Sashe 35
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ya Damir, kwana biyu ba kwa updating ɗina kame da activities na kampany?"
"Kin san na yi busy, amma ai Muhsin yana ƙoƙari?"
"Ni ma wallahi ban gaya mata ba, saboda na ga tana faɗin mu yi komai."
"Yanzu I need to know everything." Ta ce tare da saka loma fuskarta a ɗaure.
Gabakiɗaya suka bita da kallon mamaki jin abin da ta ce,"Lafiya kina zargin wani abu ne? Ko kuɗi kika nema aka hana ki?" Muhsin ya ce cikin ɗaga murya.
"No, kawai ina son na rinƙa sanin komai, ko laifi ne?"
"A,a kai Muhsin ka rinƙa ba ta update, dama ita ce ta ce ba ta buƙatar haka, tun da yanzu ta girma tana so babu laifi." Cewar Damir yana kallonsa.
"Ok," Ya ce tare da gallah mata harara, don ya san wata rigamar za ta ɓallo ƙila abu take son a siya mata.
"Yauwa game da appointment an ɗauka ne recently?" Ta ƙara tambayar da ya sa suka ƙara mamaki.
"Eh, guda goma yanzu muna son mu ƙara ɗaukar uku." Damir ya ce mata yana kallon Hajiya da ta tsaya da cin abincin tana kallonsu.
"Na gane to ina son a ba ni ɗaya." Ta daure ta furta zuciyarta na lugude, cike da tsoron ruwan da take son ɓallowa.
"Mai za ki yi da shi?" Muhsin da Hajiya suka haɗa baki gurin fadi.
"Zan bawa wata ce, saboda duk suna kawo waɗanda suka ga dama, amma babu wanda na taɓa kawo wa."
Damir da ya gama fahimtar inda take son zuwa. Tuntuni da ya ji ta yi maganar ya san akwai abin da take so, amma bai yi tunanin aiki za ta nema wa wata ba. Tunanin wacce za ta ba wa yake yi.
"Wace ce za ki bawa aikin?" Hajiya da Muhsin suka tambaye ta.
Satan kallonsu ta yi, ganin yadda suka mayar da hankalinsu kanta. Jikinta ne ya fara rawa, har ta ji tamkar kar ta furta wacce take son ba ta aikin, amma kuma tuna matsoraci ba ya zama gwani, sai kawai ta yi namijin ƙoƙari ta kawar da tsoron cikin dakuwar zuciya ta ce,"Nasreen ce."
Gabakiɗaya suka mike suna kallonta."What?" Suka haɗa baki gurin faɗin haka.
Ganin yadda suka tayar da hankalinsu kamar wacce ta gaya musu ta yi kisa, sai ta daure cikin rashin tsoro ta ce,"Nasreen, ƙawata wacce kuka sani, ita na ke son na wa aikin, saboda tana buk..."
Kafin ta ƙarashe Mommy ta ɗauke mata mari."Ashe dama kina tare da wannan yar iskan yarinyar da ta wargaza mini farincikin yarona, kuma ta hana shi aure? Duk da irin mugayen kalaman da na yi miki?" Ta ƙarashe tambaye cikin tsananin ɓacin rai.
Dafe ƙuncinta ta yi tana hawaye ba tare da ta amsa mata ba, saboda marin ya shige ta, sai kuma ta ce"Am sorry to say mommy duk abin da za ki yi mini ba zan iya rabuwa da ita ba, saboda she needs help Yayanta ya ɓata mijinta ya sake ta ya barta da yara guda biyu, babu cinsa bare kulawar makarantarsu ko magani. Kowa ya san yadda a mace bazawara take fama da wahala a duk lokacin da namiji ya saketa ya barta da yara. Nasreen tana cikin rayuwa na wahala, iyayenta basu da shi, kuma Allah ya haɗata da azzalumin namiji da ya barta da wahalar yaransa. Babu ƴaƴanta Ahmad a duniya. Ni kuma Allah ya sanya mini sonta ba zan iya ganinta cikin mawuyacin hali ba. Ki gafarce ni saboda tun ranar da na dawo na ga halin da take ciki, na ci gaba da ba ta taimakon da na saba. Ina so ta ina jinta kamar 'yar'uwa ta wacce kika Hai..."
"Rufe mini ba ki shashashar banza! Kin ji na rantse sai kin rabu da yarinyar nan.".
"Ba zan iya ba Mommy ba zan iya ganinta a cikin wani yanayi ba, na ɗauke kaina. Zan zame mata bango na maye gurbin ƴaƴanta Ahmad."
"Idan na ce ki zaɓi daya daga cikin ni da ita fa?" Ta ji muryar Damir cikin ɓacin rai yana magana.
Kallonsa ta yi jin bin da ya ce, ta san cewa ba ƙaramin wahala za ta sha ba."Kai ɗan uwansa ne ko da ace na zaɓi Nasreen kana nan a matsayinka, saboda jinin da yake yawo a jikinmu irin ɗaya ne."
"Kenan kin zaɓe ta kin bar ni?" Ya yi mata tambayar yana rintse idanunta, tare da ƙara tsanarta ganin ta raba shi da Batula kuma za ta raba shi da 'yar'uwarsa.
"Sorry, zan iya rabuwa da kowa in har zan taimaka mata, saboda a gurin Ubangiji ina da lada sosai."
"To sannu philanthropy, tun da kin zaɓe ta sai ki je kici gaba da rayuwa da ita, amma ki sani mun bar mata ke da iyayenta." Mommy ta ce cikin ɓacin rai.
"A ba ni gadona, ina da gado a ciki." ta furta tana share hawaye.
