Sashe 33
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke tafi ki ba ni guri ni na haife shi ko shi?" Ta daka mata tsawa tana faɗin hakan.
"Allah ya ba ki haƙuri." Ta ce tare da ficewa cikin ɗakin hankalinta a tashe.
Kai tsaye mota ta nufa bayan ta buɗe ta shiga. Zama ta yi tana jin yadda kanta ke juyawa. "Mai ya sa ba ke jin kamar akwai wata alaƙa da za ta ƙullu da Damir da Nasreen?" Ta yi wa kanta tambayar cikin ruɗani, jin abin da Hajiya ta ce.
"To, in haka zai faru ta yaya?" A wannan karon tashin hankalinta ya fi na ko yaushe tuna abin da ya faru.
Cikin sanyin jiki take tuƙa motarta. Kai tsaye kasuwa ta wuce ta siya kayan abinci da yawa. Gidan su Nasreen ta je a lokacin tana zaune a tsakar gida Raihann a kan cinyarta tana mata tsifa.
Ganinta ya sanya ta sauke ta tare da nufarsa cikin tsananin farinciki."Jiya na kasa bacci ina ta tunanin ki Nasreen."
Dariya ta yi jin abin da ta ce."Ni ma jiya bacci ɓarawo ne kawai ya sace ni, saboda na cire tsammanin dawowarki cikin rayuwata."
"Allah ya haɗamu shi ya san dalilinsa." Ta ƙarashe maganar hankalinta na gurin Raihan da ta riƙe hannunta.
"Haka ne." Nasreen ta ce sannan suka shiga ciki. Cikin girmama ta gaishe da Mama. Bayan sun ɗan jima suna hira ta miƙe,"Zan je school, in sha Allah zan dawo ba da jimawa ba, sannan akwai kaya a motata ko za ki sanya yara su kwaso."
Jikinta ya yi sanyi jin abin da ta ce,"Marwana, ba na..."
"Please, don Allah kar ki ce komai ko tuna abin da ya faru."
"Yarinya dole ne saboda rabuwar rashin mutuncin da aka yi, kuma mahaifinyarki ta yi miki mummunar lafazi, bai kamata ace kin ƙara shigo rayuwarmu ba."
Murmushi ta yi tare da ƙarasawa gurinta."Kar ki damu Mama, Ubangiji ya ga zuciyata na don taimakawa, kuma shi zai kawo mini mafita."
"Allah ya yi miki albarka." Ta furta tana mamakin kirkinta.
"Amin,"Ta amsa sannan suka fita waje.
Ganin kayan da ta kawo mata ya matukar razanata. Kallonta take yi cikin tsananin mamaki."Kina da kirki ban taɓa ganin mutum mai kirki da son talaka ba, irin ki. Haƙiƙa zuciyarki daban take da sauran masu hannu da shuni."
"Akwai banbanci a tsakaninmu ne? Ubangiji bai bambanta mu ba, sai ta gurin ibada."
"Na gode Allah ya saka da alkhairi." Ta ce tare da rungumeta tana murna.
A lokacin da aka fara shiga da kayan, Baba ya fito ya tsaya yana kallon ikon Allah. Babu kunya ya fara murna yana jin kamar zai sume. Zama ya yi yana kallon kayan sai kuma ya fice zuwa waje.
Marwana tana ƙoƙarin tayar da mota ya ƙaraso. Addu'a ya shiga yi mata mai kama da roƙo. Kallonsa take yi tana jin sam ta tsane shi, amma saboda Nasreen ta cire dubu goma ta ba shi. Kamar zai goyata haka ya rinƙa godiya ya shiga ciki.
"Kina ganin abin da yake miki ko? Fiye da hakan ya rinƙa yi wa Faruk a lokacin da ya zo neman aurena. Baba shi ne silar da mutuncina ya zube, kuma ya wulaƙanta rayuwata."
"Haƙiƙa bai kamata ya zama uba ba, amma ki ɗauki hakan a matsayin ƙaddararki."
