← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 92

Sashe 55

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakin takaddar ya yi ta faɗi, ƙasa ya tureta ya shige cikin ɗakin cikin tashin hankali. Yana shiga ya karasa gurin frij ya ɗauki ruwa mai sanyi ya sha. Kansa ya hada da gini yana bugawa. So yake ya mutu sam ba ya jin daɗin rayuwar sa. Ya rasa yadda aka yi ya kasa yafe mata abin da ya faru, domin in har zai ganta sai ya rinƙa jin bugun zuciya da damuwa, wannan dalilin ya sanya shi ƙuntata mata. Lokaci guda rikice hawaye yana sauka ƙuncinsa jin har ya yi mata rauni. Shi da ko kiyashi ba ya cutar da shi, amma saboda mutuwar Batula mace da yake tausayi a rayuwarsa ya ita cutar. Damuwa ce a ransa sosai yana buƙatar wanda zai ba shi shawara. Ya rasa yadda zai yi domin duk ya ganta sai ya ji ya shiga cikin damuwa. Da tsintar kansa a yanayin da ya kasa ganewa domin zuciyarsa da tunkinsa rikicewa suke yi. Wani irin tausayi da kunyarta suka kamashi har ya ji yankin kunyar haɗa idanu da ita. Kansa ne ya kulle damuwa ta yi masa yawa. Sai kawai ya miƙe zuwa bayi ya sakarwa kansa shower ba tare da ya tube kayan jikinsa ba. Saukar ruwan da hawayen da yake zubarwa, suka taru suka ƙara sanya masa damuwa a maimakon ya ji sanyi. Tsawon lokaci ya ɗauka a haka domin gani yake kamar hakan ne mafita, amma jin damuwarsa tana ƙaruwa da sauri ya yi alwala ya fito ya ɗauko maganin damuwar komai ya fara karantawa. A hankali zuciyarsa ta fara sakkowa har ya ji ɗan natsuwa. Sosai yake jin babu daɗi abin da ya aikata mata. Rintse idanunsa ya yi yana tuno lokacin da ya ganta cikin ruwan tare da watsa mata ruwan da ya yi. Haƙiƙa ya zama azzalumi kuma matsoraci ya rasa wanda zai yi faɗa da ita sai mace macen ma, wacce tasha wahala a rayuwaarta take buƙatar tallafawa. Jin ɗan'uwanta ya dawo ya yi matuƙar farinciki da haka. Tuna ta bar aikin gabansa ya yi wani irin faɗuwar da sai da ya dage gurin.

Marwana zama tayi tana cika tana batsewa saboda abin da ya yi. Zuciyarta ta sare kan haɗa su soyayya.

Ayi mini hakuri na koma gurin aiki ne malamar makaranta ce ni. In ana son na ci gaba da safe da yamma a rikitani da comments sai na cigaba da safe da yamma. Kusan ina mugun yinku.❤️❤️❤️❤️❤️
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 29

Marwana zama tayi tana cika tana batsewa saboda abin da ya yi. Zuciyarta ta sare kan haɗa su soyayya. Hawaye sosai take yi domin ya ba ta haushi. Hajiya ce ta zauna a gefenta ta kama hannunta.

"Ki yi haƙuri zan je na bata haƙuri da kaina ba za ta ije aikin ba, kuma in sha Allahu sai ya saukko da kansa ya aureta."

"Momi ki ƙyale shi kawai yaje ya yi ta fama da soyayyar marigayiyar matarsa, amma lamarin Ya Damir ya fara ba ni haushi. In ya ga dama ya ƙare rayuwarsa babu aure. Ba zan takura mata ba, saboda she had enough tana buƙatar tayi farincikin. Ina ga zan turawa Ya Annur numbarta dama yana ta yi mini magiya, sai ya ganta a campany yana so."

Murmushi Momi ta yi ta c,"Ki tura masa wannan ma zai taimaka. Ki tura masa numbar kuma ki yi ƙoƙarin ki ga takula shi. Damir yana sonta zafin kishi da girman kai yake sanya shi wannan haukar, amma ki bari ya ga abokinsa a gurin, da kansa zai bayyana abin da ke dawainiya da shi."

Kallonta da sauri ya yi tana mamakin fasaharta."Aikuwa Momi yanzu zan tura masa da nambar." Ta karashe maganar tare da miƙewa ta shige cikin ɗaki da sauri.

"Ki shirya an jima sai ki kaini gidan."

"To Mommy," Ta ce tare da ƙarashe shigewa ta rufe ɗakin.

Tana shiga ta kwanta kan gado tana ganin shawarar Mommy za ta yi aiki. Numbar ta tura masa sannan ta kira wayar Nasreen. Nasreen da take ƙoƙarin kiranta wayar ya shigo.

"Hello, yanxu na ke shirin kiranki na sanar miki da abin mamaki."

"Ai tun da Ya Ahmad ya dawo, kullum cikin abin mamaki za ki yi ta gani." Ta furta cikin dariyar jin yadda take matuƙar farinciki.

"Wallahi kuwa Marwana wai ashe da ya tafi ba su samu aikin ba, kawai sai ya tafi gurin haƙin ma'adanai Allah ya taimaka mishi ya samu. Kin san tun kafin ya dawo ya sanya aka gina mana gida?"

Da sauri ta miƙe ta ce"Don girman Allah!" Jin yadda ta nuna farinciki sai ta ƙyalƙyace da dariya ta ce"Wallahi Marwana gida mai kyan gaske na yan gayu. Na ƙarƙare miki zan ce yanzu muna cikin gidan, kuma ya ce gobe zai je da ni kasuwa."

"Iyye Masha Allah mahaƙurci mawadaci. Kin zama yar gata Yaya Ahmad."

