shi da lafiya?"
"Eh muna kan hanyar zuwa ni da Ya Damir."
"Ok, Ya Ahmad na yi-na yi ya ƙi zuwa bari na ƙara rarrashinsa."
"Ki ƙyale shi a yanzu da wuya ya je domin ya yi zuciya, in muka je asibitin zan biyo."
"To Allah ya ba shi lafiya."
"Amin," ta ce tare da kashe wayar.
Da suka je halin da suka ganshi, sai da suka tausaya masa. Yana ganinta ya fashe da kuka.
"Nasreen kinga abin da ɗan banza yaron nan ya yi mini. Wallahi in zan gan shi sai na kusan kashe shi."
"Ka yi masa addu'a Allah ya shirya shi."
Damir ya ƙaraso yana gaishe shi. Asibiti aka canza masa, sannan aka sake ɗorin don bai yi ba. Kuka da ihu har ya gaji ya daina
Faruk
Farouk tun da suka tafi da shi, yana ihu yana zambarwa sai gidansa, amma sai suka ga lamarin ya wuce ƙarfin a bar shi a gida. Asibitin mahaukata aka mayar da shi, nan take suka ba shi gado. Cikin kuka Anty Asiya suka bar asibitin.
Ya daɗe yana jinya kafin ya warke, har lokacin inya tuna sai ya ji kamar zai kashe kansa. Ga shi kullum sonta ƙara nunkuwa yake yi a cikin zuciyarsa, duk da ya san cewar matar wani ce.
A ƙalla sai da ya shafe tsawon watanni yana jinya, sannan ya samu lafiya bayan an kashe kuɗi, domin hatta motarsa sai da aka siyar.
Ya yi kukan nadama, har ya gaji don dole da ya fahimci Nasreen ta yi masa nisa.
Ya zama silent, ko magana cikin 'yan uwansa ba ya son yi. Kullum ya tuna Nasreen da yaransa suna rayuwa a gidan wani, sai ya ji kamar zai kashe kansa. Da ƙyar suka samu ya koma aiki, domin cewa ya yi ya daina komai. Rashida kuwa kullum ya yi sallah sai ya roƙi Allah ya tsine mata.
Rayuwa yake cikin rashin daɗi, domin hatta iskan da yake shaƙa ba ta yi masa daɗi. Haka dai ya ci gaba da rayuwar ba tare da yana jin daɗin ta ba.
Rashida
Rashida an samu duniya, domin a lokacin da ta gudu da kuɗin ba ta tsaya ko ina ba su Legos. Kai tsaye gidan wata 'yar uwarsu ta wuce. Duk yadda Maman Iyabo, ta so ta gaya mata abin da ta yi ta samu kuɗi ta ƙi gaya mata. Ganin tana ba ta domin tun da ta zo ita take ciyar da gidan, sai ta kwantar da hankalinta suka ci gaba da cin arziki.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta sayi gida da mota, sannan ta shiga kasuwa ta sayi kaya masu kyau. Ta zama baban mace, sai facaka take yi da kuɗi abinta.
A yawonta na shaƙatawa, ta haɗu da Abdurrashiiduu matashin mai tashe. Gayen ya haɗu ga ita turanci kamar ya haɗiyi Dictionary, don ko broken ba ya yi, amma gayu ne babu kuɗi, domin anci boko babu aikin yi. Sai dai irin aikinsu na Yahoo, duk da cewar bai yi wani ƙarfi ba, don bai daɗe da shiga ba.
Tun da ta ƙyalla idanu ta ganshi sai ta susuce, domin soyayyarsa ya kamata. Da ya fahimci haka ya mayar da ita ATM ɗinsa. Duk hidimar da take mishi burinta ya aure ta, amma shi tunainsa yar da zai yi, ya yi gaba da kuɗin da ta gaya masa ta kwashe wa Faruk, saboda soyayyarsa ya sanya ba ta ɓoye masa komai ba.
Tun daga ranar, ya shiga tatsarta ta canza mishi waya da laptop. Motarta kuwa duk inda za shi da ita yake zuwa, domin yawanci shi yake tuƙata. Ita take ciyar da shi komai har kwana a gidanta yake yi.
Lumbu-lumbu ya yi mata, sai da ya tabbatar da ya san sirrinsa, kuma ta aminta da shi. Sannan ranar safiyar talata ya yi mata ƙaryar ba shi da lafiya. Magani ta tabbatar ya sha, sannan ta bar mishi gidan.
Bayan fitarta komai ya kwashe mata, sai wayarta da motar da ta fita da shi. Pin ɗinta dama ya sani. Yana cikin haɗa kayansa ta dawo ta yi mantuwa.
"Abdu- Rashiduu!" Ta furta cikin tsananin razana, ganin yadda ya yi watsa-watsa da gidan.
Cikin yare take mishi magana, tare da kai masa duka ganin abin da yake shirin yi. Ganin haka ya ɗauki ƙaton abu ya maka mata, nan take ta zube a gurin babu numfashi. Wayarta da key ɗin mota ya ɗauka ya fice daga gidan. Gaba da gabanta, aljani ya taka wuta. Cuta ta ɗau cuta kenan Allah ya shiryamu ya sa mu daina hangen abin wani.
Sai da ta yi kwana ta wuni, sannan aka gane halin da take ciki. Ko da aka kai ta asibiti ta nakasa, domin wuyanta ya karye.