"Babu komai na ɗauka, domin ni musulma ce, kuma na yi imani da ƙaddara." Ta ce tare da share hawayenta.
"Saura wata biyu ki gama service ko?"
"Eh,"Ta amsa tana kallonta.
"Allah ya ba da sa'a." Ta ce mata tana mata murmushi a zuciyarta ita kawai ta san abin da take tsaƙawa.
"Amin,"Ta amsa tana mayar mata da murmushin.
Sai da ta bar ƙofar gidan, sannan ta juya ta shiga ciki gidan. Tana jin ta kamar 'yar'uwarta na jini.
Tana shiga cikin gidan, ta samu Baba ya zauna kan kayan yana ta zuba."Yauwa Nasreen, na tsare miki kayan ne, kin san gidan nan kamar 'ya'yan ɓera suke yanzu sai ki zo kiga an iba."
"Yaranka kake kira 'ya'yan ɓera? Anya kana neman musu shiriya kuwa?" Goggo ta furta tana kallon sa.
Ba tare da ya ce mata komai ba ya zabga mata harara. Jikinsa har rawa yake yi yana kallon kayan
"Nasreen, ko zo ki bani nawa kasan ɗaki za ki shiga?" Ya ce mata ganin yadda ta sha kunu za ta wuce.
"Mama, za ta raba kayan." Ta ce tare da shiga cikin ɗaki, ba ta ji mai ya faɗa ba. Mamakin yadda ya yi mata maganar cikin taushi ta yi.
"Shege ɗan iska Faruk, dole hankalinsa ya tashi ganinta da waɗannan yan gayun, ashe dama mutanen da take tarayya da su ba ya so, sun fi shi arziki?" Babu wanda ya tanka masa. Ganin haka ya sanya hannu ya ibi kayan da yake so ya shiga ciki.
Mama ce ta kwashi sauran kayan, ta kai ɗakinta a ranta tana takaicin halinsa.
Duka mutanen gidan zaune a dinning suna karyarwa. Damir hankalinsa a kan Little Marwana da take shan tea. Kallonta yake kamar ya lashe, musamman yadda ya ga ta ƙara girma.
"Damir, maganar Ashman da aka yi na gwajin jini kamar gobe zai zo ko?"
"Eh, Mommy ya sanar mini."
"To ina so da zarar an kawo gwajin sai a gaya wa iyayensa su turo."
"In sha Allahu." Ya ce tare da tura wainar ƙwai a cikin bakinsa.
Ta ɗan saci kallonsa tana tsoron abin da za ta gaya masa, sai kuma ta daure ta ce,"Ka san yarinyar Hajiya A'isha?"
Gabansa ne ya faɗin ganin yadda ta maida hankalinta kan zancen tana kallonsa."Eh, ƙanwar Moh?"
"Ita fa yarinyar ai tana da hankali da kyau?"
Jin abin da ta ce sai ya kalle ta, ya dakata da cin abincin ba tare da ya ce komai ba, sai kuma ya daure ya ce,"Mommy, tun da Batula, ta mutu har yau ban ga mace mai hankali da natsuwa kamarta ba."
"Ina maka maganar rayyaye kana mini na matacce. Da zarar na yi maka magana, sai ka kawo mini ita. Tsawon wane lokaci, za ka ɗauka kana tunaninta?"
Ransa ya ɓaci sosai jin abin da ta faɗa."Yanzu Mommy, har kin manta da ita kina danganta ta da matacciya?"
"Tana da rai ne? Ta riga ta mutu Damir dole za ka manta da ita ka auri wata." Ta ƙarashe maganar cikin tsananin fusata.
"Ba zan iya ba Mommy, saboda na riga na yi mata alkawari, kuma babu macen da zan iya so..."
"Zancen banza!" Ta daka matsa tsawa da ya sanya shi miƙewa a razane yana kallonta.
"Matuƙar ina raye wallahi sai ka yi aure, na yi maka umurnin ka je ka ga yarinyar saboda tare na ke son na haɗa bikinka da na Marwa.."
