← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 92

Sashe 59

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mai ya sa take shiga cikin farincikin baya ta sanya ni cikin damuwa, haka na nufin ba ta laifi kan abin da ya faru?" Ya yi wa kasa tambayarta yana shafa sajensa da ya kwanta a kyakkyawar fuskarsa ya kuma ƙawata fuskar. Komawa ya yi ya zauna yana tuna shigarta. Ga mamakinsa dawowarta aikin sai ya tsinci kansa cikin tsanannin farinciki, domin ji ya yi zuciyarsa kamar ana sauke masa dutsen dala.

Ba tare da sani ba wani laulausar murmushi ya kubce masa, har bai san lokacin da ya jawo laptop dinsa, ya fara aiki ba. Jefe-jefi zuciyarsa na tuno masa ita, tana bugu da sauri.

Nasreen kuwa bayan ta shiga ofis ɗinta ta zauna. Wayarta ta fara ƙara, ganin Annur ne ta saki laulausar murmushi ta ɗauki wayar. Ba su jima ba, ta kashe saboda sallama da ya yi mata sanin tana gurin aiki.

Marwana ta kira ta sanar mata da ta zo, sannan ta kashe wayar ta fara aiki. Hankalinta na kan aiki Ingawa ya shigo.

Murmushi ta yi tana kallonsa."Nasreen tauraruwar mata kin ga kyawun da kika ƙara? Gaskiya zan iya cewa kamar hurul ain."

Dariya maganar ta bata sai kawai ta kalle shi." Finally ƙanwata matata to be ta dawo aiki." Ya ce mata yana kashe mata idanu.

Murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sun ɗan taɓa hira ya tashi ya koma ofis dinsa.

Wayo shafin nan ya tayar mini da tsohon tsimi har na ji ina son rera waka. Habibi kai duniya ne💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃❤️❤️❤️❤️ su Damir an faɗa lambun soyayya.

Ayi haƙuri da wannan 🙏🙏🙏🙏
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whats

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 31

Murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sun ɗan taɓa hira ya tashi ya koma ofis dinsa.

Oga Damir a ranar haka ya tsinci kansa da matsanancin farinciki. Aiki sosai ya yi har yana mamakin kansa, domin rabon da ya yi irin aikin har ya manta. Ganin aikin da ya yi Muhsin ya riƙe baki."Please Ya Damir ka huta tun safe kake aiki."

Files ɗin hannunsa ya karɓa."Karka damu I will do it." Sai kuma ya kalle shi ya ce,"Bari ka gama wannan sai mu je lunch, saura minti goma lokacin break ya yi."

Zare idanunsa ya yi ya ce,"Ya Damir yaushe rabonka da ka je gurin lunch take away ake maka?"

"Yau ina son na je naci abinci da ɗan'uwana laifi ne?"

"A'a." Ya ce yana mayar masa da murmushin da yake masa. Mamakin ya ƙara kama shi ganin yana ta yi masa surutu. Ya ma rasa bakin amsawa sai dai ya ɗaga masa kai.

"Time up let's go." Ya ce masa tare da miƙewa yana kashe laptop ɗinsa.

Shima miƙewa ya yi cikin mamakin abin da ya sanya shi farikciki.

Shi ya fara gaba ya bishi a baya cikin mamaki. Damir kuwa tsintar kansa ya yi, da zuciyarsa na kitsa masa ya je inda ma'akaita duke lunch, wataƙila ya ga Nasreen da zuciyarsa ke ƙara son gani. Shi lamarin mamaki ya bashi, ganin duk yadda yake son hana xuciyarsa abin da take so ya ci tura, saboda a yadda yake ji ganinta shi ne maslahar, da za ta bar zuciyarsa bugawa da sauri tamkar za ta fito waje.

Suna tafiya yana raba ido tamkar wanda matarsa ta ɓace, amma cikin rashin sa'a bai ganta ba.

"Yaya, what for lunch?"

"Water." Ya ce masa domin da gaske baya jin cin komai.

Kallonsa ya yi cikin mamaki ya ce,"Amma ka ce mu je mu yi lunch?"

"Yanzu na rasa appetite ɗina please I need only water." Ya ce cikin ɗan damuwa ganin ba ta a gurin.

"Ok,". Ya ce tare da fara tafiya zuwa gurin.

Kamar ance ya ɗaga kansa, ya hagota tana tafiya da Ingawa sai Khausar. Wani irin mugun ɓacin rai ya ziyarce shi, har sai da ya yi dana sanin zuwa gurin. Da sauri ya miƙe tare da sakin tsaki zai bar gurin. Ganin haka Muhsin ya ƙaraso da sauri da lemu da ruwa da ya karɓo masa, sai kuma abincin da zai ci.

"Ya Damir." Ya kira sunansa ganin ya tashi zai fice.

Ba tare da ya kula ba, ya fice daga gurin zuciyarsa na tafasa. Muhsin ya bi gurin da kallo yana son ganin bin da ya ɓata ransa, ganin Nasreen da Ingawa sai ya kauda kansa ya bi bayansa da sauri.

Yana shiga ya yi jifa da flower vest da aka yi kwalliya da shi a ofis ɗin."Mai yasa in na ganta da wani nake damuwa har na ji tamkar zan kashe wanda yake tare da ita?" Ya yi maganar cikin tsananin damuwa yana rintse idanunsa.

Ba tare da ya bawa kansa amsa ba, sai Muhsin ya shigo."Ya Damir na.."

