← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 92

Sashe 25

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranar da ta cika kwana uku, yana zuba idon za ta dawo har ya cire rai. Da safe yana zaune a falon. Ya ji sallamar Yayarsa Asiya.

Cikin fara'a ya karɓe ta yana gaishe ta. Bayan sun gama gaisuwar sai ta kalle shi.

"Farouk, na ga gidan duk ya yi datti? Ko kana nufin karatun da take yi ba ta da lokacin da za ta kula da gidanta?"

"A'a tsawon sati biyu ba ta gida ta yi yaji?"

"Ya ji a wannan zamanin da maza suke tsada?"

"Shi ne ni ma na gani, saboda ko abincin da za ta ci a gidansu aiki ne a gareta."

"Amma kuma ta zauna ko? Wannan ya nuna maka ko babu abincin za ta iya zama. Kuma in ban dai Faruk, kafin ka aureta ba a gidansu take rayuwa ba. Ya kamata ka cire wannan tunanin talaka da mai kuɗi duk Allah ya yi su, kai da ka ga Allah ya azurta ka ba wayonka bane."

Shiru ya yi ba tare da ya ce mata komai ba, sai tsuke fuskarta da ya yi.

"Na san ba ka da kirki wani lokacin Faruk. Ga baƙar zuciya gaya mini mai ya haɗa ku, saboda yarinyar nan tana da haƙuri."

"Hmmmmh! Ba ki san ta bane saboda kin ganta shiru-shiru, wallahi ni kaɗai na san baƙincikin da na ke sha."

"Mai ta yi maka?"

"Ciki ta yi ni kuma na gaya mata ta zubar ban shirya haihuwa ba!"

"Kana da hankali kuwa? Cikin da ta samu shi ne ba ka so? Bayan wasu na nema."

"Gaskiya, ban shirya haihuwa ba. Na gaya mata muci amarcinmu kafin ta haihu, amma ta ƙi."

"Gaskiya Faruk, ba ka da kirki ko kaɗan, saboda wannan shi ya sa ka tura ta gidansu?"

"Ba ta jin magana babu yadda ban yi da ita ba, amma ta yi kunnen uwar shegu da ni."

"Mama zan kira na gaya mata abin da ka aikata. Ba a haihuwa aka haife ka. Kuma in ban da kai shashasha ne ai ka bari ta haihu ko sau ɗaya ne, amma da ƙuruciyarta sai ka lalatata mahaifa."

Tura bakinsa ya yi kamar ƙaramin yaro yana dana-sanin gaya mata.

"Hello, Mama ƙarar Faruku na kawo." Ta furta hakan bayan sun gaisa.

Ba tare da ɓata lokaci ba ta sanar mata da duk abin da ke faruwa. Cikin tsananin fushi ta ce a ba shi wayar.

Tatas ta yi masa tare da yi masa umurnin ya je ya dawo da ita.

Tsananin ɓacin rai ya kamashi, saboda da yasan za a yi masa dole, sam ba zai gaya mata ba.

Saboda fuskar da ya canza ba ta jima ba ta yi masa sallama. Bayan ta ƙara masa faɗa.

A ranar da ta ce ya je ya dawo da ita. Ƙin zuwa ya yi, duk da kiransa da ta rinƙa yi, kan ya haɗa su. Ganin ta yi fushi da safe ya shirya kafin ya tafi aiki.

Hon ya rinƙa yi babu ƙauƙautawa. Baba ne ya fito tsakar gida.

"Ki shirya ma za ki bi tijararren mijinki."

Jikinta a sanyaye ta ɗauki mayafinta ta fito. Tana shiga cikin motar ya saki wawan tsaki yana kallonta."Kin ji na rantse miki da ga wannan cikin ba za ki ƙara haihuwa ba, sai lokacin da na shirya."

Ba ta ce masa komai ba ta ja bakinta ta tsuke. Ya gama bambaminsa ya gaji ya yi shiru. Da suka koma gida yana sauke ta ya juya. Ciki ta shiga ta gyara gidan, don tun da ta tafi ko tsinke bai taɓa kawar wa ba. Bayan ta gama gyaran gidan, sannan ta dafa musu taliya.

Da dadddare ya dawo tana kwance a kan doguwar kujera. Ganin ya shigo ya sa ta miƙe tana gyara ɗaurin ɗankwalinta, tana kallonsa don ba ta ji shigowarsa ba, saboda baccin da ya kwashe ta.

"Sannu da dawowa."

"Yauwa,"Ya amsa da fuskar shanu.

Abinci ta kawo masa ya ci ba tare da ya ce komai ba. Ganin yadda yake cika sai ta tashi ta bar masa falon. Sai da ya gama duk abin da yake yi, sannan ya buɗe ɗakinta ya shigo.

"Kin yi bacci ne?"Ya ce tare da zama a gefen gadon yana bubbuga gadon.

Buɗe idanunta ta yi sannan ta kalle shi.Hawa gadon ya yi babu kunya ya janyota ya rungume yana sauke numfashi. Sai da ya gama abin da zai yi, sannan ya koma gefe ya fara bacci.

A haka suka ji gaba da rayuwar yau fari gobe tsumma. Duk abin da yake mata haƙuri take yi, domin haƙurin shi ya fi. Ganin Ahmad yana matuƙar kula da ita sai hankalinta ya kwanta. Ta ci gaba da rainon cikinta tana karatunta.

