Sashe 56
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Saboda ba ni daraja da ƙima ina mijinki za ki bar ni a cikin talauci ki dawo gidan da ɗana ya gina miki?" Ya yi wa mata tambayar cikin takaici yana kallon gidan.
Ahmad ne ya fito daga cikin gidan jin muryarsa."Baba sakin Mama za ka yi domin sam bata dace da kai ba."
Jin abin da ya ce sai ya kalle shi cikin fushi."Kai Amadu ka kiyaye ni kar nayi masa baki, saboda ko yi arziki sai ka sanya na rabu da matata, kar ka manta duk arzikin da ka yi nine ubanka."
"Na sani amma dole yau ka sake ta. Kullum ranar duniya sai na yi dana sanin fitowa daga tsatsonka, domin ka haife mu ka kasa bamu kyakkyawa kulawa da za mu tashi cikin tarbiyya. Haihuwarmu kawai ka sani, amma ba ka san cinmu da shan mu ba. Na yi kuka sosai da ka kasance mahaifina, kullum fatanta Ubangiji ya bani abin da zan siya mana gida mu bar rayuwar ka ta dabbo..."
"Kul! Ahmad karka ƙarashe." Mama ta ce masa ganin yadda ya fusata.
"Ki bari kawai Mama na gaya masa Allah kaɗai ya san kuma da na yi saboda dana sanin kasancewarsa mahaifina. Ya cutar da mu ya sanya wasu daga cikin 'yan'uwanmu cikin wulaƙantacciyar rayuwa. Ya yi sanadin da wasu yan uwansu suka zama faɗɗararru." Ya ƙarashe maganar yana hawaye.
"Ka yi haƙuri don zai sake ni, saboda ni kaina rayuwa nake yi cike da dana sanin kasancewarsa mijina."
Baba sai ya shiga cikin tashin hankali ganin ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Ga arziki amma za su yi masa bore."Wallahi ko kashe ni za ku yi ba zan sake taba, kuma aurena da mahaifinyarki mutu ka raba.... In har kana tunanin zan iya aminta gara ka daina, duk arzikin da ka samu da ni za a ci."
Hannun Ahmad ta kama ta kalli Baba ta ce,"In har ni ce zan ci gaba da auren da kai na haƙura da kai, don haka ka faɗi sadakinka yanzu zan biya ka."
Hankalinsa ya tashi ganin da gaske yake yi."Na gaya muku ko wuƙa za ku sanya mini a maƙoshi ba zan sake ki ba."
"Ni kuma ba za ka zauna mini a gida ba " Ahmad ya ce tare da jan hannun Mama suka shiga.
Kafin su shiga har ya riga su shiga ya zauna a falo yana raba idanu.
Babu wanda ya kula shi, haka ya gama surutunsa ya shige cikin ɗakin Mama.
Bayan Ahmad ya gama hutun gajiya, ya shigo falon Nasreen na zaune a falo da wayarta.
Gefenta ya zauna tare da kama hannun Musaddik yana mishi wasa." Barka da shigowa yayana." Ta furta tana kallon sa.
"Yauwa ya hanunn na ki? Na ga raunin ƙafarki ya yi sauƙi."
"Eh sosai har na daina ɗingishi."
"Allah ya ƙara sauƙi tun da kin samu sauki ki shirya zamu je boutique ku siyo kaya, sai ki zubarwa Mama muje da yaran."
Murmushi ta yi jin abin da ya ce."Allah ya ƙara buɗi Yaya."
"Amin." Ya furta tare da miƙewa.
"Bari na shiga ciki na gaida Mama."
"To Yaya." Ta ce tare da mayar da hankali ta kan wayarta.
Har ya fara taku sai kuma ya tsaya ya ce,"Ki gaya wa Marwana ta shirya sai mu je tare ita, ma ta zaɓa abin da take so sannan ta taya ki zaɓar kaya, saboda so na ke ki suyi kaya masu tsadar gaske."
"To Yaya Ubangiji ya ƙara buɗi."
Numbar ta ta kira ta sanar mata tare da miƙewa don ta fara shirya yaran.
Marwana ba ta ɗauki lokaci ba ta zo. A motar Ahmad suka shirya tafiyar don haka ta shigo da na ta motar cikin gidan. Tun da ta shigo kaya yake kasa. Gabakiɗaya daya ta kasa sakin jikinta, har sai da Nasreen ta fahimta. Wani irin kunyar Mama take ji sosai.
Ahmad kawai suke jira daya shiga wanka. Bayan ya fito ya shirya cikin yan kaya kuma ya yi kyau sosai. A gogonsa yake ɗaurawa Nasreen ta yi sallama ta shigo.
"Mun shirya Yaya Marwana ma tun ɗazu ta zo."
Jin ta ambaci sunanta sai ya ji gabansa ya faɗi."Ok ina zuwa."
"Wow! Ka ga yadda ka yi kyau?" Ta ce masa tare da kama ƙofar za ta fita.
"Ko ƙanwata? Kema kin yi kyau sosai na yi mamakin yadda kika canza."
"Aikin Marwana ce ita take kula da ni sosai."
"Marwana yar aljanna ce babu wacce ta kai ta a gurina, saboda ta kula da ahalina."
Daga masa kanta ta yi sannan suka fito tare.
Ganin sun fito sai Marwana ta miƙe cikin jin kunya ta ce,"Ina wuni Ya Ahmad."
