← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 92

Sashe 50

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To Allah dai ya sa haka, amma da za ta kira."Mama ta ce gaban ta yana faɗi.

"Bari na zo zan kira su Khausar."

"Da kin kira su ba sai kin zo ba, saboda har yanxu garin cida ake yi ga kuma hadari."

"Bari na kira su to."

"Allah dai ya sanya lafiya." Ta ce mata tare da kashe wayar.

Marwana Khausar ta kira, amma sai ta ce mata."Wallahi ban zo da motata ba, kuma na ɗauka da Ingawa za su tafi."

Kashewa ta yi ta kira Hajar, ita ba ma tare suka dawo ba. Wayar Nasreen ta ci gaba da kira amma a kashe

Tana ƙoƙarin ƙara kiran wayar kiran Mama ya shigo. Cikin sauri ta ɗauka saboda ta fara shiga damuwa."Mama duk sun ce ba tare suka tafi ba, amma in sha Allahu tana lafiya, bari na sanya a tura mini numbar Ingawa."

Jikinta ya yi sanyi, damuwa ya ƙara kamata jin abin da ta ce. Kashe wayar ta yi, sannan Marwana ta kira Ingawa. Bayan ya amsa da sallama ta yi masa bayani.

Jin abin da ta ce sai hankalinsa ya tashi."Ban jin daɗi yau ban je aiki ba. Mun dai yi waya da ita da safe, saboda mura ban ƙara kiranta ba."

"A'a subuhanallahi!" Ta furta bayan ta yi masa sallama ta kashe wayar.

Ɗakinta fito da makullin mota Mommy ta kalle ta.'Ina za ki je da daddaren nan?"

"Mommy Maman Nasreen ta kira ni wai ba ta dawo gurin aiki ba."

"Lafiya to?"

"Wallahi ban sani ba shi ne zan je na gani." Ta ƙarashe maganar tana kallon Damir da hankalinsa yake tibi ko kallon inda take bai yi ba.

"Ma za ki je to Allah ya sa lafiya."

"Amin," Ta amsa tare da ficewa hankalinta a tashe.

Mama bayan ta kashe wata cikin damuwa tana zagaye ɗakin. Har ta kai kofa don ta gaya wa Baba, sai kira ya shigo wayarta da sabuwar numba.

Tsayawa ta yi jikinta na kyarma ta ɗauki wayar. Tana fatan Nasreen ce.

"Assalamu alaikum." Ta yi sallama bayan ta amsa kiran.

"Wassalamu alaiki Mama Nasreen ce."

"Lafiya kina ina hankalinmu ya tashi."

"Mama ina asibiti na samu tsaguwar ƙashi faɗuwa na yi."

"Subuhanallahi! Wane asibiti na zo da Yusuf ko Musa?"

Gaya mata ta yi bayan ta sanar mata zo mata da kaya.

Hankalinta ya kwanta jin inda take. Hijabinta da ta yi sallah ta ɗauka, sannan ta shiga cikin ɗaki don ta ɗauko mata kayan.

Tunawa ta yi da Marwana, da sauri ta ɗauki wayar ta sanar mata da inda take, sannan ta koma ciki don ta haɗa mata kayan.

Cikin sanyi yake tuƙa motar, tamkar ba ya son ya karasa inda yake son zuwa. Zaune yake a cikin motar yana tuƙi cikin ƙwarewa. Idanunsa sanye da farin tabarau da ya ƙawata fuskarsa. Yana cikin shiga ta alfarma. Layin gidansu ya shigo, zuciyarsa na bugawa yana tunanin halin da zai cidda su. Iya lokacin daya ɗauka ba tare da ya gansu ba ya sanya zuciyarsa bugu.

Can nesa da kofar gidan, ya faka motarsa yana tunanin fitowa daga ciki. Kusan yan sakanni ya kwashe yana zaune a ciki ba tare da ya motsa ba, sannan ya yi namijin ƙoƙari ya fito tare da zare gilashin idanunsa, yana kallon unguwar cikin yanayi na kewa. Siraren hawaye suka sauka a kan fuskarsa, tuna irin rayuwar da ya yi a baya.

