← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 92

Sashe 9

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farouk kuwa tun yana tunanin za ta ƙara masa maganar wayar, sai ya ga kallon kirki baya samu daga gare ta, ta ci gaba da sabgarta. Hakan ya baƙanta masa rai, domin ya so ace ta nace ya samu abin duka. Ganin haka sai ya yanke shawarar ya rinƙa zuwa ɗakinta watarana ya kwana ya ga abin da take yi, take ba ta farinciki.

Da ya sanar wa Rashida zai kwana ba ƙaramin tsuya suka yi ba. Har sai da ya yi mata alkawari kallon banza ba zai hada su ba. Mamakinsa yake yi yadda take sa ya shi abu ba tare da yana so ba, musamman siyayyar da yake mata, amma sai ya ji dole sai ya yi.

A tujaninsa a buɗe take barin ɗakin don haka ya tura don ya mamaye ta, amma sai ya ji ta a kulle. Cikin ɓacin rai ya buga kofar da ƙarfi. Jin bugun ya tabbatar mata da shi ne. Da sauri ta kashe wayar Gabakiɗaya, ta buɗe ƙofar tana tunanin jarabar da ya kawo shi

Ɗakin ya bi da idanun, kamar baƙo ganin yana ƙoƙarin shiga ya sa ya ta ba shi hanya. Zama kan gadon ya yi, wanda hakan ya ba ta mamaki.

"Lafiya?" Ta ce masa tare da yin tsaye.

"Ki tambaye ni tun da uban wani ya gina gidan" Ya ce tare da ɓalla mata harara.

Jin abin da ya ce sai ta zauna kan stool taka kallon sa.

Ganin ba ta tanka masa ba ya ce,"Kwana na zo yi, ko akwai uban da ya isa ya hana ni kwana da matata?"

A maimakon ta amsa nushi ai ta saki dariya jin tambayar da ya yi mata. Gefen gadon ta kwana ba tare da ta ce masa komai ba.

Ganin sun yi shiru bacci na son ɗaukar ta ya sanya shi tashi ya zauna."Ke tashi ina son magana da ke."

Babu musu ta tashi ba tare da ta ce masa komai."Mai kike yi wanda yake sanya ki farinciki?"

"Mai ya sa ka tambaye ni kuma so kake na tabbata cikin damuwa?"

"Ya ina tambayarki kina mini?" Ya ce cikin fushi.

"To ai tambayar tana ba ta da amsa."

Jin abin da ta ce ya sanya shi matsawa kusa da ita."Wallahi zan yi matuƙar saɓa miki duk ranar da na ganki da wata wayar."

Ya daɗe a dakin komai ya gani, sai ya fasa kwana ya saki tsaki ya fice daga ɗakin. Yana fita ta shi ta rufe ƙofarta.

Rashida ta samu kan Faruk sosai take yin abin da take so a cikin gidan, domin har an kai mizanin da ta san pin ɗinsa. Shi kansa mamakin wani irin so da take mata, kamar zai kashe kansa. Gabakiɗaya ya juyawa 'yan'uwansa baya. Ko ita kanta Nasreen ta ga canji saboda watarana baya ba ta abincin da za ta ci. Ganin haka ta ƙara ƙaimi kan sana'arta, domin tana matuƙar rufa mata asiri.

Wata tsirfa da ta tsiro sai ta shiga kicin ta yi girki ta ɓata ta bar shi haka. Tun Nasreen tana haƙuri har ta kai maƙura. Ta ɗauki aniyar duk ta yi girki za ta gyara iya inda kayanta yake, ta bar mata na. Haka kuwa aka yi ranar da ta yi girki da gayya ta ɓata gurin. Da ta shigo ta ga yadda gurin ya yi datti. Ita inda kayan kicin ɗin ta, kawai yake ta gyara. Bayan ta gama dafa musu shinkafa da mai da ya ji ta koma dakinta. Suna zaune suna ci ta boko kofa tana huci.

Ba tare da ta kalle taba ta ci gaba da cin abincinta tana bawa Musaddik a baki."Uban wa kika bari ya gyara miki gurin?"

"Uban da ya yi girki ya bata gurin." Ta ce mata hankalinta kwance ba tare da ta kalle ta.

"Ke ni kike zagi?" Ta tambaye ta sai kawai ta ɗaure ta da mari.

Marin ya shige ta sosai ita ma bata ta sauke hannu ba, ta mayar mata da nata sai da ta ga wuta."Lallai yarinyar nan yau kin tsokano tsiliyar dodo." Ta ce tana gyara hannun rigarta.

Nasreen duk da ta ji tsoron don yadda ta fusata ta tabbatar yau sai buzunta, amma sai ba ta nuna mata ba."Jiki ya fi jiki ne?"Ta ce mata tana kallon ta.

Har Rashida ta ɗaya hannu za ta cakume ta, sai ta ji ƙarar hon ɗin Faruk. Da sauri ta fita tana kuka. Jin kukanta hankalinsa ya tashi sosai."Lafiya mai ya faru?" Ya ce mata lokacin da ya karaso gurinta yana kama hannunta.

"Wato Faruk ya na gaji da iskancin da yarinyar nan take mini. Ina haƙuri amma wallahi ba zan yarda ta ƙara marina ba?"

"Mari?" ya tambayeta ba tare da bata lokaci ba ya shiga ciki, yana zuwa ya ɗauke tada mari.

