← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 92

Sashe 84

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabbas a ranar ta shigar da shi wata duniya. A ranar ta san ta yi aure, kamar yadda ranar ta zamar mata ranar mai mahimmanci haka Damir. Gabakiɗaya ya rikice ya susuce sai aika mata da tsaƙon soyayya yake yi mai rikita zuciya. Kamar ba oga Damir mai ɗauke fuska da jiji da kai ba. Yau ya zamar mata daban, ya koma kalar da bata taɓa sanin sa ba, domin ya bata alakar kula da rayuwarsa. A wannan lokacin tamkar bawa yake da sarki. Ansha soyayya kuma an bawa soyayya haƙƙinta. Iya lokacin da soyayyar ta ɗauka tana wahalar da rayuwarsu. Damir sai da ya fashe musu ita, domin ya kaisu duniyar da suka shagaltu.

Nasreen, ta gode wa Marwana sosai na shawarar ɗinkin da ta bata, domin ɗinkin da magungunan da ta sha, sun kai shi wata duniyar da ban. Shi kansa kunyar kasa ya yi, ganin babu ji da kai duk girman ya faɗi a gurinta. Nasreen kam an sha wahala sosai domin mijin nata gwarzo ne. Har kuka sai da ya sha, amma bai kula ta ba domin ya yi nisa a cikin duniyar da dole sai an isa.

Saboda tsananin farinciki, rungumeta ya yi tamkar zai mayar da ita ciki."Ina alfahari da ke matata Nasreen, haƙiƙa yau ko kwana sallah na yi ba zan iya biyan Ubangiji na kyautar da ya yi mini ba. Ina godiya ga Allah da ya mallaka mini ke. Allah ya barmu tare mu yi tsawon rai, kuma ya albarkaci zuriyarmu." Ya ce yana shafa kanta.

Hawaye sosai ya wanke mata fuska, bayan kukan da ta ci saboda ɗinkin ya sanya ta dawo tamkar sabuwar amarya.

Ji ta yi kamar ta kauda saura kunyarsa da take ji. Ta rungume shi. Haƙiƙa yau ta fahimci ita ma macce ce, wacce duk namijin da ya same ta zai yi alfahari. Ba ta a cikin matan da Faruk ya sha gaya mata sun rako mata ne. Tana da nata baiwar domin ta ga zahiri, duba ga yadda tsadadden namiji kamar Damir ya rikice. Ita ma mace ce wacce za ta yi alfahari da kanta.

Wayyo amarci mai daɗi amarya da ango sannunku da amrci.

Wasu mazan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 44

Ta ga zahiri domin Damir rasa inda zai sanya ta ya yi. A wannan lokacin ya sanya ta miƙe suka yi wanka. Raka'a biyu na godiya ya sanya suka yi. Sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikinsa."Allah ya cika mini burina na samu miji mai addini. Allah na gode maka. Ina fatan za ka tarbiyantar da yaranmu su samu ilmi kamar kai?"

Abin da ta faɗa, ya ƙara sanya masa darajarta a idanunsa."In sha Allahu Nasreen. Zan bawa yaranmu ilmi fiye da nawa."

"Na gode mijina." Ta furta tana share hawaye.

"Zo mu je ki kwanta kina buƙatar bacci." Ya ce mata ba ta yi aure ba sai ta ji ya ɗauke ta zuwa kan gadon.

Kunya da farinciki suka lulluɓe ta. Jikinsa ya jawota yana shafa bayanta, domin har addu'ar bacci shi ya yi mata. Rintse idanunta ta yi alamun ta fara bacci take yi, amma ta kasa baccin saboda murna.

Fahimtar haka da ya yi, ya kai libs ɗinsa saman nata. Bacci dai da ba a yi ba kenan, sai da aka ƙara raya daren, sannan ya ja bargo ya lulluɓe su saboda wani irin bacci da ya kama su. To amarya Nasreen sai na ce asuba ta gari ango har da kai. Gareku zawarawa, Allah ya sa ku yi koyi da kunyar da Nasreen ta yi. Bari mu leƙa gidan amarya Marwana da angon ta Ya Ahmad.

Bayan Damir ya tafi, wasu daga cikin abokansa suka bi shi don siyen baki.

Marwana tana zaune a falo ita da ƙawayenta, suna jiran ango da abokanansa. Jin alamun buɗe get sai zuciyarta ta buga.

Duba wayarta ta yi, ganin ya yi chatting ɗinta ta Whatsapp sun shigo. Gyara zaman ta yi, tana jin yadda zuciyarta ke zillo kamar za ta fito waje.

Da sallama suka shigo suna ta tsokanar Ahmad.

Ahmad kai tsaye, inda take zaune ya ƙarasa ya zauna."Amaryata da fatan bamu barka jira ba?" Ya yi mata tambayar yana kamo hannunta.

Ƙasa ya yi da kanta batare da tanka ba.

Ƙawayen ta suka ta so wata daga ciki ta ce,"Mu ya kamata ango ya tambaya ba amaryarsa ba, domin iyayenmu suna can suna jiranmu."

"Yanzu za mu sallame ku." Bilal ya ce. Sannan ya juya gurin amarya ya ɗora da cewa,"

"Ai ashe amaryar taka tana da kunya ba kamar ka ba?" Kwashewa da dariya suka yi.

"Tana da kunya mana, ko ni zumar sonta ya sanya na rinƙa gaya muku haka."

"A'a to, bari mu yi mu siya baki kar a kore mu."

