← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 92

Sashe 20

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta rasa kuka za ta yi ko mamaki. Ganin lokaci guda ya canza kamar ba shi ba.

Miƙewa ta yi da sauri cikin minti goma ta shirya kamar yadda ya buƙata. Da kyar ta cire ragowar kunyarsa ta shiga ɗakin kamar yadda ya umurce ta.

Banza ya yi da ita har ta gaji ta zauna a gefen gadon. Sai da ya gama abin da zai yi a laptop ɗin, sannan ya kashe ya miƙe mata hannu.

Jikinta na rawa na tsoransa ta isa gareshi." Matuƙar kika ce saɓa mini za ki yi sai kin raina kanki, don haka ki kiyaye kin ji?" Ya ƙarashe maganar cikin ɓacin rai.

"To, ka yi haƙuri." Ta furta cikin muryar kuka.

Ba tare da ya ce komai ba ya ƙara tsuka kwanta.

Ganin abin da ya yi mata ya sanya take matuƙar taka tsantsan. Inda ta godewa Allah 'yan gidansu Ya Ahmad ya hana kowa zuwa gidan, domin ya san halinsa.

Mutane ne dai 'yan unguwada abokan da abokan arziki suke zuwa, amma ba ta da halin da za ta buɗe.

Ganin an yi sati biyu da bikin, bai yi mata maganar zuwa makaranta ba ya sa ya ta shirya.

Ya Ahmad ya fara kira ta bayan ta ɗaya ya ce,"Nasreen, maganar makaranta ko har yanzu amarcin kike ci?"

Tambayar da ya yi mata, ya sanya ta ji kunya har sai da ta rufe idanunta."A'a shi ne dai bai yi mini maganar ba."

"To ki shirya ki yi masa magana, ai dama an yi da wajewa."

"To Yaya Ahmad." Ta ce tare da kashe wayar.

Ranar Monday da safe da suke da lecture ƙarfe bakwai da rabi.

Yana kwance ta shigo cikin ɗakin bayan ta gama shirya wa.

Ƙarar buɗe ɗakin ya sanya ya buɗe idanunsa.

"Ina kwana?" Ba tare da ya amsa mata ba ya ce,"Nasreen, ɗauko mini wayata na ga lokaci, yau takwas zan fita ina da meeting."

"To," Ta ce masa tare da miƙa masa wayar.

"Bakwai da kwata ta yi." Ta furta masa.

"Da sauran lokaci bari na koma bacci." Ya ce mata.

"Na shirya zan wuce makaranta."

Jin abin da tace ya sanya shi ta shi zaune yana kallonta, don sai a lokacin ya gane shirin fita ta yi.

"Makaranta da wuri kuma daga aure sai komawa makaranta?"

Mamakin abin da ya ce, ya kamata wanda ya sanya ta yi shiru ta kasa magana.

"Ba yanzu ba, domin daga aure ba zan bari kina gantali a titi ba."

"Na ga kai ma ka koma aiki kuma test za mu fara..."

"Karki gaya mini maganar banza!" Ya katse ta yana fadin haka wanda ya sa ta yi shiru.

"Ok, na koma aiki, goyyaya za ki yi da ni? Ke ni fa ba zan lamunta da zuwa makarantar nan ba, saboda na aminta ne kawai don a lokacin ba ni da zaɓi."

Jin abin da ya faɗa hankalinta ya yi mummunan tashi.

"Farouk, don Allah ina son karatuna kar ka hana ni." Ta furta cikin muryar kuka.

"Dole ki so mana tun da za ki rinƙa fita gantali." Ya ce tare da miƙewa ya shiga bayi.

Kuka ta saka ta fita falo ta kira Ahmad.
"Ya ce shi bai lamunta da karatuna ba."

"Zancen banza! Ai wallahi ya yi kaɗan " Cewar Ahmad cikin zafi tare da kashe wayar.

Kiransa Ya shiga yi wanda ya ƙi ɗauka kuma yana ganin kiran.