Tsananin mamaki ya kamata."Saboda zalunci ba za ka tambayi abin da ya faru ba sai ka mare ni?"

"Tsoron ki na ke yi da zan tambaye ki?"

Jin abin da ya ce sai ta lalle sa tana hawaye,"Allah ya sai ya saka mini, duk abin da ya faru yana gani shi zai yi mata alƙalanci."

"Ka ji makirar yarinya? Mai na yi miki kawai fa na yi girki, bana jin dadi na ce ta gyara gurin shi ne kawai ta hau zagina."

"Lallai Nasreen ba ki da kunya, kuma wallahi zan yi maganinki. Ma za ki je ki gyara gurin."

Wani banzan kallo ta watsa musu."Wallahi babu wanda ya isa ya sanya na gyara abin da ba ni na bata ba. Girkin da in an yi sai dai na ji ƙamshi ni da yarana, amma sai dai ku cinye ku barmu da abinci kamar a gidan bursuna."

"Shi yafi dacewa da ke, saboda na ga a gidanku ba kuma samun kamarsa."

"Shi kenan ka ci gaba da yin rashin dalci Allah yana ganinka."

"Wuce ki gyara gurin." Ya daka mata tsada yana faɗin haka.

"Wallahi babu wanda ya isa ya sa ya ni." Ta ce ba tare da ta ji tsoronsa ba

"Ok, dama tun da kika dawo ban taɓa lafiyarki, jikin ki ne yake miki ƙyaikyayi." Ya ce yana ƙoƙarin kwance bell.

"Ƙyaleta hubbina karka duke ta." Ta kama hannunsa tana faɗin haka.

"Da kin bar ni na taɓa lafiyarta."

"No ka ƙyaleta haushin rashin kulawar da ba ka yi mata ne ya sanya."

"Mai zan yi da ita bayan ina dake?"

"Ni ma na tsane ka na tsane ka Faruk, kullum ina rokon Allah ya raba ni da kai." Ta ce tare da shigewa bayi ta rufe ƙofa.

Tana jinsa yana suratansa ta yi banza da shi har sai da suka fita, sannan ta fito.

Tana jinsa da zai fita yana faɗin,"Ki tabbatar da kin gyara kicin ɗin nan."

"Sai na ga uban da ya isa ya sanya ni mugu azzalimi kawai." Ta ce tare da sanya wa ɗakinta makulli.

Saboda sa'insar da suka yi sai da ya kwana biyu bai bata komai ba, ba tare da ta damu ba ta dauki kuɗinta ta yi girki. Ganin yadda sana'ar yake rufa mata asiri, sai ta godewa Allah da Maman Muwaddat da ta ba ta wannan shawarar.

Jarrabawar su ta ƙarshe duke ƙoƙarin zanawa. Gabakiɗaya hankalinta yana kan karatu. Burunta sakamakon ta ya ci gaba da kyau har ta kammala. Cikin sa'a ta kammala karatunta. A ranar tasha kuka sosai har sai da muryarta ta rushe da ta tuno Ahmad, yadda ya sadaukar da rayuwarsa don ta samu ilmi. Kullum ba shi da burin ta kammala ta samu aiki. Ashe ba zai ga kammalawar ba. Marwana ita fa ta faɗo mata a rai, ta yi burin ta gama shekarar ta je masters a waje, sai ga shi a sanadin taimakon ta ita ta gama, amma ita ba ta a ƙasar. Ta yi kuka sosai. Ganin kuka ba shi da magani ta dawo gida cike da farin ciki.

Rigimar da suka fara da Faruk ya kafe ba za ta yi service. Da ya sanar da Baba jinsa kawai ta yi, amma a ra ta ta sanya duk abinda zai faru sai dai ya faru. Baƙincikin kuɗin da za ta samu yake yi.

Tana ganin kamar wasa bayan ta kammala karatun tana zaune ƙawarta ta kira ta kan ta je ta karbi takaddunta.

Da ta shirya har za ta fita ba tare da sanin sa ba, sai kuma ta fasa sanin abin da zai haifar.

Wayarta ta ɗauka ta lalubo lambarsa. Da sauri ya ɗauka ganin numbarta.

"Nasreen, gidan uban wa kika samu waya, ashe da na karɓe wancan wata kika siya?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai.

Gabakiɗaya ta manta ya karɓi layinta ganin ya kamata sai ta ce."Ba wayata bace aro na yi."

"Kar ki gaya mini maganar banza layin fa? Ai na karɓe shi yana gurina da wayar sai kika je kika yi welcome

Don Allah ayi mini haƙuri daga yau zan rinƙa posting page ɗaya, sai bayan sallah na ci gaba da biyu.🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏

*_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 6

"Nasreen, gidan uban wa kika samu waya, ashe da na karɓe wancan wata kika siya?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai.

Gabakiɗaya ta manta ya karɓi layinta, ganin ya kamata sai ta ce."Ba wayata bace aro na yi."

"Kar ki gaya mini maganar banza layin fa? Ai na karɓe shi yana gurina, da wayar sai kika je kika yi welcome back, saboda kin mai da ni mahaukaci ko?"

"Ni fa ba wannan ya sa na kira ka, saboda ba ni da katin da zan ji ƙorafin ka. Fita zan yi ina son na je makaranta, na haɗa takadduna saboda na samu ayi tura ni service da wuri."
Chapter 9 · 0% Book details