"What?" Shi da Marwana suka zare ido tare da haɗa baki gurin faɗin haka.
"No, Mommy, gaskiya ba zai aure ta ba, saboda sam ba kalar sa ba ce." Marwana ta furta zufa na keto mata, domin zuciyarta akwai wacce take son ya aura.
"Don ƙaniyarki uwar wa kike so ya aura? Kin kashe masa mata so kike ya ƙare da rayuwar sa a haka?" Mommy ta furta cikin zafi tare da jefa mata filet.
Da sauri ta fice fakon ganin za ta illata ta.
"Ba zan iya auren wata 'ya mace ba, don haka ki janye maganar matukar ba so kike na aikata abin da zai kawo miki matsala da iyayenta ba." Ya karashe maganar tare da kwashe tarkacensa zai fice.
Ganin haka ta miƙe tana faɗin,"Dole za ka auri yarinyar nan, a matsayina na mahaifiyarka na yi maka umurni da ka je ku sasanta kanku."
"No, Mommy, impossible!"Ya ce tare da ƙarashe ficewa.
Mommy ranta ya ɓaci ji ta yi kamar ta rufe shi da duka. Faɗa sosai take yi Muhsin yana ba ta hakuri. Ganin yadda shi kansa ta rufe shi da faɗa, kamar shi ya aikata laifin, sai Marwana ta shige cikin ɗakinta. Safa da Marwa take yi tana tunanin mafita.
"Ina wallahi Ya Damir, ba zai aure ta ba, saboda akwai macen da ta fi dacewa da shi." Ta furta tana zagaye ɗakin.
Damir kuwa cikin tsananin tashin hankali ya isa cikin motarsa ya fige ta. Yana zuwa ofis ya shige ya kulle kansa."Ba zan iya auren wata bayan ita ba, mai ya sa Mommy take son sanya ni cikin damuwa?" Ya ce cikin damuwa yana kai wa bango naushi.
"No, Batula kar ki damu alƙawarin da na yi miki zan cika shi." Ya ce tare da ɗaukar fayal yana dubawa. Ganin ba ya fahimtar komai, sai ya ije kawai ya jingina da kujerar da yake zaune yana tunani.
Muhsin ya yi sallama ya shigo. Jin muryarsa ya amsa ba tare da ya buɗe idanunsa ba.
"Please Yaya ina son magana da kai."
"Then go ahead." Ya ce masa yana duba takaddun da ya shigo da shi.
"Kan maganar da Mommy ta gaya maka, You need to do something. Dole ka yi aure saboda ni kaina ina jiran ka yi sai n.."
"Na hana ka ne? Kana gani matata na rasa, amma shi ne take gaya mini ta zaɓa mini mata."
"Saboda kana buƙatar aure sannan little Marwana tana buƙatar."
"No, we are ok, I can take all the responsibility of her."
"No Yaya kana buƙatar wasu yara..."
"Please, Muhsin go don't provoke me." Ya ce tare da ɗaga masa hannu.
"You need to sleep on it." Ya ce sannan ya fice daga cikin ofis ɗin.
Tsaki ya yi tare da miƙewa yana zagaye cikin ofis ɗin. Wayarsa ta yi ƙara alamun shigowar tsako, da sauri ya duba. Ganin Mommy ce take jaddada masa kar ya sake ya dawo ba tare da ya je ba, sai jikinsa ya yi sanyi.
Wata dubara ta faɗo masa tun da ba zai iya ƙin bin umurninta ba.
Sai da ya kammala aiki sannan ya tafi gidan. Tun a hanya ya canza fuskarsa ya haɗe rai. Da ya yi hon maigadi ya buɗe masa ya shiga.
Shufa'a cikin kwarkwasa ta ƙaraso girinsa tana jin kamar za ta sume, wai yau ita Damir zai aura.
"Barka da zuwa." Ta ce masa tare da ƙarasawa gurin da ya faka motarsa ya ƙi fitowa.