Sashe 80
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da ta idar da sallar, yana zaune da waya a hannunsa da alama karatu yake yi. Ba ta san dai mai yake karantawa ba, bakinsa kawai yake motsi.
"Ina kwana? Ya jiki?" Ta ce mishi tana tsaye nesa dashi.
Hannu ya miƙa mata alamun ta zo ta rungume shi, amma maimakon haka sai ta ƙara matsawa nesa da shi. Ganin haka ya yi dariya ya amsa.
Ta yi ninyar ta koma bacci har ta fara, sai ta ji muryarsa yana kiranta bayan ya gama karatun.
Hira ya shiga yi mata tun tana gyangyaɗi har ta saki. Duk da ba wani amsa take masa ba, amma tana jin daɗin hirar sosai. Ganin yadda yake ta zuba yana bata labari.
Suna zaune har ƙarfe tara ta yi, tun tana share shi har ta saki tana dariya sosai, domin labarin dariya yake bata. Kallonsa take yi cikin tsananin ƙauna, ganin yadda yake so simple. Sosai take mamakin sa, domin duk wannan ɗauke fuska cin magani babu. Idanunsa cike suke da ƙaunarta. Yana ganin ta yi shiru zai ɗauki wani hirar.
Kallon da yake jifanta da shi, suke ƙara birkita tunaninta.
Wasu maxan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 42
Suna zaune har ƙarfe tara ta yi, tun tana share shi har ta saki tana dariya sosai, domin labarin dariya yake bata. Kallonsa take yi cikin tsananin ƙauna, ganin yadda yake so simple. Sosai take mamakin sa domin duk wannan ɗauke fuska cin magani babu. Idanunsa cike suke da ƙaunarta. Yana ganin ta yi shiru zai ɗauki wani hirar. Yawancin hirar little Marwana da Marwana rigamar da suke yi a gida ne. Sosai ta fahimci yana sonsu su biyun. Don haka ta sanya a ranta, za ta nuna musu ƙauna musamman little Marwana.
"Ki bani labarin abin da yaranki suke yi na dariya, musamman Musaddik na ga yafi wayo da rigima."
Da ya san farincikin da ta shiga, da game da tambayar da ya yi sanya ta to da ya ƙara wasu. Sosai ta washe bakinta ta fara bashi labarin ball da suke yi da Ya Ahmad. Dariya yake yi yana kallon ta. Hakan ya burgeta ganin ya ɗauki shirmensu, a matsayin abin da zai zauna yana saurare.
"Kids are very funny. Shi ya sa nake son yara sosai. Ina fatan za ki haɗa mini?"
Kunya sosai ta ji, jin abin da ya ce ganin hakan yasa ya yi murmushi. Sallama ya katse maganar da zai yi mata. Mommy ce da Marwana sai Muhsin.
Da sauri ta tashi ta tarbe su cikin jin kunya."Sannu da zuwa Mommy, ina kwana?" Ta ce bayan ta zauna.
"Lafiya kau ya mai jiki?"
Kasa amsawa ta yi ta zauna gefen Marwana.
Little Marwana ganin daddynta, sai ta ruga da sauri ta haye jikinsa."Daddy sorry, wannan mugun ya ji maka ciwo?" Ta yi masa tambayar tana kallon kansa.
"Na ji sauƙi ki daina kuka kin ci abinci?"
"Eh Anty Marwana ta bani."
"Ok, je ki gaida Ummanki."
Da sauri ta sauka, zuwa gurin Nasreen jin abin da ya ce. Cikin murmushi ta amsa gaisuwar.
"Nasreen ki sanya muku breakfast." Ta shi ta yi jin abin da Mommy ta ce ta zuba masa. Ita kuma ta sanya kaɗan ta koma ta zauna tana juya abincin. Hira suke yi cikin sanyin murya. Shiru ta yi tana saurarensu tana murmushi, don sai ta zamo ɓakuwa a cikinsu.
Suna zaune sai ga mutane sun fara shigowa, daga gurin aikinsu. Jaje sukayi musu, sannan suka yi musu murnar ɗaurin aure.
Hajar tun da ta shigo ga su Mommy da Muhsin, sai ta koma gefe ta zauna cikin kunya. Gurin Nasren ta zauna ta kama hannunta. "Mamaki sosai muka yi da aka ce an ɗaura aurenku. Na yi muku murna sosai Allah ya baku zama lafiya. Ingawa tamkar zai yi hauka, hawaye ya rinƙa yi lokacin da ya ji labarin, kin san tun da ya ɗauki jakarsa bai dawo ba."
"Allah Sarki Ubangiji ya bashi wacce ta fini." Ta furta hankali.
Mutane sosai suke ɗururuwar zuwa gaishe shi musamman ma'aikatansa.
Mommy ce ta kalle shi bayan sun fita."Ai baka samun hutun Damir, anya ba gida za mu koma ko a hana shigowa?"
Girgiza kansa ya yi don ba ya son a sallame shi, ta koma gida yafi son yi ta zama, har lokacin tarewarsu ya yi."A hana kowa shigowar dai, amma ina buƙatar hutu." Ya furta yana dafe kansa.
Murmushi suka yi domin sun ɗago shi.Muhsin ne ya shigo da magunguna a hannunsa.
"Ya Damir, likita ya ce sallamarka za a yi, ka koma gida sai ka dawo a kwance ciwon."
