Sashe 37
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Akwai buƙatar ki yi updating kanki saboda guri ne da ya haɗa manyan mutane masu kuɗi da kuma masu class. Ya kamata gobe ki shirya mu shiga kasuwa, sannan ki ɗan samu abin da zai sanya ki ciko ki ƙara kyau. Bana son wani ya yi miki kallon up and down a gurin."
Bakinta ta kama cikin mamakin abin da ta ce."Aiki zan je ki nema mini ko mijin za ki ce sai na yi wani updating kaina? Ni da na ke tunanin na rinƙa saka niƙabi."
Banzan kallo ta watsa mata."Amma tsokanata kike yi ko? Gyale za ki rinƙa sanyawa da abayoyi, kin san inda za ki fara aiki?"
"A,a ban sani ba sai na je."
"Zamu je amma kafin nan sai kin gama shiryawa."
"Allah ya kaimu." Ta ce tana ganin abin kamar a mafarki. Har ta yi mata sallama ta tafi suna zaune suna ta maganar aikin.
"Ni fa gani na ke kamar bada gaske ba! Wai ni ta sanar wa aiki kuma da albashi mai tsoka?"
"Kina mamaki ne da lamarin Ubangiji? Ko shigowarta cikin rayuwarki ya ishi ya sanya ki gane Allah yana taimakon bayinsa a duk lokacin da ya so."
"Haka ne Mama, Allah ya sa na fara aikin na ɗauke duk wani ɗawainiya ta ƙi."
"Amin, a hakan ma kina ƙoƙarin ki sana'ar da kike yi."
Kwana suka yi suna maganar aikin har sai da suka gani suka kwanta.
Marwana da ta koma gida, zama ta yi ta gama list ɗin abubuwan da za ta siya mata, dangin su abaya takalmi hijabai da kuma kayan kwalliya.
Suna zaune a falo ta fito da jakarta. Ganinta suka ɗauke kai ba tare da sun ƙara kallonta ba. Murmushi ta yi ta ƙarasa gurinsu. Fuskarta a ɗauke ta mika wa Muhsin credentials ɗin Nasreen.
"Na gani sai ki gaya mata ta zo interview, kin san dai ba haka za mu bata aiki ba bamu gwadata ba?"
"Kan me sai kun yi mata interview Nasreen tana da ƙoƙari. She is very talented."
"Kampanin na mahaukata bane ai. Idan kuma son a bata aiki dole ayi mata interview, matuƙar ta kasa ba za mu ɗauke ta ba, saboda competent muke ɗauka."
Kallonsu ta yi na rashin yadda, a tunaninta so suke su yi mata ta yadda za su kayar da ita.
"Ni fa ban yarda ba."
"To sai na ga uban da zai bata aikin." Cewar Muhsin yana harararta tare da ture takaddunta.
Ɓata fuska ta yi daidai lokacin da Mommy ta fito."Mommy wai dole sai sun yi mata interview?"
Kallonsu ta yi da suka mayar da hankalinsu kan wayoyinsu."Damir.."
"Don Allah Mommy, yarinyar nan ba ta da hankali. Kin taɓa ganin inda aka ɗauki mutum aiki ba tare da an gwada shi ba? Kamar haka na ke son a yi mata, saboda mu ba mahaukata bane kamarta."
"Na matsala in har za a yi tsakani da Allah, za ta ci ai tana da kwanya first class ce."
"Allah ya sa kar ta ba ki kunya wa ya sani sata take yi?" Cewar Muhsin tare da miƙewa.
"Allah ya kyauta sam ba ta sata."
"Ba abin mamaki bane sanin halin mata da malpractise." Ya ƙarashe maganar yana ƙoƙarin hawa sama.
Harara ta banka masa ta mayar da hankalinta kan Damir do ko kallon inda take bai yi ba, sai na ya miƙe zuwa waje.
