← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 92

Sashe 7

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi ban damu ba, saboda sam ba shi a gabana. Kawai iskancin da yake yi ne yake damuna."

"Duk zai wuce in kika jure komai zai zama tarihi. Zaƙaƙa fari yake mata, in dai Faruk ne. Kina ganin za ta ci gaba da jure maƙonsa?"

"Ina fa ko jiya sai da suka yi a kan ya fito mata madara sachet ɗaya na naira ɗari."

"Kina nan za ki ji sun yi uwar watsi zama da Faruk, sai ke da ake miki dole." Ta ce tana kallonta.

"Ko ni haƙurina ya zo ƙarshe ai."

"Kin ga yanzu bari na yi masa transfer na kuɗin nan, don a ɗinka mana hijaban a kawo da wuri."

"Gaskiya ki tura masa sa dubu ashirin ɗin sai na riƙe biyar na turawa Mama su yi amfani da shi."

"To bari na yi masa yanzu." Ta ce tare da ɗaukar wayar ta.

Ba ta bar gidan ba sai, da ta huta saboda dama daga makaranta take. Da su Raihan suka dawo, sannan suka koma gida. Kicin ta nufa ta ɗora girki ta zauna a kicin ɗin ita da yara. Suna wasa tana karanta wani littafin mai suna ranar wanka duk na Jamila Lawal Zango, don har ta gama Sakacina. So take ta rinƙa karatun saboda akwai tarin ilmi a ciki, sannan ga ɗebe kewa. Tun da ta fara karatun tunaninta yadda ƙarshen book ɗin zai kasance sam ba ta da lokacin shiga ƙunci da damuwa. A fara karatun ta ko yi darussa da dama. Duk wani abin da jarumar take yi na gari take ƙoƙarin koya. Kamar su kula da ibada tsafta, gyara jiki da kuma yanayin zamantakewa da al'umma. Hatta gyaran jiki sai ta ji tana don ta fara duk da cewar wani lokacin rashin kuɗi yake hanata. Abin mamaki Nasreen da kullum tana cikin damuwa, tare da tunanin rayuwarta babu wani amfani, sai ga shi ta sayi lalli da kurkur ta shafa a fuskarta.

A lokacin da ta je gidan Maman Muwaddat ta ce mata."Don Allah ina son ƙunshin da aka yi miki wanda ya fita, ya yi mini kyau in son na yi."

Kallonta ta yi galala cikin tsananin mamaki."Nasreen ke ce za ki yi ƙunshi? Zan iya cewa na manta rabon da ki yi ƙunshi, duk irin nacin da na ke miki da minti, saboda kina da haske ƙunshi ba ƙaramin ɗaukar ki zai yi ba."

"Ada ina tunanin tun da miji ba ya sona wa zan yi wa, amma kin san yanzu da na fara karatun novel sai kawai na ji ina son na yi don na gyara kaina, kuma na gani na yi sha'awa. Ni fa na cire takaicin ɗa namiji rayuwata zan yi mai daɗi, saboda in ba haka na yi ba wataƙila sai dai na yi bugga."

"Haka ya kamata dama, saboda in har kika sanya abin a ranki, to ke za ki yi wa kanki asara."

"Wallahi kuwa ga takaicin miji ga na mahaifina."

"Allah ya kawo miki mafita." Ta ba ta amsa tana ƙoƙarin ɗaukar wayarta.

"Bari na kira mai ƙunshi har gida take zuwa ta yi mini, da ma ina son ya yi mini kitso, sai ta fara miki lallin kin san Allah saboda farinciki ni zan biya."

Dariya ta yi ta ce,"Kai Maman Muwaddat, zan biya akwai 2k a hannuna, kuma ni ma zan yi kitson."

"To bari na kirata dai ta yi mana tun da akwai sauran time, kuma tana da sauri, amma kafin ta zo ki tsife na wanke miki sai na budar Miki."

"To aikuwa na gode da yake kitson ba shi da waya." Ta ƙarashe maganar tare da cire hijabinta, ta saɓule gashin kanta. Tana da gashi sosai ga shi baƙi

Ana busar da kan mai ƙunshin ta zo. Zuwa uku da rabi ta kammala har ta fara wa Maman Muwaddat. Ƙunshi ya yi kyau sosai. Nasreen ana mata tana karatunta. Da aka gama sai ta kalli ƙunshi cikin farin ciki ganin yadda ya yi kyau.

Bayan an gama ta koma gida wanka ta yi, sannan ta saka doguwar riga ta fito kicin. Abinci ta ɗora suka dawo falo suna kallo, saboda Rashida ba ta nan. Ba su jima a falon ba ta dawo hannu ta cike da kaya. Babu sallama ta shigo kamar ba musulma ba, kai tsaye ɗaki ta wuce ta yi wanka, sannan ta fito ta zauna a falo. Wani banzan kallo ta wurgar mata tare da ɗaukar remote ta canza tashar daga catoon da su Raihan suke kallo zuwa Nigeria Film. Ganin haka Musaddik ya saka kuka yana kallonta. Da sauri ta ɗauke shi ta kama hannun Raihan.

"Ku zo mu je na kunna muku a wayata." Babu musu suka bita.

Wawan tsaki ta tsaki tare da gyara zama tana cewa,"Na ɗauka za ki karba ki mayar musu, sai na gaya miki wanda ya haife su ba ya ƙaunarsu."

Bata tanka mata ba ta wuce ciki abinta. Sai da ta kunna musu sannan ta koma kicin ta ci gaba da girkinta.

