← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 92

Sashe 54

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da dadddare, ko da muka zo kwanciya hak ya rinƙa gaya mini tashin hankalin da zan fuskanta, sannan ya yi ta roƙona na koma gida don kar iyayena su tuhume shi, amma na yi kunnen uwar shegu da shi. Na hau shiri ina jiran lokacin da ya ce mana zamu tafi ya yi.

Ganin na yi nisa bana jin kira, sai ya fara haɗa kayansa zai koma, amma a ranar ko tunanin mai ya yi, sai ya sanar da ni shi ma yana son zuwa, saboda yana tsoron in ya koma yan bashi su dame sa.

Cikin daren da za mu je muka yi sallah na neman sa'a. Washegari muka kama hanya. Tafiya sosai muka yi har sai da muka gaji sannan aka isa. Sai da muka yi hutun gajiya sannan muka fara aiki.

Haka muke haƙin ƙasa babu ji gani, amma bamu taɓa hako komai ba. Gashi kullum ramin kara zurfi yake yi. Gabakiɗaya mun rame mun fita hayyacinmu.

Har mun cire rai da samu domin na sare sosai a wannan lokaci. Na fara tunanin mu koma gida saboda ina jin kamar zan mutu, don tsabar wahalar da muke sha. Shi ma kansa ogana ya sare sosai don har na fishi juriya.

Ƙwasam watarana muna cikin haƙi mu uku sai kawai muka haƙo zinari. Wani irin zabura Tanimu ya yi tare da fasa ihu." Yeeee! Wallahi mun samu."

Jin abin da ya faɗa sai kawai aka yi kanmu ana zare idanu. Tsoro ne ya kama shi ganin ihun da ya yi duk an kewaye mu.

Kamar wasa suna gani dai kawai suka kama mu dabbe za su ƙwace. Ganin wahalar da muke sannan muka samu, sai na zama mahaukaci kawai na shiga ka musu duka. Tunani na ke in har suka kwace shi ne kaɗai damar da zan iya fitar damu cikin halin ƙuncin. Da muke ciki. Faɗa sosai ya kaure a tsakaninmu, babu tsoron Allah burin su kawai su karɓa.

Wani ganin za mu gudu, sai ya samu abin da muke haƙi ya ƙwala wa Tanimu aka. Nan take ya saki ƙara ya faɗi ƙasa jini yana zuba a kansa.

Ganin haka na yi kukan kura na na yi kansu ina kai musu duka. Ganin na haukace sai suka gudu, domin ni kaina mamakin abin da na aikata na yi.

Da kyar muka samu suka gudu. Kan Tanimu muka yi muna kiran sunansa."Don Allah ka tashi kar ka mutu kai ka ce mu zo, kuma ga shi mun samu don Allah ka tashi."

Murmushi ƙarfin hali ya yi,"Lokacina ya yi saboda ba zan iya tashi ba, mutuwa zan yi. Don Allah ku kaiwa ahalina kasona."

Ganin yana bamu wasiya sai muka saka kuka muka rungume shi, cikin tashi hankali."Don Allah kar ka mutu ka tashi ka mori wahalar da ka yi. Kai ne fa ka kawo mu gurin nan, don Allah kar ka mutu."

Hannunsa ya daga mana sai kuma ya saki sharaf babu numfashi. Rungumesa muka yi muna kuka sosai. Mutuwarsa ta gusar da farincikinmu, domin mutum ne mai kirki yana da hankali mun saba da shi sosai."

Mutuwarsa ta sanya muka rage farinciki da muke yi, domin sai damuwa yi kusa sati ba tare da mun saki ranmu ba. Mun kaiwa iyayensa gawarsa sannan muka yi musu bayani.

A lokacin da muka je siyarwa aka gaya mana kuɗin da muka samu. Sai da muka yi suman wurin gadi, saboda kuɗi ne wanda zai canza rayuwarmu da ahalinmu bakiɗaya.

A Kano muka yii sannan muka tura kuɗin da za a yi mana gini. Ba sai da aka kammala komai sannan muka fara shiri, domin so nake aranar dana dawo washegari mu tashi.

Saboda yadda muka rame muka fita hayyacinki sa muka yanke shawarar mu tsaya a Kano sai mun dawo kamamminmu. Cikin ƙanƙanin lokaci ka canza nayi kyau, saboda abincin da muke ci. Muka siya kaya, mota da wayoyi."

Dago kansa ya yi yana kallonsu, ganin yadda idanunsa suka kike da hawaye. Ogan Ahmad ya nuna musu hotunan da ya ɗauka yana faɗin,"Tabbas wannan shi ne sanadin da muka samu kuɗi. Ga hotunan mu lokacin da muke aikin za ku tabbatar da haka. Har ma da zinari samu duk mun ɗauka don ya zamar mana sheda."

Mama da Nasreen rungume shi suka yi."Haƙiƙa Ya Ahmad bamu da ain da za mu ce maka, domin ka cike gurbin yaya da uba. Haka kasha wahala ka daure da rayuwarka don kawo mu fita daga talauci?"

Murmushi ya yi."Rayuwarku tafi mini komai a duk lokacin da na tuna irin rayuwar da muke yi, da kuma halin da Nasreen take ciki a gidan aurenta, sai na ji tamkar zan kashe kaina, ganin ba ni da halin da zan fitar da ku."

"Allah ya yi maka albarka ya ba ka mata ta gari da yaran da za su ji ƙanka Ahmad. Hakika duk uwar da ta haifi yaro irinka ta yi sa'ar haihuwa. Ubangi ya kare mini kai kula ya yi maka albarka."

"Amin Mama." Ya ce cikin tsanannin farikciki.

