Sashe 38
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Why? Marwana za ta zaɓi ta kawo ta cikin kampanin nan, why za ta zaɓi ta yi hurting ɗina bayan duk soyayyar da na sadaukar mata."
"Ka yi hakuri Please take easy." Ya ce masa cikin rarrashi.
Shiru kawai ya yi yana ganin Marwana ba ta yi masa adalci ba
Nasreen sai da ta tabbatar da ta fita daga cikin campany sai ta tsaya ta fashe da kuka."Mai ya sa Marwana za ki yi mini haka?" Wayarta ta ciro cikin ɓacin rai tana ƙoƙarin kiranta, amma sai ta ta j tana mata hon a bayanta.
Marwana da tun da ta shiga ta dawo ta tsaya a cikin motar. Jira take yi ta fito ta gaya mata su ɗauke ta aiki ganin ta fito cikin kuka ya sanya ta ruɗe.
"Saboda me za ki buƙaci na je kampanin mu na yi aiki? Bayan kin san Ya Damir ya tsane ni? Ya riƙi na yi nesa da shi, amma yau na tayar masa da mikin da yake ƙoƙarin warkewa?"
"Ki fahimce ni do.." Ta ce tare da ƙarasowa gurinta ta kama hanunnta.
Fisgewa ta yi tana faɗin,"In har ba kina son ɗan'uwanki ya ɗauki fansar abin da na yi masa ba, to ki janye maganar yin aikina a campanininku." Ta karashe maganar tana share hawaye.
Hankalin ta ya tashi sosai ganin duk rarrashin da take mata, tana son ta fahimce ta, amma ta ƙi saurarenta. Daga bisani sai kawai ta fara tafiya cikin sauri.
Ganin haka ya sanya ta sha gabanta."Don Allah koma ayi miki interview, wallahi na kawo ki aiki a nan don ki tallafawa rayuwarku."
"Bana so ki bar taimakon bana buƙata, saboda idanuwana ba za su iya ganin Ya Damir ba. Shi ne mutumin da na ke jin kunyarsa matuƙar gaske. Idanuwana ba za su iya haɗa ido da na shi ba, da suke nuna mini tsantsar zalintarsa da na yi. A duk lokacin da na kalle shi sai naga tsantsar nadamar haɗuwa da ni a idanunsa."
Kanta ya kulle sosai ta rasa abin da za ta ce." Ok, na fahimci ki shiga in kaiki gida Please." Ta ce cikin marairaicewa.
Ganin yadda ta yi ya sanya ta shiga babu musu. A cikin motar shiru suka yi kowa da abin da yake tsaƙawa a cikin ransa. Nasreen rintsa idanunta ta yi tana jin kamar a lokacin lamarin ya faru. Ganinsa ya tayar mata da mijin da Faruk ya yi mata.
Da suka isa ƙofar gidan fita ta yi daga cikin motar."Na gode da taimakon ki, amma ba zan iya aiki a campany ba." Ta ce tare da rufe motar ta shiga gida.
Kallonta ta yi ba ta ce komai ba har ta shige. Ajiyar zuciya ta yi sannan ta tayar da motar zuciyarta cike da damuwa.
Nasreen kuwa gida ta shige tana mamakin dalilin da zai sanya ta buƙaci ta je kampaninsu aiki. Ganinsa yai sai ta ji wani iri. A wancan haɗuwarsu ta farko da take da auren Faruk a kanta, ta yi masa kallon irin abin da kake fatan samu sai ka rasa, amma a yau da ta gansa. Duk da tsantsar tsanar da take hangowa a cikin zuciyarsa sai ta ji wani irin yanayi daban da ranar haɗuwarsu. Yanayin da ta kasa ta ta ce wani irin yanayi ne.
Cikin ɗakinta shiga daidai lokacin da hawaye suka ƙara wanke mata fuska. Sallamar da ta yi, cikin muryar kuka ya tsoratar da hankalin Mama da take zaune tana gyara wake.
Ba tare da ta amsa sallamar ba ta miƙe tana faɗin,"Lafiya Nasreen?"
Kuka ta fashe da shi ta faɗa jikinta."Ban san dalilin da ya sanya Marwana ta zaɓi na je kampanin su na yi aiki ba, ba zan yi mata mummunar fahimta ba, amma da sai na yi tunanin tana son yayanta ya ɗauki fansar abin da na yi masa ne."
"Kul! Karki sake ki zargi haka Marwana yarinyar kirki ce, wacce a kodayaushe take son faranta miki. Akwai dalilin ta na aikata hakan, ki yi mata uzuri ki fahimce ta."
Miƙewa ta yi tare da janye Musaddik a kan jikinta."Ko ma mene ba zan iya aikin ba, zan gaya mata gaskiya, saboda bana fatan abin da zai ƙara haɗa ni da shi."
"Allah dai ya zaba abu da yafi alkhairi." Ta cikin damuwa.
Marwan da ta koma gida kai tsaye ɗakin Mommy ta shige. Ganin ta ranta a ɓaci ya sanya ta kalle ta."Lafiya Marwana?"
Tambayar da ta yi mata ya sanya ta fashe da kuka."Dama na san cewa ba ni da matsayin da zan iya kawo ma'aikaciya a kampanin. Na kai Nasreen amma da Ya Damir da Ya Muhsin sun haɗu sun yi mata rashin mutunci, kuma wallahi in har ina da gado a campanin dole sa sun ɗauke ta."
