← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 92

Sashe 62

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajar da S.Baƙo kawai suka fahimci safa da marwar da yake yi, tamkar mi ɗawafi, domin ko da ya shiga ya ije jakarsa, sai ya tsinci kansa da kasa zama ya fito. So yake ya ganta musamman shigar da ta yi ya burge shi. Tana sanye cikin hijabi jalbab kalar maroon color, sosai ya karɓe ta. Ƙananan kaya ta sanya, don haka ta saka hijabin har ƙasa.

"Wai ko oga Damir ya yarda wani abu ne na taya shi nema? Tun ɗazu yake sintiri ya wuce yafi sau biyar."

Jin tamabayar da Hajar ta yi, tana kallon S. Bako sai ta ɗago ta kalle shi. Da sauri ta ɗauke kanta ta mayar gurin S. Bako xuciyarta ya buga da sauri.

Yana sanye cikin suit kayan sun karɓe shi. Idanuwana sanye cikin gilashi da wayarsa riƙe a hannunsa.

"Ya Damir ka yarda wani abu ne?" Hajar ta tambaye shi daidai lokacin da ya zo zai wuce su.

Ɗago kansa ya yi, ya kalle ta sai kuma ya watsa wa Nasreen kallo, wacce gabakiɗaya hankalinsa ba shi a kansa."No." Kawai ya ce tare da sakin ajiyar zuciya ya shige ofis ɗinsa.

Ganin kallon da ya watsa mata, sai suka kalle ta wacce ba ta san abin da yake faruwa ba. Murmushi suka saki sannan S. Baƙo ya cigaba da musu bayani.

Damir zama ya yi cikin ofis ɗin, yana saukar da numfashi da sauri. Idanunsa sun canza sun yi ja. Shi kaɗai ya san yanayin da yake ji in ya ganta. Yana saukar da numfashi a hankali ya kwantar da kansa.

Haka ya ci gabas ɗawainiya da sonta, amma tsabar girman kansa da izza ya kasa gane ya fahimci haka. Kullum sai da ya yi ta fama da damuwa, wanda har ta kai shi bp dinsa ya hau sosai.

Tsakanin Marwana da Ahmad kuwa lamarin ya ci gaba, domin soyayyar su sai ci gaba take yi. Wani irin ƙauna suke yi wa junansu, amma ba tare da sun yarda kowa ya sani ba. Nasreen ce ta fara zargin Ahmad ganin yadda kodayaushe yana tare da wayarsa yana chatting, sannan ya yi ta murmushi. Ganin hakan hankalinta ya tashi sosai domin a xuciyarta akwai wacce take son ya aura, aurenta kawai shi ne za su saka mata abin da ta yi musu, don haka ta yanke shawarar za ta same shi ta sanar da shi, kamar yadda ta lura ita ma Mama tana son haɗa auren, amma kuma da ta tuna soyayyar da Marwana take yi, sai jikinta yayi sanyi sosai.

Annur ya ci gaba da zuwa gurinta, tun tana ɓoyewa har Ingawa ya sani. Ganin hakan sai ha kalinsa ya tashi sosai. Sai ya fara mata ƙorafin tun da sun fahimci juna kawai a sanya rana.

Ta gefen Annur kuwa yana ta nuna matakalar soyayyarshi, sannan yana ƙara sanya jinin Damir yana hawa, domin duk abin da ya faru tsakaninsu sai ya gaya masa, wanda yake tayar da hankalinsa matuƙar gaske.

Ta bangaren Baba duk nacin Ahmad ya bar gidan, amma ina domin ta tamkar ya zama kurma haka ya koma, kuma ya rantse ko kashe shi zai yi ba zai saki Mama ba, duk da ba ta kula shi kwana kawai yake yi a ɗakinta, amma ita kanta ta rantse sai ya sake ta. Ahmad tun da ya dawo ko sisi bai taɓa haɗa su ba, saboda ya tsane shi sam babu tausayin ɗa da mahaifi a tsakaninsu.

Nasreen ce kawai yake takurawa, ta yi masa hidima ita ma ba tare da Ahmad ya sani ba.