Nasreen kallonsa ta yi sai kawai ta faɗa jikinsa ta fashe da kuka."Ki yi shiru kuka ya kare. Yanzu farinciki zamu kasance Nasreen. Zan kula da rayuwarki babu namijin da zai ƙara wulaƙanta ki in har ina raye."

Murmushi ta yi tare da ɗaga masa kanta tana murmushi. A ranar sun kasance cikin tsananin farin ciki sosai. Wuni suka yi a gidan sannan su Gwaggo duk kom zuciyarta na fatan ina ma ace ita ta haife shi.

Nasreen sai kallon gidan suke yi. Sun takure a falo suna ta raba ido. Gani suke kamar in suka shiga ciki za a ce su fita, har yanzu sun kasa yarda wai gidansu ne. Su kansu Zainab da Raihann har Musaddik jikinta ya kwanta ya ɗauka baƙunta suka zo.

Ba ta yarda gidansu bar sai da aka yi ta shigowa da abinci aka sanya a store. Ahmad ne ya kalle ta ya ce,"Ku je ku ɗora mana abinci su ma su Gwaggo na sanya an kai musu."

Rungume shi tayi ta kar fashewa da kuka."Har yanzu ka kasa yarda gidanmu ne."

"Je ki yi mana girki sarkin kuka." Ya ce tare rabata da jikinsa. Share hawaye ta yi tana murmushi sannan ta shige kicin ɗin. Abinci kala-kala ga su nan sai abin da ta so ta girka. Sai kawai hawaye suke dubo mata tuna a gidan Faruk bai taɓa aje abinci a store ba. Bayan ta yi musu girki ya ci ya fita.

Baba yana dawowa ya shiga cikin ɗakin Mama, amma sai ya tsaya turus cikin mamaki. Ciki ya buɗe labulen ya shiga. Gabansa ya faɗi ganin kamar sun ɗauke kayan sawarsu."Guduwa duk suka yi?" Ya yi wa kansa tambayar cikin ruɗani.

Da sauri ya fito zuwa ɗakin Gwaggo. Tana zaune tana cin shinkafa da miya har da nama. Ba tare daya kula da abincin da take ci ba ya ce,"Ina Maman Ahmad?"

"Duk sun tashi Ahmad ya siya mata sabon gida suna...."

"Ya siya mata ko ya siya mana? Saboda rashin mutunci ba za a gaya mini ba?" Ya faɗa cikin ɓacin rai.

"Sai ka sanya yara su kaoka, domin babu bin da za ka ji a bakina."

"Ke Nabila ta shi ki kaini gidan." Ya furta tare da ɗauko jakar buhunsa.

Marwana
cikin hawaye ta ƙarasa gidan. Cikin sa'a ta same su duka a falo suna zaune. Kai tsaye inda Damir yake zaune da jaridar daily trust a hannunsa yana karantawa ta nufa, duk da cewar karatun yake, amma gabakiɗaya ɗaya hankalinsa babu a jikinsa. Marwana yake son ya tambayi inda ta je, sai dai ya kasa saboda bai san fassarar da Momi za ta yi mishi ba.

"Ya Damir ban tana sakin muguntar ka ta kai har za ka iya kisa ba sai yau?" Tambayar data yi mishi da kukan da take yi ya daga hankalinsa da Momi.

"Kisa kuma Marwana, kan ki ɗaya?" Muhsin ya ce yana kallonta.

"Eh, kisa ya yi ninyar yi. In har ka tsane ta haka ba ka buƙatar ganinta da ka gay mini, bawai ka je ka yi niyyar kashe ta ba. Ya Damir anya akwai Tauhidi a cikin zuciyarka. Ka yarda Allah shi yake kashewa kuma ka yi imani da babu wanda ya isa ya kashe wani? In har Kanada wannnan imanin ba za ka tsani Nasreen saboda mutuwar Anty Batula ba, har ka watsa mata ruwa ta faɗi ta ji ciwo."

Jin abin da ta ce duk zare idanunsu. Momi ce ta kalle sa cikin tsananin mamaki."Wai haka ya faru?"

Ba tare da ya amsa tambayar da ta yi masa ba, ya miƙe zai shige cikin ɗaƙinsa, saboda kansa da yake juyawa tamkar ana murza sitiyarin mota.

Ganin haka ta sha gabansa babu tsoro a fuskarta."Da gaske ne Momi ya Damir ya watsa mata ruwa bayan ya ganta a ruwa ba tare da taimaka mata ba, sanadin haka ta faɗa kwalbati har ta goce hannu kuma ta ji ciwo a ƙafafunta "

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Damir saboda me za ka zama mugu azzalimi shin mutuwa kanka aka fara, ko kana so kace mini ka fi son mace da wanda ya kawo ka duniya. Mahaifinka a hannunka ya mutu, amma ka manta komai kuma ka ci gaba da rayuwa. Karka manta ana iya canza mata, amma mahaifinka da? Ka ba ni mamaki Damir ka sanya mini kokwanto a raina. Wallahi in har ka ƙara gigin shiga cikin rayuwar yarinyar nan sai na yi mugun saɓa maka."

"Momi ki kwantar da hankalinki, saboda ba zai ƙara ganin ta ba, kamar yadda ya roƙa ta yi nesa da shi hakan zai faru. Ƴaƴanta Ahmad ya dawo da dukiya na san cewa zai kula da rayuwarta, don haka ga resignation letter ta ba ni na kawo maka." Ta ɗora masa kan jikinsa tana faɗin,"Ubangiji shi yake arzurtawa yau Nasreen ta fita daga cikin jerin da za ta buƙaci' taimako. A lokacin da Ya Ahmad ba shi da shi ya kula.da rayuwarta, ballantana da yanzu Allah ya yi masa arziki."
Chapter 54 · 0% Book details