← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 92

Sashe 85

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana jin yadda yake rera ƙira'a yana fitar da tajweedi. Yana ta karatun idanunta lumshe tana saurarensa. A zuciyarta ji ta yi kamar ta ɗauro alwala su yi karatun tare. Sai dai tsanannin kunyarsa da take ji ba zai ta iya ba.

Murmushi ta yi tuna abin da ya faru jiya. A daren jiya ta daina mamakinsa, domin ya wuce duk inda take tunani. Tabbas Damir ya san kan sace zuciyar mace. A irin zumar da ya shayar da ita na ƙauna, sai ta daina ganin kishin Batula domin tana jin a yadda ta kamu da sonsa, da yadda yake kula da mace za ta iya aikata hakan. Damir duniya ne tabbbas ɗan soyayya ne. Ya san yadda zai sarrafa mace, ta kasa ganin kowa sai shi ta kowa ne ɓangare. Tunawa ta yi zai iya ƙara aure lokaci guda ta ji zuciyarta na shirin bugawa.🙄🙄🙄🙄

Tana wannan tunanin ba ta san har an kira sallar asuba ba. Tashi ya yi, ya rufe qur'anin ya tafi masallaci.

Yana fita ta miƙe da sauri ta shige bayi. A gurguje ta yi wanka ta ɗauro alwala. Saboda tana jin kunyar ya shigo ba ta ja doguwar raka'a ta sallame.

A ka gado ta yi azkar na sallah. Bayan ya yi sallah sai ya shigo cikin gida don ya tashe ta, kar lokaci ya ƙure. Tana jin alamun buɗe ƙofa ta ja bargo har saman kanta.

Sai dai kafin ta ja ya ganta. Murmushi ya yi tare da ƙarasa wa kan gadon ya hau. Mamakin yawan kunyarta yake ji. Shi da ya san ance mace bazawara sam ba su da kunya, amma ya yi mamaki ko kuma dai tasa ce a haka.

Kan gadon ya hau tare da kai hannu zai ja bargon. Kamar ta gane nufinsa sai ta juya ta cukurkuɗe shi a jikinta. Murmushi ya yi."Matata Nasreen," Ya furta tare da ƙara kai hannu, ya fara ƙoƙarin cire bargon.

"Lokacin sallah zai wuce ko tashi, dalilin da ya sanya na barki ki huta, saboda na san na wahalar da ke, amma da asuba ya dace ki yi."

"Please Ya Damir nayi sallah." Ta furta da muryar kuka, ganin zai cire mata bargon kuma akwai wadataccen haske a ɗakin.

Dariya ya yi,"Ban yarda ba domin kaya bacci ne a jikin ki." Ya ce bayan ya ja bargon.

Da sauri ta riƙe tana faɗin,"Na canza wannan fa pink ne." Cikin muryar shagwaɓa ta ce mishi.

Burge shi ta yi domin yana son shagwaɓar."Ok na yarda amma mene ne na jin kunyata? Ai na yi tunanin na cire duka kunyar?"

"Don Allah ka bar ni bacci zan yi." Ta ce masa tare da satan kallon sa domin kunyarsa take ji.

"Ni ma bacci zan yi mu kwanta matata. Yau hutu za mu yi." Ya ce mata tare da kwanciya ya jawota jikinsa.

Duk kunyarsa da take ji, kan dole ta kyale shi suka kwanta, domin ta san ba zai barta ta kwanta ita kaɗai ba.

Ba su tashi bacci ba har sai karfe goma shi ma kiran Muhsin ya tashe su. Goge idanunsa ya yi sannan ya ɗauki wayar yana faɗin,"Muhsin,"

"Na'am Ya Damir. Ina bakin get Breakfast na kawo in ji Momi."

"Ok ina zuwa." Ya ce tare da sauka kan gadon.

Yana fita Nasreen ta miƙe ta ɗauki wayarta ta nufi ɗakinta. Wanka ta shiga bayan ta gasa jikinta, saboda har yanzu duk joint ɗinta ciwo suke mata.