Rashida kuwa da ta shigo cikin dakin a lokacin da ta dawo. Ganinta a falon babu ɗankwali da kuma ƙunshi inda ta yi, sai da ya sanya gabanta ya fadi. Ta yi kyau sosai da gaske. Lallin da take shafawa ƙwana biyu ya ƙara hasken fuskarta. In ban da rashin ƙiba sai ta ce tana cikin matan da za a iya sanya su a cikin kyawawan jerin farko. Wani irin mugun kishinta ya kamata. Bisa wannan dalilin ya sanya ta fito falon don ta kore ta, duk da ta san cewar ba ta a gabansa, amma kyawun da ta yi ya firgita ta.

Tana zaune har ta kammala abincin ta ibo nasu ta shige ciki. Da sauri ta tashi ta shiga ɗaki ta ɗauki maganin da Malam ya ba ta. Zubawa a cikin abincin Faruk ta yi tana faɗin,"Yau zan yi wannan shegen maƙon naka, ace mutum sam ba ya ƙwantaluwa." Bayan ta gama zubawa ta juya sannan ya koma ta zauna a falon. Tana zaune aka yi magariba, amma ta ci gaba da kallonta, ba tare da ta damu ta yi sallar ba. Har aka yi isha'i ba ta tashi ba. Sai da ta ji motar Faruk sannan ta miƙe ta buɗe masa ƙofa. Tana shigowa ta faɗa jikinsa tana masa shagwaɓa. Shi kuma ya wani susuce.

Bayan ya yi wanka ya ci abincin sosai. Cikin jin dadi take kallonsa ganin yadda y ci sosai. A ranar ta yi masa duk abin da yake so, wanda hakan ya ƙara sanya ya shi zuzucewa, yana tunanin duk soyayya ce, ba tare da sanin abin da ke zuciyarsa ba.

Cikin sama magani ya fara cin Faruk. Wani irin mugun ƙauna yake mata kamar zai lashe ta. Ganin haka sai ta kalle sa ta ce,"Baby gaskiya bana son cimar da muke yi, ya kamata ka raba mana abinci, tun da ita ta saba." Zuciyarta na bugawa domin a tunanin ta ta ɗauka zai taso mata ne, amma ga mamakinta sai ta ga ya kalle ta ya rungume ta, tare da kai bakinsa cikin nata. "Ba ki da matsala anjima sai mu fita mu siyo duk abin da kike so, ita kuma sai na rinƙa ba ta nata."

Jin abin da ya ce sai ya sanya ta cikin farin ciki sosai. Ganin tarkonta ya kama kurciya zai zamo mata janitalau. Da yamma kamar yadda ya gaya mata suka fita. A kayan abincin har da su indomie ƙwai madara milo duk wani abin kayan ci. Bushashshen kifi da su ƙwai. Siyayya taga-raga ya yi mata ita kanta sai da ta yi mamaki, saboda cewa ya yi ta zaɓi duk abin da take so.

Da suka dawo Nasreen ta cika da mamaki. Satan kallon siyayyar take yi tana mamaki. A zuciyarta tabbata ba a cikin hayyacinsa ya yi ba, sai dai in ta bi ta bayan ƙasa, domin Faruk ko mai za ta yi masa maƙonsa a jininsa yake. Hatta 'yan'uwansa fama suke da shi. Shi kansa a irin rayuwar da yake yi status ɗin da ya wuce haka.

A store aka sanya kayan sannan ta kulle abinta. Farouk ya tsaya a falon yana kallonta."Daga yau na raba muku girki, zan rinƙa ba ki na ki da kaina, ita kuma za ta rinka mana ni da ita da abincin da yake store." Ya ce mata cikin ɗaurarriyar fuska yana kallonta.

"Ok ba matsala." Iya abin da ta ce masa kenan ta mayar da kanta ba tare da ta kalle shi ba.

Jin abin da ta ce sai ya kalle ta. Ya lura da ita kwanakin nan ta saki har ɗan murmurewa ta yi. Mamaki yake ganin ko da yaushe tana cikin ɗakinta. In dai ba girki za ta yi ba, kuka hakan ba ta nuna alamun ya dameta.

"Ko tana waya da su Marwana?" Ya yi ma kansa tambayar yana girgiza kansa, domin ya san yadda suka yi rabuwar rashin mutunci da wuya, wai auren mace da ciki.

"To mai take yi?" Ya yi ma kansa tambayar yana son gano canjin da yake hange daga gare ta. In da ace ada ne sai ta yi masa ƙarafi, amma yanzu ya lura ko kallon sa ba ta son yi, ballanatana dogon magana.

Nasreen ganin ya tsaya mata a kai kamar soja yana kallonta, sai ta miƙa tana cije baki, saboda ta yaye Musaddik nonota zafi yake mata. Ɗauki ta shige hankalinta kwance.

Kallo ya raka ta da shi yana mamakin canjin da ta samu. Ko fuskarta ya bayyana farinciki, saboda ada kullum kamar ta yi kuka, amma yanzu har wani annuri yake gani a fuskar.

Zuciyarsa ya fara zargin wayarta don haka ya ɗau alƙawarin sai ya duba.

Washegari aka gyara gyara garin aka sanya drinks. Wannan lamarin sai ya ba ta mamaki. Rayuwarsa ta zamo ta 'yan gayu, sai daɗi suke ci, saboda kullum in zai dawo, sai ya yi mata take away. Ko ya siyo mata nama ba ta san ran ci, domin ba ta sanya wa a ka za a bata, kuma kamar yadda ta yi tunani haka suke cinyewa. Wani irin love ake zubawa a cikin gidan. Ita kam dariya suke ba ta, duk da cewar wani abun da biyu ake mata.
Chapter 7 · 0% Book details