Jin abin da ya ce sa ya ji haushi. Shiru kawai ya yi, ba tare da ya ce musu komai ba. Nasreen kuwa daɗi ta ji sosai, domin ta matsu ta koma gida anan takura take yi.
"Likitan ma ya shigo sai mu fara haɗa kaya." Muhsin ya ce wanda ya sanya Marwana ta miƙe.
Suna shirin tafiya Ahmad da Baba suka shigo. Sosai ta ji daɗi za ta wuce gida. Haka kuwa aka yi bayan an gaida, sun gaisa mai jiki ta yi musu sallama. A tare suka shige mota sannan suka tafi. Damir sa ya ji babu daɗi a ransa har sai da suka fahimta. Gani yake kamar wata ɗaya shekara ne.
Da ta koma gida wanka ta yi, ta kwanta bata tashi ba, sai da kiran wayarsa ya tashe ta. Ba tare da ta gane wanda ya kira ba, ta kanga a kunninta cikin magagi ta yi sallama.
"Nasreen har bacci kika iya yi? Ni kuwa inata tunaninki." Ya yi mata tabbayar cikin mamaki.
Jin muryarsa, sai ta tashi ta zauna tana goge idanunta."Ya Damir, wata ɗaya ne fa za mu yi bamu a tare. Don Allah ka daure akwai shirye-shiryen da dole sai mun yi."
"Wata kamar shekara ne a gurina"
"Ka yi haƙuri zai zo."
"Ya zan yi tun da Mommy ta ce haka? Amma za ki dawo aiki ko? Kuma za ki zo gaishe ni?"
Dariya ta yi ganin rigimarsa kamar ƙaramin yaro."Zan iya zuwa ƙila, amma aiki sai bayan tarewarmu."
"No dole ki dawo aiki, saboda ta nan ne kawai zan rinƙa ganinki, in kuma ba so kike na tare a gidanku ba, don haka ki yi tunani."
Dariya kawai ta yi, ta sauka kan gadon ganin ya kashe wayarsa. Sallah ta yi ganin lokaci ya wuce, sannan ta fito falo. Zama ta yi gefen Ahmad da suke shawarar ranar da za a je maganar sa rana. Zainab ta ƙwalawa kira ta kawo mata abinci. Tare suka ci gaba da maganar.
Sam Damir bai barta ta huta ba kullum kira, yana gaya mata ƙosa ya yi missing ɗin ta. In ya dameta har mamaki take yi yada ya yi a lokacin da ya zauna babu aure. Gabakiɗaya ya zama mara kunya. Maganganu yake sakin mata har sai ta ji kunya ta kashe wayar. Wani lokacin irin rayuwar auren da yake so da kuma abin da yake son ta rinƙa masa yake gaya mata. Duk yadda ya so ta zo duba shi, ammma ta ƙi don kunyar Mommy take yi. Tun yana fushi har ya gaji ya saki. A ranar da ciwon ya yi sati aka warware masa bandeji.
Washegari ya shirya komawa ofis kuma ya matsa mata sai ta zo. Ta dai amsa masa ne don kawai ya barta ta kwana, saboda bacci take ji sosai, kuma ta san in har ba ta amsa ba ba zai kyale ta, ta kwanta ba. Washegari da ta tashi sai ta yi kwanciyarta, musamman da bata sallah.
Har ten ba ta fito ba tana bacci abinta. Wayarsa ya tashe ta ganin kiran ta yi murmushi ta ɗaga."Kin ce za ki zo ofis, amma tun takwas na zo ba ki zo ba?" Ya yi mata maganar ba tare da ya bari ta ce komai ba.
"Amma ka bari na amsa sallama." Ta ce mishi a maimakon ta amsa.
Shafa kansa ya yi kamar tana ganinsa."Am sorry ganinki kawai na ke son yi don Allah ki zo."
"Ya Damir, ni da aiki sai bayan tarewarmu."
"Ok, na yarda amma sai kin zo kin gaya mini ko?"
"Ga shi ina gaya maka kuma ai na gaya maka tun tuni."
"Ina kira ki a matsayin miji za ki ɗauke ni, amma maganar ofis a can za ki zo mu yi ta. Ina jiran ki." Ya ce tare da kashe wayar.
Dariya ta yi, ta shige bayi ta yi wanka tare da kintsa kanta ta koma gado, saboda hutu sosai take so ta yi.
Shiru-shiru ba ta zo ba, don haka ya ƙara kiranta."Nasreen mai ya sa ba za ki bi maganar mijinki ba?"
"Ya Dami..."
"Bana son wata magana in har ba za ki zo ba shikenan." Ya ce tare da daƙile wayar cikin fushi.
Miƙewa ya yi, yana zagaye ofis ɗin. Sosai yake jin ba zai iya jira har lokacin ba. Yana so ya shi kam ko babu biki a ba shi matarsa, amma ya san Mommy ba za ta yarda ba.
Wani feelings yake taso masa sosai har ya kasa jurewa. Sai ya rinƙa mamakin kansa yadda ya iya haƙuri ba tare da mace ba, amma kuma kuma gashi lokaci kaɗan ya kasa jira. Kodayake a lokacin ba shi da matata, amma yanzu yana ganinta ana masa ƙwalele.
Haka dai ya daure, domin tun yana sa ran zuwa har ya cire rai. Sai ya ji babu daɗi saboda takaici gida ya koma.
Da fari fushi ya yi da ita, amma sai ya ga fushin a banza ne. Don haka ya sha gayunsa ya tafi gidansu da dadddare.