Bayan ta fito daga wanka, ta zauna ta cancaɗa kwalliya, sannan ta sanya atamfa riga da siket mai kyau.

Wayarta ta ɗauka ta kira Marwana. Marwana da an ci kuka har an bawa uku lada.

Ko da Muhsin ya kawo abinci sai dai Ahmad ya karɓo, amma bai ganta ba.

Tun dare yake aikin rarrashi, amma kamar kara tunzurata yake yi. Kalmar mugu kam ya sha babu adadi. Shi kansa ya tausaya mata, domin bai san ya zaƙe da yawa haka ba.

Da kyar ya samu ta yi sallah sannan ta sha magani. Tsoro ya ji ko sai an yi mata ɗinki. Yanzu haka ma kiran likita ya tafi Nasreen ta kira.

Tana ɗauka ta rushe mata da kuka."Nasreen kin ce Ya Ahmad zai kula da ni, ashe mugu ne?"

Dariya ta ba ta sosai, duk da tambayar da gaske ta yi mata. Sai ta ba ta tausayi, domin ko ita da ta taɓa aure ta san wuyar da tasha.

"Marwana ki yi haƙuri, wannan shi ne auren ke ma kin san haka?"

"Na sani amma ai zalinci ya yi mini. Na rantse gun Mommy zan koma."

Dariya ta yi jin abin da ta ce,"Ina Ya Ahmad ɗin?"

"Ya fita kamar likita ya k.."

Kafin ta gama maganar, kawai sai ta gan shi a tsaye ya fisge wayar yana huci. Kunya sosai ya kama shi, ganin da wacce take wayar.

"Yanzu kin kyauta Baby. Nasreen ƙanwata ce, amma kika zauna kina gaya mata komai?"

"Nasreen ƙawata ce, dole na gaya mata abin da ke damuna." Ta yi maganar cikin zallar shagwaɓa tare da karɓe wayarta.

Kunya sosai ya ji dama ya san tun da suka aure su, shikenan sirrinsu yana hannun ƙanni. Ta gaya mata rayuwarsu ita kuma ta gaya mata na su da damir.

"Mommy ta kawo abinci ta shi kiyi breakfast, sannan ki sha magani."

"Ni ba zan sha ba gida zani."

Jawota ya yi yana murmushi, saboda ya gane muguwar 'yar shagwaɓa ne.

"Haba autar Momi zuciyar Ahmad." Abin da ya ce ba ta san lokacin da ta yi murmushi ba.

"Yauwa haskena let's go and eat." Ya ce mata tare da kama hannunta.

Da ƙyar ya samu ta ci abinci, sannan tasha maganin ta kwanta. Shi ma bacci ya koma, saboda jiya bai samu ya rintsa ba.

Damir ɗa ya dawo ya ga ba ta a ɗakin. Bayi ya shiga ya yi wanka, sannan ya cancaɗa kwalliya tamkar wanda za shi gasar kyau. Ya yi kyau sosai a cikin ƙananan kaya.

Tana cikin ɗaki, tana sanya ɗan kunne ya shigo da sallama. Da sauri ta koma gurin windo ta ɓoye a labule. Ganin haka babu shiri ya saki dariya tare da ƙarasawa kusa da ita.

"Yau na zama surukin ki ko Nasreen?" Ya ce yana haɗa jikinsu.

Fuskarta ta rufe tana furta,"Ina kwana Ya Dam..."

"Shitttt!" Ya ce bayan ya kai hannunsa kan bakinsa.

"Ba na son Yayan, saboda yau ya kamata a canza mini suna."

"Abban Marwana." Ta ce cikin jin kunya.

"Nope wannan is local I need special and extraordinary."

"Ok, Rajlul salihi."

"Umm partially, saboda so na ke duk za ki kira ni, ki canza mini suna."

Zare idanunta ta yi jin abin da ya ce."Yes Nasreen ni da matata tamkar Hassan da Hussaini muke. Don Allah ki saki da ni mu ci amarcinmu, sannan na kwaso kyawawan yaranmu mu yi rayuwarmu cikin farinciki."