Cikin har ya shiga wata bakwai, amma ko ɗan kamfai bai taɓa siye ba. Ganin haka ta same shi yana zaune."Ina son magana da kai." Ta ce masa tare da zama kusa da shi. Kallonta ya yi hankalinsa na kan wayrsa da yake chatting.

"Ina jin ki." Ya furta tare da mayar da hankalinsa kan wayarsa.

"Yaushe za ka fara siyayyan kayan haihuwa? Cikina wata bakwai ƙarshen watannan zai shiga takwas."

Daina typing ɗin ya yi yana kallon ta."Kamar ya ya siyayya? Me kike so na siya? Ba kayan da jariri zai sanya ɗan kala ɗaya ko biyu sai famfas da zan siya ba, kafin ki samu na suna?"

Jin tambayar rainin wayon da ya yi mata ya sanya ta kalle shi cikin mamaki."Faruk, ko wace mace in ta samu ciki za ta haihu, mijinta yana ba ta kuɗi ko ya ɗauke ta su je kasuwa, don ayi wa jaririn siyayya."

"To sai ki gaya mini tun da ban sani ba. Nufin ki so kike na ba ki kuɗi ki je kasuwa tun da ban san me na ke yi ba ko?"

"Za ka iya zuwa ka siyo, damuwata kar na ta shi haihuwa babu kayan da za a sa."

"Kar ki gaya mini maganar banza. Tun da gani matsiyaci ko? Zan baki naira dubu goma ki je ki yi siyayyar.."

"Dubu goma da ka ce Faruk?" Ta tambaye shi cikin zallar mamaki.

"In kin raina ki siya da kanki tun haƙosu na ke yi."

Mamakinsa ya kamata don a tunaninta dubu gomar bai wuce su sayi pampas ba.

Washegari ya cire dubu goma ya ba ta. Galala ta yi tana kallonsa. Ganin ba za ta karɓa ba ya sanya shi ije kuɗin ya fice. Ahmad ta kira tana kuka ta gaya masa. Bayan ya ba ta haƙuri ya bata dubu goma sha biyar ta haɗa ta yi siyayyar. Duk da ranar da za ta awo sai sun yi faɗa, watarana ma Ahmad yake ba ta ta je. A haka ta rainin cikin har ya isa haihuwa. Cikin dare na naƙuda ta kamata. Da fari banza da ita ya yi yaci gaba da baccinsa, sai da ya ga lamarin ya girmama ta fita hayyacinta, sannan ya kwashe ta suka tafi asibiti. Cikin ikon Allah bayan ta sha baƙar wuya, ta haifi yarta mace aka sanya mata . Ranar suna ƙin taro ya yi sai dai kawai ka radawa 'yar suna da Raihan.

Tun kafin ta yi arba'in ya so ta fara planning amma sai ta ƙi tashin yin hakan ya ƙara sukurkuta rayuwar aure su. Raihan na da wata goma ta ƙara samun ciki, inda ya buga tsalle kan sai ta zubar da ciki. An kai ruwa rana kafin ya haƙura don har sai da mahaifiyarsa ta sanya baki. Tun da ta haifi Musaddik rayuwar aurensu ta ƙara tabarbarewa. Faruk irin maza nan ne wanda suke son kulawar mace, ga kuma shegen maƙo baya barinsa ya ba da abun da za a gyara masa jikin. Idanunsa a buɗe suke sosai, domin yana san mace wacce take 'yar bariki, sai aka ci rashin Sa'a ya auri Nasreen mai kunya da hankali. Ga shi dai zaman su ya ƙare kuma ya auri mace da yake so, sai mu yi musu fatan zaman lafiya.

AN DAWO LABARI

Barka da sallah fans ɗina ina yi muku Barka da sallah tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. Sai na zo muku yawon sallah. Tamu Jamila lawal Zango Jamsy❤️❤️❤️❤️❤️🙏🙏🙏💃💃 Nasreen, Damir, Marwana, har ma da Faruk capacity yana muku barka da sallah.
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 13

Kuka take yi sosai, har Mama ta gama dafa mata ruwan wankan ta kai mata bayi. Tana wanka tana kuka. Abin da take gudu kenan, wannan dalilin ya sanya ta jure duk wani tozarci, amma ga shi daga ƙarshe dai dole hakan ta faru. Bayan ta gama wankan ta shafa mai. Ta kwanta sakamakon zazzaɓi mai zafi da ya rufe ta.

Baba kuwa yana tafiya yana zagi da surutu kamar mahaukaci. Takaicin sakin yake yi sosai, saboda kafin ta zo da yunwa ta ishe shi har ya fara tunanin kiransa. Duk da ya san sai ya wulaƙanta shi kafin ya ba shi, amma da yanzu ƙila ya samu abin da zai ci.

Da ya isa gidan da ƙarfi yake buga get ɗin gidan. Farouk na zaune tun da ya yi sakin ya zauna ya kasa fita. Sai ɗura mata ashar yake yi. Kulle ɗakinta ya yi, don kar ta aiko wani daga gidansu, sannan ya gargaɗi Rashida a kan kar ta sake ta bari a shigo.

Ita dai shiru ta yi masa dukan da ya yi masa ta ga rashin imaninsa. Tana zaune a gidansa yana ta danna ashariya kamar wani bamaguje, duk da cewar ta ji daɗin sakin, domin yanzu za ta sakata ta wala a gidan, amma zagi da tijarar da yake ya matukar ba ta mamaki.
Chapter 25 · 0% Book details