Kamata ta yi tana rarrashi."Dama abin da yake zuciyarsu kenan? Shi ya sanya suka ce sai sun yi mata interview? Ki bar ni da su dole su ɗauke ta."
Jin abin da ta ce ya sanya ta saki murmushi tare da share hawayenta. Saboda rigima sai da ta daidaici lokacin da za su dawo ta zauna a falo.
A lokacin da ta ji alamun buɗe get sun shigo da mota. Ƙara tamke fuska tayi tana kallon bakin ƙofa. Muhsin ne ya fara shigowa da suit ɗinsa a hannunsa yana ƙoƙarin cire neck tie ɗinsa, Damir kuma yana bayansa waya yake yi.
Yana shigowa ta banka masa harara tare da shan gabansa."Saboda me za ku ƙi ɗaukar ta aiki?" Ta ce fuskarta babu tsoro.
"Ke! Matsa kafin yanzu na wanka miki mari ina wasa dake ne?" Muhsin ta ce cikin fusata.
"Ba zan matsa ba har sai na ji dalilin.." Da sauri ta matsa tare da kiran Mommy da ƙarfi ganin ya ɗaga hannunsa.
"Mara kunya da ki tsaya ki ga yadda zan ɓata miki fuska da mari."
Har yanzu dai ana nan ana posting a paid group mai kuke tunani? Nasreen za ta amince ta yi aikin sannan ya za ta kasance tsakaninsu da Damir?
In ana son na ci gaba da posting safe da yamma sai na ga ruwan comments.
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 20
A lokacin da ta ji alamun buɗe get sun shigo da mota. Ƙara tamke fuska tayi tana kallon bakin ƙofa. Muhsin ne ya fara shigowa da suit ɗinsa, a hannunsa yana ƙoƙarin cire neck tie ɗinsa, Damir kuma yana bayansa waya yake yi.

"Ke! Matsa kafin yanzu na wanka miki mari ina wasa dake ne?" Muhsin ya ce cikin fusata.

"Mara kunya da ki tsaya, ki ga yadda zan ɓata miki fuska da mari."
Mommy ce ta ƙara so cikin falon tana faɗin,"Dole za su ɗauke ta, ko da ace ba su yi mata interview ba."
"Dama babu abin da muka yi mata, rashin dacewar ta a gurin ya sanya ta kori kanta." Muhsin ya ce tare da zama a falon.
"In har ina da iko daku ku ɗauke ta." Mommy ta furta tare da shigewa ciki.
Damir da ya ji tana maganar daidai lokacin da ya gama wayar, ya sanya a cikin aljihunsa zai shigo. Kallo ya bi ta da shi, saboda ba ya son ya yi magana, tun da ya ganta mood ɗinsa ya canza damuwa ta yi masa yawa.
Raka shi da idanu suka yi har ya haye sama."Ki je ki kai masa abincinsa." Mommy ta ce wa Marwana tare da shiga ɗakinta.
Ganin haka shi ma ya yi hanyar na sa ɗakin. Bayan ta gama haɗa abincin, ta shiga cikin ɗakin na sa. Yana kwance ya yi rigingine yana tunani.
Sunan shi ta kira, amma bai ji ba ganin haka ta ƙarasa ta sauke abincin."Yaya.." Ta furta tare da janye hannunta ganin yadda ya ɗan firgita alamun bai san ta shigo ba.
"Ya..."
"Fita ba kin sanya dole a bata aiki ba? Fita ki ba ni guri." Ya daka mata tsada yana faɗin haka..
Kafin ya rufe bakinta fice da sauri cikin ɗakin. Tsaki ya yi tare da miƙewa ya shiga toilet.
Wanka ya yi, sannan ya saka gajeren wando da riga ya zauna a gefen gadonsa. Wayarsa ya ɗauka tare da kunna hoton Batula yana kallo.
Washegari da safe Marwana ta shirya don ta je ta kai ta gurin aiki. Da ta shiga gidan da sallama. Turus ta yi tana kallonta da take kan turmi tana gyarawa Musaddik wandonsa.
Tamkar babu abin da ya haɗa su ta miƙe."Musaddik, Anty Marwana." Ta ce masa tana nuna masa ita.
Da sauri ya ruga ta ɗauke shi tana murna. Sai dariya yake mata, saboda ya saba da ita.
"Lafiya na ganki babu shiri aiki, kuma ba ki ga misscalls ɗina ba?"
"Wayar tana kan kujerar na barta, na gaya miki ba zan yi aikin nan ba."
"Dole ki yi kina buƙatar aikin nan, in don Ya Damir ne ba za ki rinƙa haɗuwa da shi ba, wannan ranar ma kuskure ne, saboda bai san za ki so ba, amma in har ya san kina kampanin zai yi ƙoƙarin ba ku haɗu ba."
Kallonta cikin mamaki ta yi,"Saboda ne zan takura masa haka? In har kina don na yi aiki, to don Allah ki nema mini amma ba a kampanin ku ba."
"Za ki yi dole za ki yi don cigaban ki." Ta furta tare da ƙara da wa gurin Mama da ta shigo.