Raka shi da idanun ta yi, har ya fice sannan ta mayar da hankalinta kan takaddun Nasreen.
Da ta shiga ɗaki zama ta yi ta kira ta."Zan zo gidanku don Allah ki shirya dole sai an yi miki interview."
"Babu matsala Allah ya kaimu." Ta ce mata. Hira kaɗan suka yi sannan ta kashe.
Sai da ta je kasuwan ta yi mata siyayya, da yawa sannan ta tafi gidansu."
A lokacin da ta iso Nasreen ta gama shiryawa. Ganinta da kaya niƙi-niƙi sai ta tsaya tana kallonta.
"Babu time ki shiga ki canza kaya muje."
Kallo ta bita da shi ta kasa karɓar kayan." Ba kyauta na kawo miki ba da zarar kin fara salary za ki biya ni."
"In sha Allah salary farko na ki ne."
"Je ki shirya Nasreen." Ta ce mata tare da tura mata kayan.
Ciki ta shiga ta samu wata abaya mai kyau sosai. Kalarta marun mai an yi mata ado da duwatsu da aka yi mata. Da ta fito kallonta ta yi domin ta yi kyau. Ramar da yake jikinta ya ke rage kyawunta.
"Kin yi kyau mu je." Ta ce tare da yi wa Mama sallama.
A hanya suna tafe suna hira. Hirar ta su kan aikin ne. Marwana take ta gaya mata ta kula da aikin da zuwa kan lokaci."Dole ki kula kin san aikin campany ba kamar na gwammati ba, saboda suka sanya idanu sosai, don suka ana yi musu aikin kuɗin da suke biyanka."
"Zan kiyayye in sha Allahu, ina son na yi aikin don na ɗauki hidimar Mama."
"Za ki yi abin da ya fi haka saboda suna biya da tsoka, amma fa shugaban kampanin yana da tsaurin ra'ayi."
"Zan kiyaye tsakanina da shi gaisuwa, sai kuma in ya bani umurni na yi."
"Da kyau na san ba zan samu matsala da ke ba." Ta ce daidai lokacin da suka kawo kampanin.
Cikin tsananin razana ta kalle ta tana faɗin,"Kina nufin a wannan tanƙamemen companin kika samar mini aiki?"
"Eh, shi ya sa na ke ta gaya miki da ki kula."
Jinjina kanta ta yi tana kallon gurin, cikin mamakin girmansa da kyawunsa.
"Please Nasreen, kin ga yanzu Mommy ta yi mini text na dawo gida ba ta jin daɗi ba zan samu shiga ba, don Allah ki shiga ciki akwai da na gaya mata za ki zo. Ga numbarta ki kira ta in kin gama sai ki koma gida."
"Ok, ba matsala Allah ya ƙara sauƙi." Ta ce tana ƙoƙarin ciro wayarta ta kwafe numbar.
"Buɗe data na tura miki ta Whatsapp." Ta ce mata bayan ta mayar da wayarta cikin jaka.
"Bari na shiga to." Tare da fara tafiya.
Marwana kallo ta bita da shi sai kuma ta ce,"Fatan nasara don Allah ki natsu kar ki ji tsoro, ki amsa duk tambayar da aka yi miki na san za ki iya."
"In sha Allahu, I won't disappointed you."
" I know da zarar kin gama give me a call."
"In sha Allahu." Ta ce sannan ta tayar da motarta.
Sai da ta nace sannan ta shiga ciki.
Marwana kuwa ta yi hakan ne don kar ta ga yadda ake girmamawa, ta gane cewar kamafaninsu ne.
Kiran wacce ta ba ta numbarta ta yi ganin ta kasa gane ko ina. Kasancewar kampanin saman ginin gilad ne aka ƙawata da shi.
Ba ta jima da kiranta ba sai ga ta ta fito. Tana sanye da abaya baƙa. Tana da kyanta tana da kiɓa daidai, sannan za ta iya girma ta ko su zo tsara.
