Sashe 31
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Marwana sai da ta gama hutun gajiya sannan ta shirya don ta je makaranta. Tafiya take cikin farin ciki tana tunanin rayuwar da ta yi da ƙawayenta musamman su Nasreen, yau ga shi ƙaddara ta sanya duk sun gama, amma ita sai wanann shekarar za ta gama. Ba ta manta ranar da wasu ƙawayenta suka yi posting hotonsu da kayan copper har sai da ta yi kuka, amma babu komai za ta ɗauki hakan a matsayin ƙaddarar rayuwar ta in har Nasreen tana cikin farinciki.
Bayan ta isa makarantar ta kashe motarta tare da fitowa ta kulle ta. Sai da ta gama lecture sannan ta fito daga cikin makarantar.
Tana ƙoƙarin shiga cikin mota ta ji an ƙwala mata kira. Da sauri ta waiga tare da zare gilas ɗin idanunta."Asmy, ke ce ko idona gizo yake mini?"
"Ni ce mana ko na canza kama ne? Ke ya kamata na yi mamakin ganinki saboda na san kina waje."
"Wallahi sati ɗaya da dawowarmu ya service?" Ta ce mata tare da kama hannunta ya riƙe.
Barka da sallah fans ɗina ina yi muku Barka da sallah tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. Sai na zo muku yawon sallah. Tamu Jamila lawal Zango Jamsy❤️❤️❤️❤️❤️🙏🙏🙏💃💃 Nasreen, Damir, Marwana, har ma da Faruk capacity yana muku barka da sallah.
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 16

"Hmmmmh! Ki bar tuna mini abin haushi kar kisa na ɗorawa lecturer Tukur zagi, kin san ɗan Iskan malamin nan, sai a semester na ƙarshe ya bani spill ov..."
Kafin ta ƙarashe ta saki salati tana faɗin,"Yanzu duk ƙoƙarin ki Asmy? Amma bai kyauta miki ba."
"Wallahi na yi kuka da zaginsa yafi sau nawa."
"Ki yi haƙuri rabon zamu ƙara ganin juna ne."
"Haka ne wallahi dana ganki dai na ji makarantar ta yi mini daɗi."
"Dariya ta yi tare da rungume ta."Wallahi I couldn't forgot those day memorable kenan."
"Sosai wallahi don ma kin haɗu da Nasreen sai kika share mu."
Gabanta ya faɗi jin abin da ta ce,"Allah Sarki, Nasreen ai kamar 'yar'uwa na ɗauke ta sai ga shi ƙaddara ta raba zumuncinmu."
"Sosai lamarin bai yi daɗi ba. Ina Ya Damir amma yanzu ya manta komai?"
"Sosai ya dawo kamar da dama zafin mutuwa ce."
"Wallahi ai yana ƙaunar matarsa sosai kowa ya sani."
"Haka ne Allah ya saka masa ya jiƙanta."
"Amin," Ta ce tare da kallonta ta furta,"Kamar kin gama lecture ko zan fita dake ne?"
"Da kin kyauta wallahi saboda na gaji." Jin abin da ta ce sai ta fara tafiya zuwa motar ta suna hira.
Sun shiga cikin motar ta fara tuƙawa. Waiwawoya ta yi ta kalle ta."Na san cewa Nasreen tana cikin farinciki, Ƴaƴanta Ahmad ya raba aurenta da ɗan iskan mijinta Faruk. Wataƙila lokacin ku kammala makaranta ta canza ta yi ƙiba?"
"Allah Sarki ba ki da labarin abin da ya faru?"
Cikin razana ta yi ƙoƙarin taka burki tana kallonta.Mai ya faru?"
"Ai ba ta rabu da Faruk ba har muka gama makaranta."
Tsananin mamaki ya kamata jin abin da ta ce."Saboda me bayan na mu bar ƙasar ya ce zai yi masa hulɗi."
"Hmmm! Bayan tafiyarku aka ne ni Ahmad aka rasa har muka kammala karatu bai dawo ba, wannan dalilin mahaifin ta ya tilasta mata ko....."
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta fira sai kawai ta fashe da kuka.
"Ban gane an nemi Ya Ahmad an rasa ba? Kina nufin live bayan tafiyarmu ba a ga Ya Ahmad ba?" Yadda ta fita hayyacinta, tana kuka tana tambayarta ya sanya ta yi dana-sanin gaya mata.
"Don Allah Marwana ki faka motar nan, sai na yi miki bayani karki kashe mu." Ta furta cikin tana tana hawaye.
Da ƙyar ta yi nasarar gangara ta yi parking."Don Allah ki gaya mini da gaske Ya Ahmad ya ɓata?"
"Wallahi an neme shi an rasa kuma har muka gama karatu ba a gan shi ba, saboda har jaje muka je mata, domin ta yi kamar za ta zauce. Rashin ganinsa mahaifinta ya tilasta mata ta koma. Har muka kammala karatu Nasreen tana da aure, kuma kin ga ni ban je service ba, wataƙila da na gan..."
"Wayyo Allah! Haƙiƙa Nasreen kina ganin jarrabawa. Anya ba Faruk ya ɗauke shi ba? Domin ba abinda imani zai iya."
"Hakan zai iya yiwuwa saboda mutum mugun icce ne. Ni dai sauke ni anan zan ƙarasa, saboda ban shirya mutuwa ba." Ta ce tare da buɗe motar ta fita.
Tana fita ta kece da kuka sosai. Kuka take yi tana tunanin halin da take ciki na rashin Ahmad. Zuciyarta ta karaya da tausayinta, har ta ji ba za ta iya biyayya ga Mommy ba da ta yi mata tsakani da ita.