A hankali ya fara taku zuwa cikin gidan, zuciyarsa tana bugawa na tunanin halin da zai riski mutanen, da ya sadaukar da rayuwarsa saboda su.

A hankali ya yi siririyar sallama, ya buɗe ɗakin Mama yana kallon ɗakin cikin mamaki ganin wasu canje-canje.

Zainab da ta ji muryar da sauri ta ɗago kanta don ta tabbatar. Idanu ta zare taba nuna shi da yatsa, amma ta kasa magana kamar wacce ciwon kurumta ya kamata lokaci guda. Sai da ta ɗauki 'yan daƙiƙa sannan ta takura iya ƙarfinta ta ƙwala ƙara.

Mama na ƙoƙarin buɗe akwatin Nasreen, ta ji razanannen karan tare da kiran sunanta.

Ƙarar ya gigita ta ta fito a gigice tana faɗin,"Zainab lafiya?"

Ganin Zainab tsaye, numfashinta yana son ya shiɗe tana nuna mata mutum, sai kawai ta bi gurin da kallo tana mamakin wane ne.

Mutumin da ta cire rai da ganinsa. Wanda take masa addu'ar samun rahma a makwancinsa. Mutumin da ta rayu saboda shi, take jin rayuwarta da nasarar ta sun jingina gareta. Mutumin da ta haife shi, amma dai ya zame mata gurbin uba da uwa. Mutumin da adalilin da ta samu hasken rayuwa. Ta haife shi da kanta, amma sai ya zame mata fitila mai haskaka rayuwarta. Ya zamo bango abin jingina da tubali mai kyawu. Mutumin da ta cire rai da ganinsa yau ga shi a tsaye gareta. Cikin shiga ta alfarma, ya zama mutum nagartacce. Ya zama wayyaye mai arziki.

Jikinta ya kama rawa, domin ta ɗauka gizo da yake mata ko famarkin da ta sha yi ne zai dawo mata kamar haka take yi.

Baki ta buɗe za ta yi magana, amma sai ta kasa. Hannu ta ɗaga tana nuna sa da yatsa."Ahmad kai ne ko idanuna ke mini gizon ka?" Ta furta tambayar cikin tsananin mamaki.

"Ni ne Mama, nine ɗanki da yake jin ranshi fansa ne a gareki da Nasreen. Yau na dawo gareku zan zame muku bango abin jingina. Daga yau babu wanda zai ƙara nuna muku don yatsa. Zan tsaya na kula da rayuwarmu, na ba ku irin jin daɗin da na ke fatan samar muku."

Mama sai kawai ta zube luuu kasa ta sume. Da sauri ya yi mata yana kiran sunanta. Kafin kace me gida ya rikice kowa ihu yake ana murna. Masu sume-sume suna ta yi Ahmad ya dawo. Babban abin da ya fi murna, wata irin ƙatuwar mota mai kama da jirgi ya zo da ita. Sannan ya zama ɗan gayu ya yi ƙiba ya ƙara girma. Kowa kallonsa yake yi, yana mamakin canzawarsa. Sai shafa jikinsa suke yi suna ihun murna.

A ƙalla Mama sai da ta yi suma uku, domin abu ne tun tana sakarai har ta fara sarewa. A na ƙarshen ya rungume ta yana kuka."Mama don Allah kar ki ƙara suma walllahi nine na dawo gareki, na san na yi kuskure na nisanta kaina da na yi damu, amma a wannan lokacin hakan shi ne kawai mafita a gareni."

"Ahmad ka bar ni na ci gaba da suma don na ci gaba da ganinka, bana son na dawo daidai ace mini mafarkin da na ke yi ne " Ta kamashi tana kuka tana girgiza shi.

"Ba zan taba barin ki ba Mama na dawo gare ki ina Nasreen? Yanzu ne zan tsaya na yi fito na fito da Faruk. Nasreen za ta bar gidan Faruk ayau zan sanyata a cikin farinciki. Zan tsaya a rayuwarta na yi fito- na fito da Baba har sai ta samu miji na gari.