Sai da ya gama shirya wa, ya fito daki ya same ta tana zubar hawaye."Kin haɗa ni da Ahmad. Kin san shi ya haife ni, dole na ji tsoron sa na barki. Ina aurenki ba uban da zai rinƙa kafa mini doka." Ya ciro naira ɗari biyar ya wuta mata.

"Ga shi ki nemi abin kari, don kin ɓata mini rai ba zan baki abinci ki dafa ba."

Share hawaye suka ƙara zubo mata. Ɗari biyar ɗin tabi da kallo tare da tunanin abin da za ta siya da shi.

Kuka sosai take yi ganin ya fice daga gidan.

Ahmad kuwa cikin ɓacin rai yake zaginsa ganin ya ƙi ɗaukar wayar.

"Wallahi uban kuturu ya yi kaɗan dole ta ci gaba da karatunta." Cewarsa yana safa da marwa a tsakar gidan.

Baba da ya fito daga ɗaki, da asuwaki yana goge bakinsa ya tsaya yana kallonsa ganin yadda ya ke huci

"Kai kuma da uban wa kake ɓata rai da zage-zage da sassafe nan?"

"Ni da wancan tijararren mijin Nasreen."

"Mai ya faru?" Ya tambayesa jin abin da ya ce.

"Wai ba za ta ci gaba da karatu ba, bayan duk abin da na kashe?"

"To shi ne me, ba mijinta bane? Ga ga ka fitar harkar rayuwar gidansa kar ka sanya ya yi fushi, don ba zan lamunci zawarawa biyu a gidan nan ba. Kana ganin tujarar da mijin Abida ya yi, har da saki ɗaya ya yi mata ko? Roƙon sa na ke ya zo ya kwashi matarsa, don babu shegiyar da za ta zauna a gidana, ballantana ta zo da yaro."

"Ka san Allah Baba? Dole ya bar Nasreen ta gama karatunta don bai isa ba."

"To sai ka je ka tilasta masa tun da uban shi ne kai." Ya ce masa daidai lokacin da zai fice daga gidan.

Daga nan kai tsaye ofis ɗin da ya wuce. Kamar ya san zai zo, da aka gaya masa ana nemansa sai da ya shanya shi, sannan ya ba da umurnin ya shigo.

Ahmad da zuciya ta tiƙo shi, amma babu yadda zai yi, ya daure ya tura ƙofar.

"Wa alaikissalam," Ya amsa sallamar ba tare da ya kalle shi ba.

"Na zo kan maganar karatun Nasreen."

"Ba ta gaya maka abin da na ce ba?"

"Kai ma kasan wasa kake Faruk! Wallahi ka ji na rantse maka, dole ta ci gaba da karatunta, domin zan iya komai don na ga ta kammala digiri."

"Nasreen, mallakina ce, kuma ina da iko na hana ta abin da ban yi na'am da shi ba."

"Kai ɗan boko ne amma na fika iya amfani da bokon. Duk maganar da muka yi da amincewar da ka yi za ta yi karatu, duk na yi recording ɗinsa. A addini in har mutum ya amince da abu kuma ya musa, mace na da damar da zata zaɓi rayuwa da shi ko rabuwa. Nasreen za ta zaɓi karatunta ko da ace tana sonka, in har na tilasta mata, ballantana kasan babu soyayya a tsakanin ku."

Jin abin da ya ce ya ɗan firgita amma sai bai nuna masa ba.

"Rayuwarta ka cuta saboda ko yau muka rabu na fanshe kuɗina, tun da na mayar da ita ƙaramar bazawara. Don haka, ka je duk abin da za ka yi." Ya ce masa yana huci.

"Ok, to shikenan tun da haka kace?"Ya buga ƙofar ya yi da ƙarfin gaske.

Rintse idanunsa ya yi, saboda ƙarar ya firgita shi, kamar yadda barazanar da ya firgita shi.

