Sashe 57
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Amma ko mai nayi masa ai ba a sake wa tuwo suna? Saboda har yanzu ina nan da matsayina na mahaifinsa?"
"Ana sakewa in har ya kwana ya zama ɗumame." Mama ta ce masa tare da shigewa cikin ɗakinta.
Nasreen tana shiga cikin ɗaki ta kira wayar Marwana."Na yi mota Marwana Ya Ahmad ya siya mini mota." Ta ƙarashe maganar cikin ihu.
Ita ma ihun murna ta sanya sannan ta ce,"Na yi miki murna sosai sai na zo gani."
"Ya ce zan fara zuwa gurin koyon mota."
"Ki gaya masa zan koya miki."
"Yauwa na gode sosai."
"Su Nasreen an zaman yan mata wayyo Allah ina ma Faruk zai ganki?"
Tsaki ta yi ta ce,"Bana fatan Allah ya ƙara haɗa ni da shi." Sallama ta yi mata kashe wayar.
Cikin nasara ta fara koyon moton don har ta fara iyawa. Mai mai tsada da suka siyo ta fara shafawa. Lokaci guda ta canza ta zama mace mai class. In har ka san Nasreen a da to ina tabbata maka yanxu ba za ka gane ta ba. Ita kanta sai ta yi ta kallon madubi wai ita ce kuwa. Dan kwanakin da suka yi a cikin daula, ta jikinta ya canza ta goge sosai ta zama tamkar tarwaɗa. Ko ina ya ciko sai juyi ta ke yi abinta tubarkallah.
Ranar da Marwana ta biyo mata za su je wankin kai. Mamaki ya kamata tsaya tana kallonta. "Nasreen kin ga kuwa yadda ki koma?"
Dariya ta yi tare da kama hannunta."Mu je don Allah. In kowa yana mamakin canzawata har da ke?"
"Hmmmmh! Ba ki ga yadda kika koma bane wallahi ni kaina da nake mace kamar na haɗiye ki. Ina ga gobe zan kawo Ya Annur gidanku na huta da mitar da yake mini."
Ba ta ce mata komai ba, sai ta yi dariya kawai. Ƙara kallonta ta yi tana fatan ina ma ace Damir zai ganta. Da suka shiga mota. A motar Nasreen suka fita. Ita ce take tuƙa su.
"Yaushe za ki koma aiki?"
Jin tambayar da ta yi mata ta bata fuska."Ni fa aikin nann."
"Karki manta Mommy da kanta ta zo ta bada haƙuri, sai dai kuma in za ki bijire mata."
"Ni na isa ƙarshen wata in sha Allahu. Ingawa ma yana ta mini ƙorafi."
Tsaki ta yi ba tare da ta ce komai ba jin abinda ta ce.
Damir ya shiga cikin wani yanayi tun ranar da abin ya faru. Ji yake rayuwarsa wani iri. Hatta Little Marwana ya shafe ta, domin ya daina kula da ita kamar yadda yake yi a da.
Ya daina surutu komi sai kallo, in yan gida to yana ɗaƙinsa a kulle yana kwance. Ba bacci yake yi ba, amma ya gwammce ya zauna shi kaɗai. In kuwa gurin aiki ya je shi ma baya samun sauƙin domin duk ma'akacin da zai shigo yana kalla da ta window. Burinsa zancen aje aikin ya zama wasa, amma har akayi sati biyu da faruwar haka ba ta zo ba. Hankalinsa ya yi matuƙar tashi, saboda wani yana yi da ya tsinci kansa. Sai ya rinƙa shiga damuwa ina y tuna ba ta kampanin, saboda damuwar da ya sanya wa kansa har faɗawa ya yi,ga shi Momi ta yi halin ko ina kula da rayuwarsa. Ko abinci ta ce masa ga shi ya ce ba zai ci ba, to ba za ta ƙara masa maganar ba, saɓanin da za ta tas shi a gaba kamar wani karamin yaro har sai ya ci.
Lamarin Marwana kuwa shi yafi ƙona masa rai, saboda kullum a gidan nan ba ta da zance sai Ahmad ya yi wa Nasreen kaza. Nasreen kaza kuma abin takaici Momi da Muhsin su yi ta biye mata ana hirar..
Gabakiɗaya ya zame musu bare a cikin gidan. Hatta Little Marwana fita sabgarshi take yi, ganin yadda yake ci magani ta maƙale wa su Hajiya. Damuwa ta yi masa yawa. Ga yawan tunanin abin da ya yi mata, wanda suke sanya yan jin takaicin cutar da ita da ya yi, hakan kuma ke nasarar saka tausayinta da yake rikiɗewa yan zama masa abin da baya fatan shi ne.
Wani lamarin da ya kara damunsa a yanzu feelings ɗinsa yana canzawa, saɓanin da yake jin ya yi isolating kansa da kowa, domin in har yana cikin mutane hatta atmosphere na gurin ba ya yi masa daidai, amma yanzu sai ya ji he is feeling lonely a lot. Lonely da yake sa zuciyarsa cikin tsananin buƙatar some one that will keeps his accompany, if possible ya ji mutum a jikinsa har ya yi hugging ɗinsa, wannan sabon al'amari da yake ji dai ya rikita tunaninsa, don haka ya jawo yarsa Little Marwana kullum yana tare da ita, don ta ɗauke masa wannan kewar, amma kuma sai dai babu abin da ya ragu, domin wannan kewar daban ce ba irin wanda za ta ɗauke masa ba.