Faruk sai da aka yi musu albashi, sannan ya sanya mai a mota, ya kuma wanke motar ya shirya zuwa gidansu Nasreen.

A lokacin da ya isa kofar gidan, sai ya cika da mamaki ganin an gyara gidan. Tunanin da ya faɗo masa Baba ya ɗauko rigimar da aka sayar da gidan. Hankalinsa ya kwanta sosai, domin hakan zai ba shi damar mayar da ita cikin ruwan sanyi, domin yasan cewa yanzu tana nan cikin mugun halin da za ta gwammace zaman gidansa da zawarci.

Yana tsaye a gurin, cikin tunanin yadda za a yi a kira masa ita, sai ya ga wani yaro ɗan maƙocinsu.

"Yauwa kai zo nan."Ya ce tare da fara tafiya gurin yaron.

"Nasreen za ka kira mini." Kallon sa yaron ya yi yana son gane ko baƙo ne.Yadda yake kallonsa cikin mamaki, sai ya ƙara tabbatar da abin da zuciyarsa ta gaya masa.

"Nasreen sun tashi ai yanzu bata a gidan ita da mamansu."

"Ya sayar da gidan." Ya ce a ransa yana ayyana rayuwar wahalar da suke ciki.

"Don Allah za ka kaini gidan?"

"Eh mu je, amma akwai nisa sosai."

"Karka damu zan dawo da kai."

Yaron cikin murna, ya shige gaban motar Faruk yana ta zare idanu. Sun yi nisa sosai, yaron ya nuna masa unguwar masu kuɗi ya ce,"Nan za ka shiga a nan unguwarsu take."

Da sauri ya zaro ido tare da rage gudun motar."Nasreen fa na ke gaya maka yar gidan Bukar ƙanwar Ahmad!" Ya ce masa yana kallonsa cikin mamaki gain inda ya kaisu.

"Eh ba wacce ƴaƴanta ya ɓata ba kuma tana da yara biyu?"

"Ita wata yar fara-far siririya."

"Na santa nan ne unguwarsu."

Tsoro ya bayyana a fuskarsa, da sauri ya kalle sa ya ce,"Ta yi aure ne?"

"A'a mu je ai mun kusa zuwa gidansu." Yaron ya faɗa cikin ƙosawar tambayar da yake masa.

Ganin haka sai ya yi shiru, ya ƙara gudun motar zuciyarsa na bugawa da sauri tunani sosai yake zuwan masa. Take ya fara tunanin ko su Marwana sun dawo rayuwarta ne? Wannan tambaya da zuciyarsa ta yi masa sai, da ya ji kamar sama za ta faɗo kansa, domin ko alokacin da yake Faruk ɗinsa da yana masifar shakkarta, ballanatana yanzu da duniya ta yi masa atishawar tsaki.

Bai gama shiga cikin mamaki ba, sai da suka kai kofar gidan. Yaron ya dakatar da shi tare da nuna masa get ɗin gidan, yana jira ya ba shi tukuci. Wani irin tashin hankali ya ziyarce sa. Lokaci guda kansa ya fara juyawa tamkar ana murza sitiyarin mota.

Da sauri ya kalle shi cikin tsanannin mamaki."Nan ne gidan?" Ya yi masa tambayar cikin rashin hayyaci.

Cikin fariciki yaron ya washe baki, ya fara magana ba tare da ya lura da halin da ya shiga ba."Eh nan ne sabon gidan da Yay..."

Kafin ya gama maganar, sai ya ji ana ƙoƙarin buɗe get gidan. Da sauri Faruk ya ƙuraawa get ɗin gidan ido yana kallo. Burinsa Nasreen ta fito don ya tabbata da maganar yaron, amma sai ya ga Baba ya buɗe get ɗin gidan ya fito, da sabuwar rediyo da yana saurara. Ya yi ƙiba ya canza hatta shigar shi ta canza.

Matsawa ya yi, cikin tsananin razana yana zare ido. Tsoro firgici da tashi hankali suka ziyarce shi.

