Sashe 43
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ya fita daga ofishin cikin damuwa jin ƙayyadadden lokacin da ya ba su. Mamakin abin da ya tunzura zuciyarsa lokaci guda yake. Ya san lafiya suka rabu a gida har yana gaya masa ya tsaya ya gama abin da yake yi."To mai ya faru ya yi sa kansa tambayar cikin rashin amsa."
A lokacin da ya da sanar da taron mamaki ya kama su, amma saboda lokacin da ya bayar dai suka fara tashi da sauri suna tunanin dalilin taron."
Nasreen tana zaune tana waya tsaƙon ya riƙe ta. Da sauri ta miƙe tana zare idanunta."Innalillahi! Na shiga uku meeting yanzu har da ni?" Ta yi wa Khausar tamabayar tana zare idanu.
"Ok, tambaya kike yi? Ki ga na tafi ga Hajar can ta kusa shiga."
Jin haka ya sa ta ja kujerar da take zaune ta bi bayanta.
A hankali take taku har ta isa cikin dakin taron. Ba tare da ta ɗaga idanunta ta kalli kowa ba ta nemi guri ta zauna. Zuciyarta bugu take yi haka kawai ta tsargu game da taron da ya haɗa.
"Innalillahi! Kun ga yadda yake fushi yana nishi kamar mesa? Allah ya da ba haɗiye mu zai yi ba." Hajar ta furta cikin raɗa tana kallonsa.
Jin abin da ta ce sai ta ɗaga idanunta tana kallonsa. Da sauri ta mayar da idanunta kasa tana fatan kar ta ƙara kallonsa.
Ɗakin taron ya yi shiru ba ka jin komai sai ƙarar A.C da bugun zuciyoyinsu suna tunanin abin da zai ce.
Cikin fusata ya buɗe baki ya fara magana ba tare da ya kalle su ba."Saboda na sakin muku da yawa, har kina da lokacin da za ku zo kuna tsayawa hira? To daga yau na kafa dokar zuwa gurin aiki kafin na zo, kuma ba zan gaya muku lokacin da zan zo ba, duk wanda ya sake na riga shi zuwa ya kori kansa, don ba kuɗin banza na ke samu hada har na ke biyanku kuna zuwa lokacin da kuka ga dama har ku tsaya hira ba, sannan waɗanda ba su ba, in suka zo ku gaya musu na ba su hutun wata ɗaya, kuma babu albashi."
Maganar da ya yi ya bawa kowa mamaki. Dakin taro sai ya fara surutu ƙasa-ƙasa, kowa na mamakin dokar da ya saki. Kallonsu da ya yi yasa suka yi shiru.
Ta shi ya yi ya fice ba tare da ya samu da yadda suke kallonsa ba. Muhsin ya mike da sauri ya bi bayansa yana mamakin dokar da ya sanya, da kuma tunanin abin da ya sanya shi dokar.
Nasreen tun da ya fara magana, ta kasa daga idanunta ta kalle shi har ya gana ya fice. Mamaki take yi saboda ko ita kanta dokar ta yi mata tsauri. Idan ta tashi tana samu ta yi sallah da asuba, sannan ta yi karatun Alkur'ani, bayan ta yi azkar ta shirya Raihann har ta haɗa musu abin kari. In har ya sanya wannan dokar ta yaya za ta yi ga shi tana tunanin sanya Musaddik a makaranta? Kuma ta yaya zai kafa dokar tun da ba shi da takaimainan lokacin zuwansa?" Irin tambayoyin da take yi haka sauran ma'aikatan suke yi.
Ganin surutun ba mafita bane, sai suka tashi kowa ya nufi gurin aikinsa.
Da ya shiga cikin ofis yana zaune P.A dinsa ta shigo."Sir, ga shi na gama singing ɗin, zan kai wa Hajar da Khausar su ƙarasa aiki." Ta furta cikin sanyi da girmama.
"Ok, shi kenan files ɗin?"
"No akwai wasu zan ƙaro."
Good ya ce yana murmushin mugunta."Ki haɗa su duka ki kawai wannan sabuwar ma'aikaciyar wacce take kusa da ofis ɗin S. Ɓako. Ki gaya mata kafin awa uku ta gama aik.."
Zare idanunta ta yi tana kallon sa."Awa uku sir? Ko ni sai da na yi kwana uku ina yi, sannan aikin ba nata bane na..."
"Will you shut up!" Ya daka mata tsawa tare da miƙewa.
"An sorry sir." Ta ce tare da fara ƙwasan files din za ta fita. Tsaki ya yi, ya koma ya zauna ba tare da ya ce mata komai ba ya ɗauki wayarsa.
Cikin mamakinta isa ofishin na ta tana tunanin uban aikin da ya ba ta. Da sallama ta shiga. Amsawa ta yi tana kallonta
"Ga shi in ji oga Damir, ya ce na kawo miki za ki kawo nan da awa uku."
Zare idanunta ta yi bayan xuciyarta ta buga jin abin da tace, sai kuma mamaki ya kamata ganin uban akin."Sister Salima wannan aikin a cikin awa uku? " Ta tambaye ta fuskar ta da mamaki.
"Am sorry that was what he said."
"Ok," Kawai ta ce tare da fara duba takaddun cikin mamaki.
"Have a nice day." Ta ce mata sannann ta fice daga ciki.
Jaɓar ta zauna tana share zufa. A ranta ta san kawai so yake ya wulaƙanta ta, amma in har ba ijin bace ita ba zata iya gama aikin ba. Idanunta suka kawo ruwa sai ta yarda da zargin da xuciyarta take yi kan meeting da ya haɗa.