Ba tare da dogon tunani ba, ta fi motarta cikin tashi hankali zuwa gidan Faruk. "A wannaan karan Mommy ki yi haƙuri zan saba wa umurninki. Sai na cike gurbin Ya Ahmad. Zan tsaya mata na maka Faruk a kotu." Tafe take tana sumbatu kamar sabuwar kamu har ta isa get ɗin gidan.
A lokacin da ya isa sai ta yi parking a ƙofar gidan ta fito. Ta ɗan ɗauki lokaci tana tunanin ƙwakwansa gidan. Tsoro take ko Faruk zai fito ya yi mata tijara. Kusan 'yan sakanni ta ɓata tana tunani, kafin ta yi namijin ƙoƙarin ta fara buga get ɗin gidan.
A lokacin da ta ƙwankwasa Rashida ce a falo tana zaune tana kallo. Miƙewa ta yi ta je ƙofar gidan ta buɗe. Ganin mace 'yar gayu sai ta ba ta hanya ta shiga cikin gidan. Kallo Marwana ta yi mata tana ƙoƙarin danne dariyar da take sin kubce mata. Tuni ta raina abin Faruk ganin matar da ya aura. A tunaninta za ta girme shi ko su zo tsara.
"Mu shiga ciki." Ta ce mata duk da bata taɓa ganin ta. Babu musu ta bi bayanta har zuwa cikin ɗakin tana raba idanu.
"Baiwar Allah daga ina?" Ta ce mata ganin ta mayar da hankalinta cikin gidan, burunta ta yi idanu biyu da Nasreen ko yaranta.
"An sorry, Nasreen na zo nema Ummu Raihann."
Jin abin da ta ce sai ta ɓata fuska ta ce,"Yaushe rabon duniya da ayyaraye, hala kin yi tafiya ne?"
"Eh, mun fita waje ne."
Tana ƙoƙarin bata amsa sai kawai Faruk ya fito daga cikin ɗakinsa.
Ganinta ya sanya zare idanu yana kallonta. Yadda ya kalle ta a wulaƙance ya ce,"Uban me ya kawo ki gidan nan?"Ya tayar da hankalinta.
Miƙewa ta yi tana kallon sa,"Ba faɗa ya kawo ki ba, gurin Nasreen na zo."
"Gidan ubanki ne za ki shigo kai tsaye?"
"Ba zan ɗauki rashin mutunci ba duk da gidanka na zo." Ta ce tare da miƙewa ta rataya jakarta
"Fita daga gidan nan mara mutunci kin san yadda na tsane ki?"
"Farouk, ka santa ne?" Rashida ta yi mata tambayar ganin yadda ya harzuƙa.
"Ita ce ƙawar Nasreen wacce ta lalata mata rayuwa, ta mayar da ita mai ƙwaɗayi har ta raina ni. Ita ce wacce ta sanya ɗan iskan ƴaƴanta ya ba ta jini aka sanya wa matata da aurena."
Jin abin da ya ce sai ta ɓata fuska ta koma ta zauna."To kuma mene na damuwa bayan ka rabu da ita?" Ta ce masa cikin gatsali.
Marwana jin abin da ta ce ba ta san lokacin da ta saki murmushin farinckin ba."Alhamdulillah! Allah na gode maka da wannan azzalumin ya rabu da Nasreen." Ta ce cikin farin ciki.
Jin bin da ta faɗa sai ya harzuƙa ya yi kanta."Fitan mini a gida, tun kafin zuciyata ta sanya na kassaraki. Ki fita wallahi xan iya ɗaukar ranki."
"Zan fita saboda yanzu babu abin da zai ƙara haɗa ni da kai. Allah zan godewa da ya gabata da mugun miji kamarka, kuma sai ka yi dana-sanin ƙuntata mata da kayi."
Cikin tsananin ɓacin rai ya nufota yana kumfar baki. Ganin zai iya dukanta ya sanya ta fita da sauri." Da ki tsaya ki ga yadda zan illata ki."
Har ƙofar gida ya biyota yana zaginta da jawo mata alkaba'i iri-iri.
Marwana ba ta tanka masa ba ta fara ƙoƙarin shiga cikin motarta. Matuƙar farinciki take ji saboda ya sake ta.
Sai da ta bar ƙofar gidan sannan ya koma yana zaginta.
Har ta wuce gidan Maman Muwaddat sai kuma ta dawo ta tsaya, ganinta ta fito tana ƙoƙarin kulle gidan za ta fita.
Da sauri ta kashe motar ta fito so take ta tambaye ta, domin ta san cewa ba zata rasa sanin gidansu Nasreen ko labarin, inda take ba tun da maƙota suke.
"Ni fa kamar na sanki?" Maman Muwaddat ta ce tana ƙoƙarin son tuna inda ta santa.
"Ayya da wu..."
"Marwana." Ta furta tare da nuna ta da yatsa cikin tsananin farinciki.
Kallonta ta yi ta kasa cewa komai tana mamakin inda ta santa.
"Don Allah kece?" Ta yi mata tambayar kamar za ta shiɗe.
"Ni ce."
Jin abin da ta ce sai kawai ta rungumeta."Wallahi ita ce dole na gane ki, saboda Nasreen duk ta shigo cikin gidana sai ta nuna mini hotonki har kuka take yi."
"Allah Sarki," Ta furta tare da share hawayen da suka zubo mata sai kuka ta ce,"Sati ɗaya da dawowa daga waje, sai na je makaranta na haɗu da maye ɗina, na tambayeta Nasreen take gaya mini ba su rabu ba, saboda Ya Ahmad ya ɓace." Ta ƙarashe maganar cikin hawaye.