Kallonta ya yi na dan daƙiƙa."Kina lafiya ya Mommy."
Kasa amsa tambayar ta yi ganin yadda ya yi kyau kuma ya yi mata ƙwarjini. A gidan baya suka shiga sai suka sanya yaran a gaba. Tun da suka shiga motar Ahmad da Marwana sun kasa magana, sai Nasreen take ta zuba sai dai su amsa da um ko a'a. Ganin haka ta ja bakin ta ta yi shiru tana kallon titi.
Marwana kuwa kasa sakewa ta yi, saboda duk ta kalli madubi sai sun haɗa ido da Ahmad. Wani iri take ji game da shi har ta kasa jurewa.
Da suka isa cikin boutique ɗin. ATM ɗinsa ya miƙa musu."Marwana ku sayi duk abin da kuke so, sannan ki zaɓawa Nasreen kayan da kika san za ta zama babbar mace mai aji."
Murmushi ta yi cikin jin kunya ta karɓa."Ya Ahmad kana son Nasreen sosai."
"Ya zama dole na kula da ita. Ku je ku zaɓa bari na duba abin da na ke so."
Godiya suka yi masa sannan duk wuce don su fara siyayyar. Kamar yadda ya ce kaya sosai na manyan mata ta siyawa Nasreen. Ganin tun da suka shiga kayan take zaɓa mata sai takama hannunta."Please ki zuwa kanki kayan sun isa, kar ki manta da zan fara aiki kin siya mini wasu."
"Akwai buƙatar ki yi updating kanki Nasreen,musamman yanzu da kika yi babban catch up. Abokin Yaya Damir ya ganki yana so. Na share batun ya Damir yanzu campain ɗin Ya Annur na ke miki. Yana da kyau sannan akwai ya'yan banki, kuma yana da ilmi sosai injiniya ne shi, shi yake yi wa kampaninmu zane."
Mamakin abin da take faɗi ta yi, sai kawai ta yi dariya ta ci gaba da duba kayan."In har kika kula shi ba za ki yi nadama ba, saboda gayen ya haɗu ta ko ina."
Ba tare da ta ce mata komai ba ta cigaba da duba kayan."Kin ga wannan zai yi miki kyau, bari na fara zabar miki tun da kin kasa." Nasreen ta ce tana nuna mata doguwar riga.
Siyayya sosai suka yi har sai da suka gaji. Ko da suka gama suka kai masa ATM ɗinsa kallonsu ya yi."Saura bags and shoes ki zabar mata dayawa, waɗannan sun yi kaɗan."
Jin abin da ya ce yana miƙawa Marwana katin sai ta kama hannunsa."Wallahi sun yi ina zan kai kaya?"
"Je ki zaɓar mata so nake duk inda ta wuce sai an kalle ta." Ta kasa magana kawai kallonsu take yi da hawaye.
Sai da yamma sosai suka dawo, sannan Marwana ta yi musu sallama ta tafi. Kallon kayan Mama ta yi sai alkbarka take sanya mishi. Nasreen ba ta ƙara yarda ta zama yar gatan Yaya Ahmad ba, sai da ya shigo da makullin mota. Miƙa mata ya yi ta karɓa tana zare idanu.
"Mota na siya miki Nasreen tun da kina aiki kina buƙatar mota ga kuma dauko yara."
Zare idanu ta yi, tana kallon sa cikin tsanannin murna da mamaki. Sunan Mama ta kira da karfi sai ta rungume shi tana hawaye."Ikon Allah ashe ni ma zan tuƙa mota? Mota Yaya Ahmad ya siya mini."
Mama cikin murna ta ce,"Masha Allah rayuwa ta canza Allah ya yi albarka."
"Amin can gidan ma na sanya za a zo a rushe a gyara musu."
"Da kyau Ubangiji ya ƙara buɗi."
Jin hayaniya Baba ya fito daga ɗakin Mama, tun da ya zo gidan da ƙyar ranar kwanarsa yake tafiya, duk da cewar kallon arziki baya samu a gurin ta.
"Amadu yanzu kana da kuɗi amma ba ni da maraba da almajirin gidan nan. Kowa ka canza masa kaya, amma ni ina yawo cikin tsumma?"
"Haka ya kamata ka yi rayuwa saboda sam bana tausayinka, ko gidan nan da kake zama ina jiran na gama abin da ake yi sai ka saki Mama bisa dole."
"Wallahi ba zan saki matata ba in har mafarki kake ka farka."
"Banza ya yi da shi ya miƙe cikin jin hushinsa ya fice. Sam a zuciyarsa baya jin tausayinsa.
Kallon Mama ya yi yana
Ayi haƙuri da wannan 🙏🙏🙏🙏
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 30

Kallon Mama ya yi yana faɗin,"Kina ganin har mota ya siya wa Nasreen, amma ni ubansa ko wayar kirki bai siya mini ba?"
"Mai zan ce masa? Alokacin da na ke gaya maka, irin wanna rana kar yazo ai ba kasaurare ni ba. Haka ka haife su kara zube suna yawo kaman awakai a gari, ba tare da kula kula da rayuwarsu ba, sai yanzu ya samu ya inganta kansa nayi masa dole? Sam ba zan takura masa ba domin haka ya kamata ga azzalumai iyaye irinku, waɗanda suke yin aure don biyan buƙatarsu ba wai don su haihu, ranar gobe ƙiyama Ubangiji ya yi alfahari da su ba."