Mamaki ya kama su ganin yadda fuskarta babu nadama."Yanzu kin zaɓi ki barmu saboda wata bare can? To ba za a bayar ba, sai ki je can ku ci gaba da rayuwar tala..."
"Ka isa ka faɗi haka? Ka manta ina da gado ko don ka ga na bar muku komai bana magana. Ko kuma da believe cewar mace ba ta da matsayin da za ta iya juya duniyarta, mai rauni ce shi ya sa kuke abin da ku ka ga dama a kampanin har ba. Ni ma ina da ikon da zan ɗauki wacce na ke so aiki."
Mari Damir ya wanka mata cikin fusata."Ki kiyaye harshen ki ba zan ɗauki raini daga gareki ba, duk son da na ke miki."
Muhsin kuwa hauri zai kai mata yana faɗin,"Da ka tsaya na yi maganinta fitsarrarriyar kawai."
"Ai wallahi in har ana son zaman lafiya a gidan ko a ɗauki Nasreen aiki ko kuma a bani share nawa." Ta ce tana kuka tare da zama a ƙasa kamar ƙaramar yarinya tana birgima. Ganin haka Little Marwana ta faɗa jikinta ta saka kuka tana taya ta birgimar.
Mamaki lamarin ya basu sai kawai suka tsaya suna kallonsu. Tsaki Hajiya ta saki."Sai dai ki mutu amma ba za mu bawa maƙiyarmu aiki ba." Ta shige dakinta.
Damir ganin yadda suke kuka sai hankalinsa ya tashi. Ya kalli Hajiya da ta haye sama Muhsin ya zuba mata rankwashi yana dariya ya fita.
"Little Marwana zo mu tafi Anty Marwan rigima take yi, ba ta son Daddy tafi son wacce ta sanya ni cikin damuwa." Ya ce mata tare da miƙa hannu yana maganar cikin karayar zuci.
"No, dad do what Anty Marwana wants."
"I won't let's go." Ya ce mata cikin tsawa, amma sai ta maƙe ta ƙara rungumeta da take kuka.
Ganin haka ya saki tsaki ya fice daga gidan bakiɗaya. Suna fita ta share hawaye ta tana dariya. Mamaki ya kama Little Marwana."Anty, dama ba kuka kike yi ba?"
Dariya ta yi jin abin da ta ce,"Kuka ne kuma dadinki na ke yi wa ya fita. Mene ne amfanin kukan?"
Kallonta ta yi tana share hawaye na don ita bilhaƙƙi take kukan."Kar ki damu kin ji? Kukan ina yi ne saboda dadinki ya amince na ƙulla alaƙar da zai sanya miki Mommy, mai kirki wacce za ta so ki fiye da ni." Ta ce tana jan kumatunta.
"Ko ba kyau so?" Ta yi mata tambayar gani yadda ta yi shiru."Ina so Anty Marwana ina son wacce za ta sanya dadi ya daina hawaye da daddare yana rungume hoton Mommy."
Tausayinsu ya kamata jin abin da ta ce."In sha Allahu Ya kusa dainawa." Ta ce tare da kamata ta rungume.
Da sauri ta ƙara sakin kuka jin kamar
Hajiya na saukowa."Da ma na san a gidan nan ba a sona, ana nuna mini bambanci, saboda ni mace ce ina da rauni." Ta faɗa da ƙarfi yada za ta ji.
Hajiya ba ta kula ta ba, ta shige kicin taja jan tsuka ta wuce kicin.
Dirama sosai take yi a gidan har fushi da abinci ta yi, amma a bayan idanunsu za ta ci ta ƙoshi. Tun daga ranar ta daina cin abinci da su babu ruwanta da kowa. Su ma hakan bai dame su ba saboda abin da take so ba mai yiwuwa bane.
Ganin sun ƙi kula ta sai ta daina zuwa makaranta. Kullum tana cikin ɗakinta tana kuka. Hakan ba ƙaramin tayar da hankalin Hajiya ya yi ba. Ganin yadda ta rame ta fige sai ta same ta a cikin ɗakinta. Tana kwance ta yi rub da ciki da waya suna chatting da Nasreen ta ji alamun murɗa ƙofa. Da sauri ta kashe wayar ta tura cikin ƙarƙashin filo.
Shigowa ta yi ta tsaya a bakin ƙofar tare da jingina."Yanzu rayuwar da kika zaba wa kanki kina ganin kin yi adalci kenan? Kina huci don an ƙi ɗaukar ta aiki bayan ta yi sanadin da karatun ki ya zama shiririta ga shi yanzu ma a dalilinta kina son wasa da karatunki?"
Juyowa ta yi cikin hawaye jin abin da ta ce."Mommy, Nasreen ba ta da aifi a duk abin da ya faru, domin komai muƙaddari ne. Taimako na ke son yi in har ana son farincikinta dole a bata aiki tun da ta cancanci hakan, kuma ina da haƙƙin da zan ce a ba duk wanda na ke so."
"To ba za a bayar ba yar banza mara kunya, sai ki yi abin da za ki yi. Kin san waɗanda kike wa gorin kina haƙƙi duk sun fi ƙarfin abin da kike ikirarin kina da shi."
"Mommy, taimako zan yi kuma ba kyau tunanin Nasreen ce kawai za ta dawo da Yaya cikin hayyacinsa? Ita ce ta yi sanadin da ya kasa aure. Wataƙila za ta iya yin nasarar saka soyayyarta a cikin zuciyarsa, saboda ƙiyayya na iya zama soyayy.."
"Amma ba ki da hankali sai na rasa wacce zan yarda ya aura sai ita? Idan ma wannan ne tunaninki tun wuri ki cire banza mai tunanin yara kawai."
"Saboda ita talaka ce ko kuma bazawara?"