Fara aikin ta yi cikin ɗaurewar gwiwa saboda ta san duk takura kanta ba za ta iya gamawa ba. Tana cikin aikin ta yi nisa hankalinta yana kai. Ingawa ya yi sallama tare da murɗa ƙofar ya shigo.
Ganin yadda hankalinta ya ɗauki ya ƙaraso."Ƙanwata haka kika yi busy?" Ya ce mata tare da ɗaukar files ɗin yana dubawa.
"Eh wallahi tun safe?"
"Waya kawo miki wannan aiki saboda na su Hajar ce?"
Kallon sa ta yi ta ce,"Oga Damir ne ya ba P.A ta kawo mini."
"Shi da kan shi? Na yi mamaki saboda ba aiki ki bane."
"Wallahi kuwa kuma awa ɗaya da rabi na kai masa, saboda ya ce awa uku ya bani."
Dariya ya saki yana kallonta."Wasa yake miki wataƙila, domin ko shi kansa a wuni ba zai iya gamawa ba ballantana ke."
"He is serious ba ya wasa da ni." Ta furta cikin gajiya.
Ganin yadda fuskarta ya yi na don ta gama aikin sai ya yarda."I don't know why he is so strict kwana biyu. Ki na jin nonsense dokar da ya kafa?"
Ajiyar zuciya ta yi kawai ba tare da ta ce komai ba."Nasreen, komai za ki yi ba fa za ki iya ba, just do you best ki je gobe ki ƙarasa."
"Ya zan yi? Ta ce da gaske yake so."
"You are not a robot, amma bari na taimaka miki." Ya faɗa tare da zaunawa kusa da ita ya ɗauki files ɗin
"Ka bar shi kai ma kana da aiki."
"Kar ki damu sister." Ya ce.
"Na gode." Ta furta tana kallon sa ganin yadda yake kallonta.
Ƙasa da kanta ta yi suka fara aiki. Yana mata hira sai dai ta amsa da um a'a, ko ta yi murmushi. Gabakiɗaya hankalinta a kan aiki. Hirar ya ci gaba da yi mata, bature da ya kula da jan ajin da take ma ba, domin so yake ya sanya shaƙuwa da soyayya yadd za ta aminta da shi.
Damir yana zaune a ofis ɗinsa, tun lokacin har yanzu zuciyarsa tafasa take yi. Ba ya son a taya ta aikin so yake ta kasa ya yi mata tijara. Da sauri ya miƙe zai je ya gani, amma sai ya fasa yan jin girman kan ya je ofis ɗin ta. Da sauri ya kunna C.T Camera don ya gani.
Zuciyarsa be ta buga ɓacin ransa ya nunku ganin su zaune suna aiki. Kaima tv ɗin duka zai yi, amma sai ya fasa ya fice daga ofis ɗin kamar kububuwa. Duk wanda ya hadu da shi ya gaishe shi. Kallon banza ba ya samu. Wasu daga cikin ma'aikatan suka tsaya gulmar, ganin inda za shi cikin fushi kamar fusataccen zakin da ya yi kwanaki a dawa babu abinci.
Da karfi ya buga ƙofar har sai da ta miƙe saboda razana.
"Are You stupid! Na ba ki aiki kin kira wani ya yi miki, ko ke kike biyansa da za ki hana shi na ki aikin ya yi na ki?" Ya yi mata tambayar tare da zare mata idanu.
Jikinta ya kama rawa sai ta ɗago idanunta tana kallonsa hawaye fall a idanunta.
Ta buɗe baki za ta yi magana ya daka mata tsawa, sai ta yi shiru hawaye yana zuba a ƙuncinta.
"Ba ita ta kira ni ba, kuma ba ni..."
"Please get out, kuma daga ya bana son a rinƙa taya co-workers aiki. Kasan ina ganin mutuncinka da wani ne sai na embarrassing ɗinsa."
"Ok sir." Ya ce tare da juyawa ya fice bayan ya kalle ta.
"Ma za ki gama a lokacin da na baki." Ya juya ya fice yana huci.
Kuka ta saki tana jin ba za ta iya jure wulaƙanci ba. Duk yadda ta so ta gama aikin kafin a tashi kuma daidai lokacin da ya ba ta hakan yaci tura. Ganin lokacin ya yi tattara zuciyarta na bugu ta kai wa P.A ɗinsa.
"Don Allah ki ba shi haƙuri wallahi ban ga..."
"An sorry that I can help ya ce ke za ki kai masa."
Da sauri ta ɗago idanuta kamar za ta yi hauka." Ba zan iya ba.."
"Zuwa ya zamar miki dole gaifis ɗin." Ta nuna mata tare da wucewa bayan ta daga kafaɗunta.
Jikinta ya na rawa ta rasa yadda za ta yi. Har ta juya dai kuma ta tsaya ta zare ido, cikin rashin dubara ganin saura minti uku lokacin ya cika.
A hankali ta tura ƙofar bakinta ɗauke da sallama. Yana zaune da Little Marwana da take kwance a jikinsa bacci yana son kamata. Ganinta ya sha kunu ya canza daga dariyar da yake mata, yana shafa bayanta don har waƙa yake yi mata don ta yi bacci.
"Um..eh. ga.." Ta kasa magana xuciyarta na bugawa, amma ganin ya mike a xafafe sai ta daure ta ce,"Ka yi hakuri saura kaɗan..."
"Kin san Allah sai kin gama za ki tashi. Ke da masu gadi za ku rage."
Zare idaunta ta yi dai hawaye da gudu ta fice da sauran aiki. Tsayawa ta yi a bakin ofis ɗin ta goge hawayen gudun kar wani ya gani.