Ganin yana ƙoƙarin cutar da kansa sai yake kokarin fitowa falo, amma babu amfani, domin da alama mutanen gidan sun gaji da halinsa, domin babu wanda ke kula shi sai dai su yi ta hirarsu. Shi ne da ya ke binsu dai idanu yana fakewa da kallo yake yi, amma duka bin da suke cewa babu wanda ba ya ji,musamman in suka ɗauko hirar gidansu Nasreen sai ya mayar da hankali fiye da da.
A hankali ya tashi ya fara hawa sama tamkar marayan da ya rasa uwarsa. Kallo suka bi shi da shi har ya haye. Momi ce ta yi tsaki ta ce,"Wallahi Yayanki haushi yake bani sosai, saboda na tabbata da ace shi ya mutu, Batula ba za ta yi wannan jimammin haka ba."
"Mai zai sanya ta yi Mommy? Musamman zai bar mata arziki, amma shi har yanzu ya kasa mantawa da ita ya fuskanci rayuwarsa na gaba."
Shiru kawai ta yi saboda takaici ba ta tare da ta ce komai ba.
Da ya shiga cikin ɗaƙinsa kan gado ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, tare da janyo filo ya matse a ƙirjinsa. Idanunsa suka canza daga farare tare zuwa wasu kalar. Ya daɗe a wannan halin ya jin tamkar ya mayar da filon cikin jikinsa kafin bacci mai karfin gaske ya kwashe shi. Bacci da ya yi, ya ɗan samu raɗaɗin ƙuncin da zuciyarsa take ciki.
Yana zaune ofis ransa na ƙuna Muhsin ya yi sallama ya shigo."Na rasa yadda aka yi ma'aikatan nan suka raina ni, sam ba sa son zuwa aiki kowa sai ya rinƙa fashi duk lokacin da ya ga dama. To ka gaya musu duk wanda ya kara fashi sai na cire kuɗinsa."
Kallonsa ya yi cikin mamaki."Amma kuma Ya Damir suna ƙoƙari fa, kuma yau kowa ya zo aiki Nasreen ce kawai ba ta zuwa, kuma Marwana ta kawo maka resignation letter, sai mu nemi wanda zai yi replacing ɗinta."
Wani wawan tsaki ya ja don ba haka ya so ya ji ba. So yake ya gaya masa zai kara tuntubar Marwana ta dawo aiki, tun da ya ji Mommy ta je gidan, wataƙila ta ba ta haƙuri kuma ta haƙura. Tattara tarkacensa ya yi ya fice daga ofis ɗin. Muhsin raka shi da idanun ya yi tare da murmushi ya girgiza kansa.
Ya dawo daga gurin aiki ya shigo falo. Suna zaune suna kallo ya yi sallama. Zama gefen Momi daidai lokacin da Marwana ta fito da ɗan kunni tana faɗin,"Mommy taimaka mini ki sanya mini dan kunnin nan, Ya Annur ya kira ni yana hanya za mu je gidansu Nasreen."
Wani irin kallo ya watsa musu yayin da ya ji maganar ta duki zuciyarsa."Ke ma kin cika nawa tun safe ya sanar miki sai ki shirya."
"Mommy little Marwana ta wahalar da ni gurin parking gashinta." Jin abin da ta ce sai ta yi dariya.
"Na lura yau tsiya ta ke ji."
"Sosai har sai da na ce mata zan kaita gurin Raihan." Murmushi Mommy ta yi bayan ta sanya mata dan kunnin ta ce,"Ga hon ɗinsa nan kamar yana kofar gida sai ki yi sauri."
"To kafin ya shigo bari na ɗauko mayafina. Momi da sawa Little Marwana takalminta." Ta ƙarashe maganar tana hawa upstairs da sauri.
Damir sai ya tsinci kansa da tashin hankali.Miƙewa ya yi yana jin kamar ya ja hannunta ya ce ba za ta je ba, amma sai kuma ya fara tafiya ba tare da ya kalle su ba."
Yana ƙoƙarin hawa sama Annur ya shigo. Cikin girmama ya gaishe da Mommy tare da ƙarasawa gurina ya miƙa masa hannu.
Haushinsa sosai yake ji tamkar ya rufe shi da duka. A maimakon ya ba shi hannu sai ya zura cikin aljihun wandonsa.
Ganin haka ya zauna yana kallonsa. Miƙewa Mommy ta yi."Bari na sanya Hajjo ta kawo maka ruwa, kafin Marwana ta fito." Ta nufi hanyar kicin.
"Yane Damir?Zan je zance tun da ka ƙi yi mini hanya, ka je ɗaurin aure ai?"
Wani banzan kallo ya watsa masa tare da jan ƙaramin tsaki ya haye sama da sassarfa.
Marwana ce ta sauko tana murmushi."Sarkin nawa har yanzu ba ki shirya ba?"
"Kai Yaya Annur na shirya muje." Jin abin da ta faɗa ua miƙe yana yi wa Hajiya sallama.
Nasreen tana kicin tana haɗa salat, cikin sauri saboda Marwana ta kira ta ta sanar mata suna hanya. Tana ƙoƙarin kaiwa dinning ta shiga wanka Ya Ahmad ya shigo.
'"Babu inda zan je, saboda ina son na ga ƙanwata tana zance." Dariya ta yi tare da rufe idanunta cikin jin kunya.
Yana ta tsokanar ta su Marwana suka iso. Fita falo ya yi domin ya ƙosa ta zo, tun da aka ce za ta zo ya ƙosa, ya rasa dalilin da ya sa yake jin nauyinta da son ganinta.
Tana shigowa ganinsa a falo ta ji nauyi. Cikin jin kunya duk gaisa sannan ya saki ajiyar zuciya ya fita.
Nasreen ce ta fito cikin shiga ta alfarma. Cikin jin kunya ta saci kallon Annur saboda ba ta san shi ba. Ganinsa kyakyawa sai ta ji ya kwanta mata.