"Sosai yau ina cikin farinciki sai na ke ganin kamar a mafarki."

"Haka za ki gani wanka kawai xan yi, za mu zo da Hajiya sai ki yi mini text adireshin gidan."

"Ok sai kun zo bari na yi miki." Ta ce tare da kashe wayar.

Bayan ta fito daga wanka suka shirya zuwa gidan. Mamaki sosai Marwana ta yi ganin get ɗin gidan, sai kuma ta daina mamaki data tuna motar da ya zo da ita.

"Wai da gaske wannan gidan ya gina musu?" Momi ta yi tambayar cikin mamaki ganin get ɗin gidan.

"Masha Allah haihuwa ta yi rana." Ta furta daidai lokacin da Zainab ta ji hon ta buɗe musu gidan.

Marwana tana ƙoƙarin paking Nasreen ta fito cikin sauri. Idanunta a ƙasa ganin Hajiya. Abin da ya faru ya dawo mata har sai da ta yi ƙwalla. Ita kanta Hajiyar wataƙila ta tuna abin da ya faru ne, domin ganinta jikinta ya yi sosai.

"Ina wuni momi?" Ta ce tare da durƙusawa sai hawaye.

Hannunta ta kama ta miƙar da ita."Nasreen ya kike da yaranki ina Mamanki."

"Tana ciki yanzu ta shiga wanka, mu shiga ciki."

Ta furta tana kallon Marwana da ta kulle motar ta rungumeta. "Gida ya yi kyau Allah ya sanya alkahiri."

"Amin," Ta amsa sannan suka rankaya suka shiga ciki.

Mamaki sosai suka rinƙa yi ganin yadda gidan ya haɗu. Mama ta fito daga cikin ɗakinta daidai lokacin da Ahmad ya yi sallama ya shigo.

Da sauri Marwana ta daga idanunta tana kallonsa. Tun daren jiya ta ƙosa ta ganshi da rana. Zuciyarta ce ta buga wanda ya sa ta saukar dakanta daidai lokacin da ya sanya idanunsa cikin nata. A tare suka kauda idanunsu. Ahmad ya karaso cikin jin kunya ya durƙusa.

"Ina wuni Hajiya?" Ya ce mata idanunsa a ƙasa domin kunyarta yake ji.

"Wannan shi ne Ahmad ɗan albarka ko?" Momi ta kalli Marwana tana faɗin haka.

Satan kallon shi ta yi da idanunsa yake kasa. A hankali ta ce,"Eh, shi ne."

"Masha Allah Allah ya yi maka albarka haƙiƙa ka zama ɗan halak."

Cikin jin kunya ya amsa sannan ya tashi ya shige ciki. So yake ya yi wa Marwana magana, amma sosai yake jin kunyarta sam ya kasa saki da ita.

Nasreen da Zainab suka kawo musu drinks da ruwa, sannan ta zauna tan shafa kan Raihann da take gefenta.

Sai suka yi shiru ganin shirun ya yi yawa Momi ta katse shurin ta hanyar cewa,"Ga shi Allah ya sake haɗamu a karo na biyu, ko a wancan shi ya haɗamu tsautsayi ya gifta, amma a wannan karon ina fatan ya zama ɗorewar xumuncin da zai sanya mu zama 'yan'uwa. Mu manta komai mu yi kokarin gida kyakkyawar alakar da zai mayar da jininmu daya?"

"In sha Allahu ai an zama ɗaya Marwana kamar Nasreen na ɗauke ta, abin da ta yi mana Ubangiji ne kawai zai bata lada, saboda ta bamu taimako sosai a rayuwar mu, sai dai mu yi mata fatan samun miji na gari." Mama ta faɗa tana kallonta.

"Masha Allah Ubangiji ya yi mata albarka."

"Amin,"Suka haɗa baki gurin faɗin haka.

Saboda rashin sabo, Hajiya da Mama ba su yi hira sosai ba, sai Nasreen da Marwana suke ta hira.

Sai da za su tafi Mommy ta kalli Mama ta ce,"Ayi haƙuri abin da Damir ya yi, don na yi masa faɗa sosai kuma hakan ba zai ƙara faruwa ba, don Allah kar ya zama silar da zai raba zumunci ko ta aje aiki, domin duk yadda kuka samu buɗi aikin zai taimaka."

"Sosai kuwa ai aikin ma ya taimaka kuma yana kan yi. In sha Allahu da zarar ta warke za ta dawo aiki."

"Allah ya ba da lafiya yaran ne sai a hankali. Har yau ya kasa mantawa ya rungumi ƙaddara."

"Komai zai wuce aci gaba da masa addu'a."

"Muna nan muna yi." Mommy ta ce sannan suka shiga cikin motar suka tafi.

Suna fita Baba ya tsaya a ƙofar get ɗin gidan cikin tsananin mamaki."Ke don ubanki kar kar ki sanya na shiga gidan mutane su yi mini duka?" Ya ce mata cikin mamaki yana kallon gidan.

"Allah baba nan ne su Anty Nasreen suka dawo, muma Ya Ahmad ya ce zai mayar da gidanmu na zamani."

Mamaki sosai ya kama shi musamman da ya ga ta tura gidan ta shiga."Baba ka shigo su Anty Sha'awa ma suna ciki." Ta ce masa bayan ta leƙa cikin harabar gidan.

"Ikon Allah!" Ya furta daidai lokacin da ya tura kofar ya hango Musaddik da yake wasa a cikin gidan.

Da sauri ya shige da mulkin buhunsa. Anty Sha'awa ta fara ganinsa yana zare idanu, sannan ta nuna wa Nasreen da take riƙe da wayarta.
Chapter 55 · 0% Book details