Murmushi ta yi tare da sunne kanta."Please baby close you eyes, I wanna surprised you." Ya ce mata tare da ɓoye abin da yake hannunsa.

"Ok, Husband." Ta ce masa sannan ta rufe idanunta.

"Don Allah ki fi ce mini Husband, domin ni na gaya wa Batula ta rinƙa kirana haka, amma da yake ke 'yar baiwa ce kin kira."

"Ok, baby."

Murmushi ya yi jin ta bi umurninsa."Then did you close?"

"Yes I did." Ta ce tare da ƙara rufe idanun sosai.

"Ok, You can open." Ya ce bayan ya ɗora mata ɗan kunne da tsarkar gwal a hannunta.

Ware idanunta ta yi cikin mamaki ta ce,"Wow! Masha Allah."

"My gift for yesterday saboda jiya kin kai ni wata duniya."

"Kai Ya Dam... Husband." Ta yi maza ta ce haka ganin kallon da ya watsa mata.

"Na gode Allah ya ƙara buɗi, ya tsare mini kai ya kuma ba ni ikon maka biyayya."

"Amin," Ya ce cikin farinckin addu'ar da ta yi masa.

"Kawo na sanya miki." Ya ce tare da miƙa mata hannunsa ta saka masa. Haɗawa da hannun ya yi, ya sumbaci yatsun da suka sha adon lalli yana murmushi. Ita ma murmushi ta yi masa.

"You You look pretty!"Ya ce tare da rungumeta.

"Zo mu je mu karya." Ya kama hannunta suka nufi dinning. Duk kunyarsa da take ji sai da ya nace ya bata abinci, domin ta fuskanci ta karɓa shi ne kawai zaman lafiyarta. Bayan sun ci, duk da ba abincin kirki ta ci ba saboda kunya.

Bacci ya jata suka koma, domin maigadi ya sanar kar wanda ya shigo. Bacci sosai suka yi, sai ƙarfe ɗaya suka farka. Da ya yi alwala, ya fita daga nan zai wuce gidan Hajiya.

Yana fita ta gyara gidan sannan ta zauna tana kallo. Ba ta jima da zama ba, Momi ta kawo lunch.

Su Anty Sha'awa suka kira ta suna waje. Suna shigowa ta rungume su cikin farinciki.

"A Lallai ka ga amare su Nasreen har an fara kyau, ko dai kin samu ciki ne?"

Dariya ta yi jin tambaye banzar da tayi mata."Anty Sha'awa yanzu ne na yi aure. Dama akwai maza 'yan aljanna irin mijina?"

"Lallai Nasreen sabon shiga." Suka ce tare da kwashewa da dariya.

"Ba za ku gane farincikin da na ke ciki ba. Haƙiƙa in har ya ɗore a haka sai na ce na fi ko wace mace sa'a. Mijina daban yake a cikin maza. Haƙiƙa dole matarsa ta yi kishinsa."

"Ai Nasreen ko a ido aka kalle shi an san kin yi dace. Daga gidan Marwana muke ko kaɗan ba ta da matsala. Ba ki ga yadda ta karɓe mu ba, duk da ba ta da lafiya don shi ya yi hidimar gidan."

"A Ya Ahmad dole ai ya yi aiki ya taɓo autar Momi."

"Aikuwa abin ka da 'ya'yan hutu. Magana kawai ya yi mata, ta fara kuka tana gaya masa kanta bai daina ciwo ba."

Dariya ta yi ta ce,"Zai sha shagwaɓa Marwana akwai raki."

Shiga kicin ta yi tare da su su ci wannan su ɗauki wannan. Kaza ɗaya ta ɗauko musu suka yi warming ɗin ta.

"Ke dai Nasreen, in miki ta Baba ya ce jinin arziki ne dake. Dubi wannan rayuwa, kana irin wannan rayuwa ai mantawa da kowa za ka yi. Farouk ina ma zai zo ya ganki? "
Chapter 85 · 0% Book details