"Labari mai tsawo Nasreen ta bar gidan Faruk sun rabu ai." Wani irin farinciki ya kama shi jin abin da ta ce.

"Da gaske kike Gwaggo?"

"Eh Nasreen ta bar gidansa mugun azzalumi. Rayuwarta ta canza duk adalilin wannan yarinyar 'yar albarka Marwana. Yanzu haka tana aiki a kamfanin su. Ka duba rayuwarmu ya canza duk a dalilinta."

Hawaye ta ga yana yi tare da kabbara. Mama ta kama shi ta ce,"Mu je ɗaki na ɗauko kaya zan kai mata tana asibiti ta faɗi ta goce."

Zare idanunsa ya yi, sai ya kamata hannunta suka ɗauko kayan. "Mu yi sauri Mama na kai ki a motata." Ya ce tare da ƙarasawa gurin motar.

Shafa idanunta ta yi sai ko mafarki take yi."Ahmad, satan mutane ko garkuwa da mutane ka yi ka siya wannan motar mai kama da jirgi?" Ta yi masa tambayar cikin tsanannin tashin hankali.

"Allah Ubangiji ya tsare ni da haka. Mu je na halin da take ciki zan yi miki bayani saboda labarin mai tsawo ne." Da kyar ya samu ta shiga cikin motar tana zare ido.

Har suka isa cikin asibitin hawaye take sharewa. Suna isa ya fito da sauri ya kama hannun ta suka shiga. Burinsa ya yi toxali da yar ƙanwansa da ya yi mata laifi.

Suna shiga ɗakin Mama ta hango ta, tana zaune tana dage da hannun a lokacin aka gama gyarawa. Da sauri Mama ta ƙarasa gunta."Kin ga tsautsayi sannu ya hannun?"

"Da sauki."Ta furta tana cige baki."

"Na zo miki da wani albishiri Nasreen." Ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushin da rabon ta ganshi a fuskarta tun ranar da Ahmad ya ɓata

Xuciyarta ta buga haka kawai ta ji faɗuwar gaba."Mama mai ya faru?"

"Kalli can." Ta nuna mata Ahmad dake tsaye, yana rungume da hannunsa, yana kallonta cikin tsanannin mamaki ganin yadda ta canza ta yi kyau ta zama 'yar gayu.

"Ya Ahm..." Ta kwala ƙara har sai da asibitin ya ɗauka tana nuna shi da yatsa

Abin da bata taɓa tunanin ganinsa a wannan rana ba. Xuciyarta cike yake da damuwar abin da Damir ya yi mata, amma kuma ya Allah ya share mata hawaye ta. Ya dawo mata da mutumin da ta ke gani a matsayin uba, uwa shi ne rayuwaarta gabakiɗaya. Mutumin da ya tsaya mata ya yi yaki da duk wanda ya zalince ta. Ya ga shi a gabanta yana kallonta ya canza ya samu kyakkyawar rayuwa

"Mama ki mare ni na gane ko mafarkin da na saba ne. Don Allah ku yi ta dukana har sai na farka in mafarki na ke yi." Ta furta tana hawaye

"Ba mafarki kike yi ba Ahmad ne dan'uwanki a gabanki."

Sai kawai ta faɗi ƙasa ta sume ganin haka suka yi kanta. Da ta farfaɗo kuka take yi tana faɗin,

"Wayyo Allahna na gode maka da ka dawo mana da farincikin rayuwata."

Ganin tana son miƙewa sai ya rungumeta. Kuka take yi sosai tana ƙara rungume shi."Ya Ahmad ina ka tafi ka bar ni da kewarka? Kasan halin da na kasance a lokacin da na rasa ka? Kasan damuwar da na shiga. Yaya Ahmad duniya ta yi mini ƙunci rayuwata ta munanta. Na shiga kunci da tashin hankali na rashinka. Don Allah kar ka ƙara guduwa ka barni."

"Is ok ƙanwata na dawo gareki kuma ba zan ƙara gudun ki ba."
Chapter 50 · 0% Book details