Sashe 23
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana kwance ta ji ana ƙwanƙwasa get ɗin gidan. Da ƙyar ta samu ta je ta buɗe masa.
Ganin tana layi ya kamata yana faɗin,"Ba ki da lafiya, amma ba za ki fada ba, sai ciwo ya ci ƙarfinki Nasreen?"
"Kwana biyu ne na fara ciwon Ya Ahmad."
"Ma za shiga ki ɗauko mayafinki, mu je asibiti, domin ciwon nan ya wuce kyamis."
Suna zuwa asibitin likita ya tabbatar masa da ƙarin ruwa za a yi mata, saboda yadda jikinta ya yi weak.
Duk da babu wasu isassun kuɗi a hannunsa, ya ba da umurnin a sanya mata ruwan.
Fita ya yi bayan ya ɗauki wayarta. Numbar Faruk ya ɗauka a cikin wayarta, sannan ya kira shi.
"Hello," Ya furta ba tare da ya ce komai ba.
"Ahmad ne Yayan Nasreen." Ahmad ya ce bayan ya yi masa sallama.
"Ok, lafiya?" Ya yi maganar cikin sham ƙamshi.
Ƙoƙarin danne ɓaci ransa ya yi."Nasreen ce babu lafiya muna asibiti."
"Allah ya ba da lafiya, ai na gaya mata ƙwandalata ba za ta yi ciwo ba, tun da shegen taurin kanta ya kai ta ta yi ciki.
A yadda ransa ya ɓaci matuka, in har da yana kusa da shi, babu abin da zai hana bai kai masa duka ba.
"Faruk, da kake ganina ni ma ƙwallon shege ne, saboda wallahi in iskancinka haye ka yi, to ni gadonsa na yi. Albarkacin Nasreen kake ci, in bacin haka ko kallon banza ba ka isa ka yi mini ba."
"Ai ba abin mamaki bane, in ka gaya mini kai cikakken ɗan bariki ne, tun da ba ku samu tarbiya ba. To ni ma daidai na ke da kai, in saboda ita kake daga mini. Ga tan nan sai ka je ka yi kwaɗonta ka ci, domin in har ba ta amince an zuba cikin nan ba, sam ba za ta dawo gidana." Yana faɗin haka ya yanke wayar.
Sororo ya yi da wayar a hannunsa cikin takaici. Ji yake kamar ya janyo ta wayar ya yi masa dukan tsiya.
Komawa cikin ɗakin ya yi, ganin tana bacci sai rufe ƙofar ɗakin ya fita.
Da ƙyar ya samu bashin dubu biyar ya biya kuɗin asibitin. Bayan an ƙara mata ruwan aka ba ta sallama da daddare.
"Nasreen, na kira mijinki amma ya yi mini rashin mutunci, kuma ya ce in har ba ki zuba cikin jikin ki ba, sam ba za ki zauna masa a cikin gida ba."
Barka da sallah fans ɗina ina yi muku Barka da sallah tare da fatan Allah ya karbi ibadunmu. Sai na zo muku yawon sallah. Tamu Jamila lawal Zango Jamsy❤️❤️❤️❤️❤️🙏🙏🙏💃💃 Nasreen, Damir, Marwana, har ma da Faruk capacity yana muku barka da sallah.
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 12
Hawaye suka wanke mata fuska jin abin da ya ce. Cikin jin kunyar sanin tana ɗauke da juna biyu ta ce,"Ni ma bana buƙatar ci gaba da zama da shi, kuma duk abin da zai faru ba zan zuba cikin jikin ba, amma kuma ina tsoron Baba, wataƙila ba zai lamunta na zauna ba."
"Ki koma gidanki Nasreen in har ba takadda ya ba ki ba, kar ki sake ki dawo. Ga wannan ki sayi abin da za ki ci."
"To Yaya, na gode Allah ya saka da alkhairi." Ta ce masa tare miƙa hannunta ta karɓa kuɗin.
Har ƙofar gida ya ije ta sannan ya tafi. A lokacin da ta shiga gidan baya nan. Kwanciya ta yi bayan ta sha magani. Bai dawo gidan ba, sai goman dare.
Hankalinsa kwance ya shigo cikin gidan har da 'yar waƙarsa, domin a tunaninsa babu kowa a cikin gidan.
Kai tsaye ɗakinsa ya wuce, amma sai ya dawo ganin haske a cikin ɗakinta.
"Nasreen," Ya kira sunanta cikin ɓacin rai.
"Sannu da dawowa." Ta ce masa tana ƙoƙarin tashi.
"Ba na ce kar ki dawo gidan nan ba, in har ba ki zubar da cikin jikinki ba?"
"Gaskiya ba zan zubar ba, kuma ni ba zan tafi gidanmu da sunan yaji ba."
"Ok, uban me kike so?"
Shiru ta yi ba ta ce masa komai ba.
"Kin san dai ba zan sake ki ba, don ban gama more kuɗi a ba, kika yi ciki. In har saki kike nema sai dai a biya ni duk abin da na kashe." Ya ƙarsahe maganar cikin murmushin ƙeta.
Jin abin da yasa hankalinta ya tashi matuƙar gaske! "FARUK, ka ji tsoron Allah akan abin da kake akata mini. Ka san ba ka son haihuwa da ni, mai ya sa ka aure ni?"
