Sashe 4
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Da kyau Masha Allah! Ubangiji ya kawo kasuwa." Ta ce mata tana kallon ta.
"Ke ma ki fara sana'a tun kina gida na yanke shawarar san zo mu yi maganar. Zan rinƙa baki kan sari kina ɗora na ki. Idan Allah ya sanya kina da rabon sai ki ga Allah ya ɗaukaka ki. A waya za ki yi Faruk ba zai san kina business, sannan kina zuwa makaranta za ki yi ciniki."
Kallonta ta yi cikin farin ciki ta ce,"Gaskiya na gode sosai. Zan gwada Allah ya sa na samu, duk da na sayar da wayar na sayi ƙarama ba ta rike caji sosai, kuma makarantar ai na kusa gamawa."
"In har kika fara sana'a kwana nawa za ki canza. Kin san wani lokacin rayuwa tana cakuɗe wa mace ne, in ba ta da sana'a. In har kina da abin yi ɗin namiji yana wulakanta ki wallahi ba ki da lokacinsa. Abinci ne zai baki, kuma ya san ko bai baki ba, kina da abin da za ki siya. Ko da za ku samu matsala da sauki ba kamar ace kina zaune komai sai ya ba ki ba."
"Haka ne zan gwada in sha Allahu. Ni ma akwai sauran dubu hamsin da ban kashe ba, a cikin kuɗin lapton ɗina. Dama na ije na makaranta saboda biyan kudin makaranta, amma da zarar har mun kashe hamsin."
"Ki sai waya da shi Nasreen sai ki fara business. Akwai groups kala-kala na sana'a cikin ƙankanin lokaci in sha Allahu za ki samu kuɗin. Sannan ki rinƙa hawa social media kina karanta labari ɗan Whatsapp ɗin nan ki shiga groups groups za ki samu farin ciki, kuka ki san halin da duniya take ciki. Ga kuma marubuta suna ƙoƙarin su gurin sanya mutum nishadi har ma da darasi."
"In sha Allahu zan kira shi na ba shi kuɗin ya nemo mini. Facebook ɗin don tun da ya Ahmad ya ɓace ban ƙara shiga ba, Whatsapp ɗin kuwa ina ya yi expired."
"Zai yi tun da an daɗe." Ta ce mata tana kallonta.
"Miƙewa ta yi tana kallon agogo."Bari na tafi suna bacci na taho, kar ya tashi ya ga bana nan ya kira Baba."
"Ok, ki je kin san Baba da faɗa. Zan kira Musa in ya gama ɗinkin sai ya ƙara da wanda zan baki."
"To na gode Allah ya saka da alkhairi." Ta ce mata. Har bakin ƙofa ta rako ta sannan ta tafi.
Da ta koma har lokacin ba su tashi ba. Kicin ta wuce ta gyara sannan ta fito. Tana ƙoƙarin rufe kicin ɗin Rashida ta fito tana wani takun yanga ita a dole ta kwana da miji. Wucewa ta yi tana mata kallon ƙaskanci bisa abin da suka yi jiya. Za ta shige cikin ɗakinta Faruk ya fito da alamu ya shirya zai fita.
Kanta ta ɗauke ganin yana kallon tsabar idanunta ya ga ko za ta ji haushi, amma sai ya ga saɓanin haka. Har za ta wuce sai kuma ta ga in ba ta gaishe shi ba, zai yi tunanin ta ji haushin ƙin kwana ɗakinta da ya yi.
"Ina kwana." Ta ce masa ba tare da ta jira amsar ba ta shige cikin ɗakinta.
Ƙuta ya yi yana kallon hanyar ɗakinta."Wato kin dawo da raini. Ni kike gaishewa kamar kina gaida sa'an ki?" Ya ce cikin ɓacin rai.
Yana tsaye yana yana gyara zaman takalmin da Rashida ta fito ranta a ɓaci."Baby, dankali na ga an siya da wani barbaɗaɗɗen kwai, aka sanya a kula?"
"Da kular kike so ya cika. Guda biyu na siyo in aka sanya kayan miya yawa yake yi sosai. Ita Nasreen ta san yadda take yi ai." Ya ce mata yana gyara takalmin da ba tare da ya ɗago ya kalleta ba da take jin kamar ta kifa masa mari.
*_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 3
"Da kular kike so ya cika. Guda biyu na siyo in aka sanya kayan miya yawa yake yi sosai. Ita Nasreen ta san yadda take yi ai." Ya ce mata yana gyara takalminsa, ba tare da ya ɗago ya kalleta ba da take jin kamar ta kifa masa mari.
"Kwai biyu duk mutanen gidanan? Shi ya sa na ga ko kama kayan miyan baya yi. Haba don Allah ace rai kusan biyar su karya da ƙwai biyu? Ni fa wallahi na gaji da maƙon ka, kana da shi Allah ya buɗa maka, amma ba za ka wadata iyalinka ba. Haka fa ranar nan ka siyo ƙullu na sayarwa Faruk da matsayin ka kana babba a gwamnati? Wannan zaluncin ya yi yawa."