"Nasreen ko?" Ta tambaye ta hakan tana mutmushi
"Eh, ni ce." Ta amsa bayan ta gaishe ta.
"Ok, mu shiga ciki." Ta ce tare da juyawa.
Babu musu ta bi bayanta, tana ta kallon gurin da mamakin a nan za ta yi aiki.
Da suka tsaya ofishin Muhsin kallonta ta yi sai kuma ta kallo masinjarsa."Ki shiga da ita Please."
"Ok," Ta ce tare da mata nuni da alamun ta biyo ta.
Da sallama ta shiga cikin ofishin tana kallon cikinsa. Wani irin ƙamshi mai daɗi ya bugu hancinta.
Muhsin yana zaune yana duba fayal. Jin sallamar ya ɗaga idanunsa yana kallonta. Tun da suka iso Marwan ta yi masa text tare da mishi kashidin karya kk pmayar da ita. Murmushi kawai ta yi yana mamakin yadda akai suka yi sake ta raina su.
Kallonta ya ƙara yi tare da yi mata izinin ya zauna. A hankali ta zauna tana kallonsa. Natsuwarta da hankalinta, da yadda take kama kanta suka sanya shi kasa mata wulaƙanci.
Yana shirin fara mata interview biyu sai aka buɗe ƙofa. Damir ne ya shigo hannunsa da ƙaramin tawul da ya gana wanke hannunsa yana gogewa.
"Please, Muhsin na manta ban gaya maka ba, baƙin nan they are on their way kuma zan fita na kai Marwana gidan su Batul..."
Da sauri ta ɗago idanunta zuciyarta na wani irin bugawa. Saboda tsananin razanar da ta yi sai da ta ji kamar ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba. Karab idanunsu ya haɗu da na juna.
" Ya Damir." Ta furta cikin ranta tana mamakin ganinsa.
Shi ma kallonta ɗago ya yi, ya gane ta tun ranar da ya ganta ya kasa manta kamanninta, saboda tabon da ta yi masa a zuciya. Wani irin tafasa zuciyarta ta yi har baya iya hangen abin da ke gabansa. Ganinta ya dawo masa da mikin rashin Batula da ya yi. Ganin ta ya sanya shi tuna rana ɗaya wace ta tarwatsa rayuwarsa. Rana ɗaya da ya haɗu da ita ta zame masa baƙar rana. Ta sanya masa mikin da ya ke tashin masa kuma ya kasa mantawa. Rana ɗaya da ya yi nufin mata alkhairi, ana sai ta zame masa tauraruwa mai wusutsiya, ta hanyar sanadin mutuwar matarsa wacce yafi so fiye da komai
Nasreen kuwa wani irin juya ya fara ibanta. Da kyar ta iya dafa bango jikinta na ɓari ta fara neman hanyar fita.
Ganin tana shirin fita Muhsin ya buɗe baki zai kira ta."Ƙyaleta ta tafi ita kanta ta san bata cancanci ta yi aiki anan ba, saboda in har ba mahaukaciyar kamar Marwana, za ta fahimci ya kamata ta ci gaba da ɓoye kanta, daga idanuwana har ƙarshen rayuwarta."
Kuka ta fashe dashi ganin yadfa tsantsar tsanarta yake idanunsa."Eh, tabbas ba ka yi ƙarya ba Ya Damir. Haka ya kamata na yi ta gujewa haɗuwarmu, in har na san mai na ke yi. Kaicona da na bari muka ƙara haɗuwa bayan ka nemi alfarmar na yi nesa da kai." Ta karashe maganar cikin kuka tare da ficewa da gudu.
Ajiyar zuciya ya fara saki akai-akai yana jin zuciyarsa na zafi, yayin da komai ya dawo masa sabo. Ga mamakinsa sai hawaye suka zuba masa.
"Please Ya Damir, be a man." Ya ce masa ganin yadda ya rikice.