Baba da yake cikin fariciki har da yar waƙarsa yana tafiya. Ba tare da ya lura da Faruk yake cikin tsanannin tashin hankali ba. Yaron da ya ga Faruk ya shiga cikin ruɗani sai ya kalle shi ya ce."Ga Baban Nasreen nan ma ya fito."

Da sauri Baba ya kalle shi, tare da zabura cikin tsananin mamaki. Shi ma zaburar ya yi, yana jin lamarin kamar a mafarki.

Goge idanunsa Baba ya yi, tare da aro rigar rashin mutunci ya sanya. Lokaci guda fuskarsa ta canza ya ci magani.

Faruk ganin yadda ya yi, sai tsoro ya kama shi jikin shi ya kama rawa. Kallon Baba ya yi, da ya ɗora hannunsa a kirji yana dariyar muguntar ganin yadda ya koma. "Wayyo Duniya mai kirari da yawa; in ji kwaɗo ya ce wai juyi-juyi da ya ji shi a cikin ruwan zafi.
Duniya rawar 'yan mata, mai karambani a gaba sai ta watso shi baya;
Duniya mai halin ɗan mangwaro, sai an sakankance ana tsotsar ta sai ta sulluɓe ta gudu." Baba ya ƙarashe karin maganar cikin muryar waƙa yana wata irin shegiyar dariyar da ko kyau ba ta yi masa ba.

Kallon Faruk ya yi, da ya zare ido yana kallo da kamar zai yi hauka. Tamke fuska ya yi yana ƙarasowa gurinsa.

"Kai tijararre uban mai ya kawo ka gidan nan?" Ya yi masa tambayar yana zagaye shi yana kallonsa kamar ranar ya taɓa ganin.

Farouk da yake cikin tsananin tashin hankali. Zare idanunsa ya yi ya kasa magana sai kallonsa yake.
"Dangin ƙaruna magana na ke yi." Ya daka masa tsawa yana faɗin haka.

Jikinsa na rawa ya kalle shi ya buɗe baki zai yi magana, sai ya kasa yana raba idanunsa. "Tambayarka nake yi uban mai ya kawo ka gidan nan?"

"Eh... am na zo ganin yarana ne." Ya furta cikin rawar murya, yana mamakin yadda aka yi suka canza gida.

"Au dama akwai yaranka a gidan nan? Har kana da bakin da zaka iya furta yaranka? Yaran da ka wulaƙanta su da mahaifiyarsu, sai yanxu da duniya ta yi maka tutsin mage sai ka lallaɓo ka kwaso ƙafafunka kamar na biri ka zo?"

Kasa magana ya yi, yana ta masa tijara, amma ya kasa cewa komai. Tunanin yadda aka yi rayuwarsu ta canza yake yi. Ganin zai tara masa mutane, saboda magana yake yi da karfi ya sanya shi sausauta murya ya ce,"Bab..."

"Kul Karka sake ka kira ni da ubanka uban Nasreen dai." Ya daka matsa tsawa yana faɗin haka.

Kasa magana ya yi, yana shafa kansa cikin tashin hankali, daidai lokacin da Ahmad ya fito zai shiga cikin mota zai fita. Maigadi ya wangame get yana jiran ya fito.

Faruk jin an buɗe get ɗin gidan, da sauri ya kalli cikin gidan burinsa kawai ya ga Nasreen. Ahmad fasa shiga cikin mota ya yi jin muryar Baba.

Fitowa ya yi daga gidan, yana son ganin wanda yake tsaye a kofar gidan. Cikin tsananin mamaki Faruk ya kalle shi ya ce,"Ahmad!"

Ahmad kallon sa ya yi, shi ma cikin tsananin mamakin ganinsa, sai kuma ya ci magani yana watsa masa mugun kallo.

Kallon juna suka ƙara yi, kowa zuciyarsa da abin da yake tsaƙawa. Mamaki sosai Faruk yake yi, ganin yadda Ahmad ya canza ya dawo dan gayu jikinsa ya yi kyau ga hutu ga ƙiba da ya yi.
Chapter 62 · 0% Book details