"Sai aka ce miki duk wanda kika ga ya yi aure don ya haihu ne?Ina sam ba zan tarawa kaina ɗawainiyar yara ba, tun ina ƙaramin a ban girma ba, ba zan cuci kaina na mai da kaina tsoho ba."Ganin ta yi shiru tana kallonsa ya sanya shi kama hannunta.
"Ki fahimci abin da na ke son ki gane Nasreen. Guda nawa muke? Muna da time da za mu ci amrcinmu. Mu more rayuwarmu sai mun girma mun ci ƙuruciyarmu, sai mu haifi yara biyu ko ɗaya."
"Ka fito fili ka gaya mini sai ka lalata mini mahaifa da magungunan hana haihuwa, kai kuma sai ka je ka auro wacce za ta haifa maka yara. Sam ba zan yarda da daɗin bakinka, na lalata mahaifa ta ba."
"Shegen taurin kanki da rashin mini biyayya suke ƙara tunzura zuciyata na ke miki wulakanci. Kin san Allah? In har ba za ki cire cikin nan cikin lalama ba, sai dai na ba ki zaɓi biyu. Ko ki cire cikin nan ko kuma ki koma gidanku."
Shiru ta yi tana kallonsa cikin tsananin mamaki.
"Ba zan cire cikinta ba, kuma ba zan koma..."
"Wallahi ba ki isa ba! In har kin zaɓi barin cikin jikinki. To ba za ki kwantar mini agida ba." Ya ce mata tare da miƙewa yana zare idanu.
Miƙewa ta yi ta ɗauki mayafinta, don ta san yadda ya nuna ba zai ƙyaleta ta kwana ba.
Ba tare da ta ce masa komai ba ta kama hanya. Tana fita ya rufe ƙofarsa da ƙarfi bayan ya zabga tsaki.
Tsananin mamakin rashin tausayinta ya kamata. Dare ya yi sosai domin a lokacin goma har ta wuce.
Sauran kuɗin dake hannunta ta tari mashin har ƙofar gida.
Babu kowa a tsakar gidan ta yi sallama ta shiga cikin ɗaki. Mama da ta ɗauki muryarta, da sauri ta tashi tana kallonta.
"Nasreen, lafiya da daddaren? Ahmad bai jima da dawowa ba, ya sanar mini da ya mayar dake gida."
"Eh Mama, zabi ya ba ni ko na xubda cikin cikin ko kuma na bar masa gidansa."
"Anya Faruk na da hankali kuwa?" Mama ta yi mata tambayar cikin damuwa.
Za ma ta yi a gefen gadon tana share hawaye."Ya ce sai kin xubda ciki, sai ka ce shi ba da aure aka haife shi ba? Kuma duk wanda ba ya ƙaunar aure, ba ya ɗabbaka sunnar da ya zama tushen sa ke nan."
"Lamarin Faruk sai shi Mama. Sam ba ya ƙaunata. Na fi buƙatar a raba auren, don ban san nan gaba yadda rayuwar aurenmu zai kasance ba."
"Kul Nasreen! Zawarcinma babu daɗi. Wataƙila don ba ki taɓa yi bane, shi ya sa kike faɗin haka, amma ko zawarcin kika dawo kina yi, shi babu wani samun kwanciyar hankali, musamman da kin san yanayin rayuwar da muke ciki. Ga shi in auren na ki ya mutu, tunanin wane irin miji da za ki aura ya ishi rayuwarki. Sannan shi ɗan cikin kin san gararin rayuwar da zai yi? Mahaifinsa bai riƙe shi ba sai wani. Ko a nan gidan za ki watsar da shi shi ma ya tashi a irin halin da kika tashi? Don haka kar ki ƙara to wa kanki fatan zawarci, sam ba shi da alfanu ga 'ya mace."
"To Mama ina ji ina gani saboda takaici da tsoron zawarci sai na bari baƙincikin Faruk ya kashe ni? Ba ki san halin da na ke ci ki ba, in har yana cikin gidan nan, ban isa na zauna kan kujera na tashi lafiya ba, sai ya yi mini gori."
"Ki yi hakuri laifin mahaifinki ne. Shi ya ja mini duk abin da yake miki."
"Lafiya Mama ta dawo?" Ahmad ya miƙa mata ledar sabar biredi da ya shigo mata yana tambayarta.
"Ga ta nan wai ya ba ta zaɓi, ko ta xubda ciki ko kuma ta dawo gida."
"Kai! Anya wannan ɗan iskan yana da kirki kuwa? Cikin dare zai turo ta gida, in 'yar'uwarsa ce aka yi wa haka zai ji dadi?"
"Allah dai ya kyauta na gaba kawai, amma mijin Nasreen yana buƙatar gyara a rayuwarsa."
"Ki bar ni da shi sai na koya masa hankali."
"Mai za ka yi masa? Kar dai ka je ka cutar da shi, tun da dai an riga an haɗa zuriya."
"Shi ke nan sai na ƙyale sa ina kallo yana cutar da ita?"
"Allah ya shirye shi. Addu'ar da za mu yi masa kenan." Mama ta karashe maganar cikin damuwa.
"Ki kwanta ki huta kar ki sa ya abin a ranki. In sha Allahu, ba za ki wulaƙanta ba." Ahmad ya ce yana kallonta.
Gyara kwanciya ta yi kan gadon Mama sai bacci.
Babu wanda ya san da zuwanta sai da safe. Bayan ta yi sallah komawa bacci ta yi, don har lokacin jikinta babu ƙarfi. Da gari ya waye Mama ta dama musu koko da ragowar biredin da ta rage suka sha.