Yana son Nasreen sam ba zai iya rabuwa da ita ba. Da sauri ya miƙe ya shiga motarsa.

Kamar yadda ya zargi gidansa zai wuce. Aikuwa yana shiga cikin gidan ya ga mashin ɗinsa a cikin gidan.

Gabansa ne ya faɗi ya shiga cikin falon da sauri.

Nasreen na zaune Ahmad yana ba ta baki tana ta kuka.

"Ya Ahmad, ina son karatuna, amma kuma bana son na zama bazawara."

"Karki damu Allah yana tare da ke, in kuma kin haƙura da karatun ba zan yi miki dole ba."

Miƙewa ta yi za ta bishi Faruk ya shigo.
"Wallahi in har ka fitar mini da mata sai na yi ƙararka." Ya faɗa tare da riƙe hannunta.

"Ka kai ni kotun ƙoliya, amma matuƙar ba za ka amince da karatunta ba, sai ta bar gidan nan."

Ganin da gaske yake hankalinsa ya tashi.

"Na aminta ta ci gaba, amma ƙwandalana ba za ta yi ciwo ba."

Jin abin da ya ce ya sanya ta zare idanunta.

"Ni ma na amince." Cewar Ahmad cikin ɓacin rai.

"Nasreen ɗauki Hijabinki, ki wuce makaranta."

"Girgiza kanta yi cikin damuwa tana kuka.

"A'a Ya Ahmad, mu bar zancen karatun nan, kana da ɗawainiya a kanka."

"Karki damu je ki shirya, na yi miki alƙawarin in har Ina raye sai kin kammala karatun ki."

Farouk tsuka ya ja ya fice daga gidan cikin ɓacin rai, domin ya so kar ta yi karatun.

Kallonsa take yi cikin mamakin muguntarsa. Tabbas ya cika maƙetaci wanda ba ya son cigabar matarsa.

"Ya Ahmad, ban yi dacen miji ba." Ta furta tare da ƙara fashewa da kuma ta rungume shi.

"Ki yi haƙuri. Matuƙar ina raye ba zan bari ki yi kuka ba."

Kuɗi ya miƙa mata dubu ɗaya." Ga shi ma za ki ɗauki Hijabinki na kaiki makaranta, in kin gama sai ki dawo. Zan tura miki kuɗi a account ɗinkin, wanda zai ishe ki da transport da abinci na satin nan."

"Na gode Yayana haƙiƙa bani da kamar ka." Ta ce masa cikin kuka.

Wanke fuskarta ta yi ta shafa gida sannan ya kaita har cikin makarantar.

"Ki kula da kanki sannan ki yi karatu. Ke yanzu matar aure, ban da kula wasu samari da kuma 'yan mata marasa tarbiyya."

"In sha Allahu, zan kiyaye." Ta ce masa tana ɗaga masa hannu har ya tafi.

Ajiyar zuciya ta yi ganin Ubangiji bai ba ta miji da uba na gari ba, amma sai ya ba ta Yaya wanda ya cike dukkan gurbin.

Fadila ta taso ta rungume ta cikin murna.

"Mara mutuncin ya barki?"

"Hmmmmh! Ke dai akwai labari." Ta ce mata.

Bayan sun gama lecture kai tsaye gida ta dawo. Tana zaune a falon ta ci ye sauran gurasar da ta siya. Kwanciya ta yi ta huta, sannan ta miƙe ta ƙara gyara gidan.

Farar taliya ta dafa ta ci da mai da yaji da daddare ta kwanta.

Bai dawo gidan ba sai goma da rabi.

"Sannu da zuwa." Ta ce masa tana kallon sa. Tsaki ya yi ganin ta a falo ya shige ɗauki sa da leda niƙi-niƙi. Sai da ya ci ya yi tam, sannan ya kwashe ragowar ya sanya a frij.

Ta shi ta yi ta shiga ɗaki ta kwanta. Dama ta gaji bacci kawai take son yi.
Chapter 20 · 0% Book details