"Ku dai yi sauri kar ku ɓata mana lokaci." Ya ce yana dariya.

Bayan sun gama barkwancin suka yi addu'a, sannan suka shafa suka siyi bakin.

A motar su suka tafi da 'yan matan. Ahmad ya raka su har get ya dawo ya kulle ƙofar gidan.

Ya shigo tana zaune a falo. Hannunta ya kama yana murmushi.

"Marwana yau kin ga mun zama ma'aurata?" Ya ce mata cikin zallar mamaki.

"Ni ma ina mamaki Ya Ahmad, ban taɓa tunanin haɗuwarmu da Nasreen zai haɗa mana zumunci."

"Haka Allah ke lamarinsa autar Mommy."

Rufe idanunta ta yi jin abin da ya ce. Kamar yadda addini ya sharada suka yi sallah, sannan ya yi mata addu'a.

Marwana, ta ci naman kaɗan saboda ta saba da Ahamd sosai. Duk da yau ne amarcinsu ba ta ji kunyar sa sosai ba, sai dai tsoro da take jin kamar zai fasa zuciyarta, musamman yadda ta ga yana mata.

Suna zaune suna hira, yana bata labarin yadda ɗaurin aurensu ya kasance. Ganin tana hamma ya kalle ta ya ce,"Ki je ki kwanta."

Kamar jira take yi ya ce mata, sai ta miƙe ta shiga cikin ɗakinta. Bayan ta canza kayan baccin, sai ta yi kwanciyarta a ɗakinta.

Tashi ya yi ya kulle falin, sannan ya shiga ɗakinsa, ya yi wanka ya ɗauki wayarsa zuwa ɗakinta.

Bugawa ya yi, ta taso ta buɗe tana hamma don har bacci ya fara kamata.

Matsawa ta yi ya shiga yana faɗin,"Na ɗauka ɗakina za ki kwanta babyna?"

Kunya ta ji ta ce,"Am sorry Ya Ahmad baccin ne ya kwashe ni kan kujara." Ta yi masa ƙaryar haka.

"Ok, babu komai gajiyar biki." Ya ce tare da zama gefen gadon.

Sakin ƙofar ta yi, ba tare da ta kulle ba ta koma kan kujera ta zauna. Ganin haka ya kulle kofar ya koma kan gado.

"Ki zo ki kwanta."

"No, zan kwanta a nan ba, saboda a gida a kan kujera na ke kwana na fi bacci."

"Shi ne ba ki gaya mini ba da sai na koya, don kin san babu yadda za a yi na barki ki kwanta ke kaɗai, dole na kula da amanar da Ya Damir, Nasreen, da Mommy har da Mama suka ba ni."

"Ai muna ɗaki ɗaya ka yi baccinka." Ta ce tare da kwanciya kan kujera.

"Ba za a yi haka ba, saboda in sauro ya cinye ki mai zance wa waɗanda suka ba ni amanarki?"

Dariya ta yi jin wayon da yake son mata, kamar ƙaramar yarinya."Kujerar ya yi mana kaɗan."

"Ok, to ki kwanta a gadon bari na kwanta a nan."

Ta buɗe baki za ta yi musu, sai ya watsa mata kallo. Babu musu ta koma ta kwanta tare da jan bargo."Good night Ya Ahmad."

"Good night." Ya ce mata yana dariya jin yau ko sunan soyayya ba a kira shi da shi ba.

Tana kwancen a tunaninta wayo zai yi mata, amma tun tana tunanin zai jawo gadon, har ta cire bacci mai ƙarfi ya kwashe ta.

Ahmad yana kwance, yana lura da ita sai da baccin ya kwashe ta, sannan ya hau gadon ya haɗata da jikinsa.

Cikin bacci ta ji sa a jikinsa da sauri ta miƙe. "Let's sleep baby." Ya ce mata da wata kalar murya.

Tsoro ta ji muryarsa sai ta kwanta. Duk dai kauce kauncenta sai da ya shawo kan abinda ya amshe sadakinsa. Yasha kuka don babu wanda ba a kira ba. Hatta Damir da Nasreen da suka tafi duniyar sama sun sha kira.

Cikin farinciki ya rungume abinsa yana rarrashi. Bayan sun yi wanka sai bacci.

Kamar yadda Damir yake jin daɗin baccin haka Nasreen, domin za ta iya cewa tun da take bata taba yin bacci mai daɗi irin sa ba.

Kiran sallar asuba ya farkar da Damir. Ya buɗe idanunsa a hankali yana tuna daren jiya. Murmushi ya saki cikin tsananin farinciki tare da ƙara rungumeta.

A hankali ya zare jikinsa tamkar wanda ya shinfiɗar da jariri, saboda har filo ya tura mata a kusa da ita. Duƙawa ya yi ya sumbaci gefen fuskarta, sannan ya nufi bayi ya yi wanka da alwala.

Raka'atul fijr ya yi, sannan ya ɗauki Alqur'ani yana kara yawa cikin ƙira'a mai daɗi.

Nasreen da take kwance, tana kasa kunne don ta saurari karatun, duk da ya rage muryarsa saboda kar ya tashe ta, amma ba tare da ya san ta riga shi tashi ba.

Wasu hawayen farinciki suka gangaro mata. Yau ita ce Allah ya ba ta mijin da zai tashi tun asuba ya yi sallar nafila, sannan ya yi karatu yana jiran ayi sallah. Hawaye sosai yake zubar mata cikin tsantsar farinciki.
Chapter 84 · 0% Book details