"Please Muhsin I need my space can you go?" Jin tambayar da ya yi masa ya ce,"Ok,"Ya juya ya fita baya ya ije masa ruwan da lemon roba, yana mamakin ƙarfin halinsa.

Kulle ofis ɗin ya yi, sannan ya zauna ya jingina kansa a danna kujeran yana jin wani ƙunci yana mamaye zuciyarsa. Nan take ya nemi farincikin da ya rasa. Sosai yake jin tsanar Ingawa a cikin ransa, har yana jin in har ya ci gaba da ganinsu zai iya rasa aikinsa, domin ba zai mayar masa da campani gurin soyayya ba.

Haka ya wuni sukuku, kamar mara lafiya har lokacin tashi yayi. Da yazo zai tafi tare ya gansu sun fito. A wannan karon daurewa kawai ya yi ba tare da ya kalli inda suke ba.

Nasreen kuwa ɗauke kanta ta yi ba tare data ji komai ba, ta yi wa Ingawa sama ta shige motarta.

A daren damuwa ta yi masa yawa har ya kasa bacci. Ji yake zuciyarsa ba za ta iya cigaba da ganinsu ba, ya zama dole ya ɗauki matakin da zai kusanta su. Da tunanin matakin da zai ɗauka ya je aiki.

Yana cikin wannan tunanin a ofis Annnur ya yi sallama ya shigo. Ransa ne ya ɓaci don ya san ba gurinsa ya zo ba. Kauda kansa ya yi ya ci gaba da aikinsa, bayan ya amsa sallamar tamkar an yi masa dole. Ƙarasowa ya yi, cikin sakin fuska ya ba shi hannu don su gaisa. Kamar am masa dole ya miƙa masa yana wani shan ƙamshi. Shi abin ma dariya ya ba shi. Ganin sun yi shiru sai ya katse shirun da cewar."Na zo gurin gimbiyarce, saboda ina son in ganta, gabakiɗaya na kasa sukuni jiya ne fa kawai ba mu...."

Kasa ƙarashe maganar ya yi, ganin wani mugun kallo da ya watsa masa. "An gaya maka kuɗin banza nake samu da za to aiki ka biyo ta?"

"To ya zan yi? Ka san dai yadda so yake ma zuciya, soyayyarta ya mini kamun kazar kuku.."

"Annur ba na son ji. Please as you can see am busy." Ya katse shi yana faɗin haka.

Dariya ya yi tare da miƙewa ya ce,"To ya zan yi yarinyar ce zazzafa ga shi ta iya kalamai tana kashe mini murya..."

"Get out Annur before I show you my madness!" Ya daka matsa tsawa yana faɗin haka.

Dariya ya saki ganin yadda ya kunna shi."Shikenan tun da ba za ka kai ni ba, bari na je Hajar ta nuna mini ofis ɗinta. Na ganta ko zan samu matsawa."

"Ka san Allah? Daga nan sai fita ka tafi gurin aiki, amma wallahi babu wanda ya isa yazo ya yi soyayya da ma'aikaciya, ka bari in ta koma gida ka je ka haɗiyeta " Ya furta cikin tsanannin zafi yana huci.

"Wai ni kan Damir ko son yarinyar nan kake yi?" Ya yi masa tambayar da ya razana shi.

Zare idanunsa ya yi da sauri ya ce,"Allah ya kyauta mai zan yi da ita, karka manta ita ta raba ni da matata ta bar ni a gwauro?"

"Wannan dalilin ya sanya na yi maka wannan tambayar, ka ga sai ka aureta ta maye gur..."

"Allah ya tsare ni." Ya tsinci kanshi da faɗin abin da bashi ne a zuciyarsa ba.

"Mene ne na tayar da jijinyar wuya? Tambaya ce, saboda naga yadda kake tada jijiyar wuya ne na ɗauka ko kishinta kake."

"Aini na wuce da ajinta." Ya ƙara furta wa.

"Haka ne mai aji, na manta ni dai bari naje na bawa fulawa ruwa." Biyo shi ya yi ya hana shi zuwa gurinta, har sai da ya raka shi gurin motarsa ya shiga yana ta yi masa dariya.

Sakin ajiyar zuciya ya yi, ganin ya ci nasarar ƙorarsa ya koma ciki.

A cikin kwanakin da Nasreen ta dawo aiki ya shiga cikin tsananin damuwa, yadda ita da Ingawa suke kunna shi, saboda a tare suke fitowa su shiga mota, kuma wani lokacin kamar haɗa bakin zuwa suke yi. Ga shi shi ma kamar an masa dole ya daidaici lokacin da take zuwa yake zuwa. In kuma ya riga ta zuwa, ba tare da ya ganta ba sai ya shiga cikin tashin hankali. Ya rinƙa safa da marwa har sai ya ganta. Ga kuma Annur da ya dame shi da maganarta. Wannan lamari ya jagula tunaninsa, har ya ɗan faɗa. Ya tabbata da za a gwada jininsa sai ya hau.

Ana wannan diramar yarinyar kaninn mahaifinsa Hindatu ta tashi aure. Damir shi ne jigon bikin domin komai shi ya yi mata. Mommy ta ce amarya ta yi zaman biki a gidan, musamman da yake ƙawar Marwana ce suna shiri sosai, kuma mahaifiyarta da mahaifinta sun rasu.
Chapter 59 · 0% Book details