Miƙewa ya yi a fusace yana kallonta."Ok, so kike na zauna na siyo crek ɗaya sai ku soye a lokacin, tun da kina auren ɗangwate ko Aliko ko? Don ina aikin gwamnati sai na dinga watsa muku kuɗina. Ba ki da hankali ya kamata ki dawo hayyacinki, saboda ni Faruk ba mahaukaci bane, na san yadda na tara kuɗina. To ki sani a gidana cimar da na ga dama ita zan bayar, kuma babu wanda ya isa ya sanya na canza mini ra'ayi. Yauma mai da ya ji zan bayar ku dafa, sannan wallahi ki daina zuba mai da yawa, don in ya ƙare sai dai ku siya da kuɗin ku, sisina ba zan bayar ba." Ya ƙarashe maganar yana nuna ta da yatsa sai kuma ya ce,"Na manta ba ke za ki yi girkin ba, ita wacce za ta girka ta san dokar gidan."
"Kan uban nan!" Rashida ta lailayo ashar ta ƙunduma.
"Ke zagina za ki yi?" Ya yi mata tambayar tare da ɗaga hannunsa.
"No Faruk! Ba zan iya daukar cimar gidan ka ba, wallahi in har kana son zama da ni dole ka canza. Kana ba matanka abinci kamar kana ciyar da 'yan gidan yari?"
"Guri kika samu, saboda ba ki zo lokacin da na ke bawa Nasreen abinci sau ɗaya ta girka ba, don kin ga ina bari ki yi girki duk lokacin da kike so. To ki yi gigin da zan hana girki a gidan nan, sai na dawo daga gurin yawona."
"Ka isa wallahi ba ka isa ba, saboda ba dabbobi ka ije ba, da za ka rinƙa ciyar da su lokacin da ka ga dama."
"Tun da haka kika ce sai mu zuba in na fara idonki zai raina fata."
Gabansa ta sha ganin zai fita."Ba zan taɓa yin irin wannan rayuwar ba, dole ka canza ko mu hau sama da kai. Idan matarka ba ta san darajar kanta ba, ta bari kana mata abin da ka ga dama wallahi ba zan ɗauka ba, zaman aure ba zaman bauta bane."
"Ok haka kika ce?"
"Eh Faruk fiye da hakan zan faɗa." Ta furta tana kama ƙugu.
"To shege ka fasa."Ya tureta ya fice daga falon.
Nasreen dake cikin ɗauki ta tana zaune tana jin sa'insar da suke yi. Dariya ta saki tana faɗin,"Daɗina da gobe saurin zuwa."
Rashida kuwa cikin takaici ta tura ƙofar ɗakin Nasreen ta shigo. Ganinta ya sanya ta miƙe tana kallonta. Ganinta ya sanya ta ɗan razana, amma sai ta daure ta ce,"Lafiya kika shigo mini ɗaki babu sallama, kamar ba ki san hukuncin yin sallama ba?"
"Eh saboda ba ita ta kawo ni ba. Na shigo na gaya miki tarbiyar da kika ɗora mijinki sam ba ki yi masa tarbiyar kirki ba, kin koya masa maƙo kin zauna kin zubar da kanki, yana da kuɗi yana baki cimar talakawa."
Jin bin da ta ce sai ta ba ta dariya sosai."Ok, kena kina da believe cewar uwargida take ɗora mijinta kenan? Ba zan yi miki musu ba, amma ba irin mijin da kika aura ba. Faruk yana cikin WASU MAZAN da mace ba ta isa ta sanya shi ba kuma ta juya shi. Faruk yana cikin WASU MAZAN da ba su ɗauki mace a bakin komai ba, abin da suka gama shi suke yi. Idan ya je ya gama gaya miki ƙarya da gaskiya cewar bana masa biyayya ni ba macen ƙwarai bace, kin shigo da ninyar ƙwace zuciyarsa ta hanyar yi masa jin da bana yi, sai na ce alhamdulillah ga fili ga mai doki sai sukuwa."
"Ai wallahi ba zan ɗauka ba, saboda na san daraja ba zan yarda ya rinƙa ciyar da mu, kamar yana cutar da bursunoni ba."
"Allah ya ba ki sa'a sai ki gyara shi yadda kike so, tun da ni uwargida ban ɗora shi a kan turbar ƙwarai ba."
Ta buɗe baki za ta yi magana, amma sai takaici ya sa ta kasa cewa komai. Cikin fushi ta fice tare da buga kofa.
Nasreen ta sanyawa ƙofarta makulli tana faɗin,"Shashashar banza! Suna zuwa suna gaya muku ƙarya da gaskiya kuna yarda. Yanzu sai na ga abin da za ki iya." Ta koma ta kwanta. Wayarta ta ɗauka ta kira ƙaninta Bala, ta yi masa bayanin tan sun canza wayarta.
Babu ɓata lokaci ya zo get ɗin gidan ya kira ta ta fita. Wayar ta ba shi sannan ta cika masa dubu arba'in. Tana kwance a dakinta kasancewar hutu ake yi na makaranta girki kawai ta yi sannan ta ɗauki Raihan. Tana cikin ɗaki suka wunin binsu.
Bayan magariba Bala ya kawo mata waya mai kyau. Ta yi murnar wayar da ya canza mata, don ta yi mata kyau Infinix hot eleven play.
"Allah ya sanya ka sanya mini caji?" Ta ce tana kallon sa.
"Haba Anty Nasreen, sai da na cika ta sannan na gwadata har layinki na sanya miki. Za ki ji dadin wayar tana riƙe caji."
"To ka shigo gidan na ba ka ko na mota."