Sashe 90
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wasu mazan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 47
BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR.
Rayuwa ta shuɗe da canjin da aka samu a cikinta. Damir da Ahmad Allah ya buɗa musu sosai sun ƙara kuɗi, domin Ahmad ya canza wa Mama gidan da take ciki.
An yi auren Muhsin da Hajar har sun haifi yara biyu. Sannan Zainab ma an yi mata aure da saurayinta, da suka haɗu a lokacin da take service, har sun haihu ɗaya.
Nasreen ta ƙara haihuwa biyu bayan Zahira da ta haifa. Ta haifi namiji an sanya masa Umaimah sai muka Nauwal sai ya zama yaranta bakwai kenan. Marwana ma ta ƙara uku maza biyu da mace.
Raihann da Little Marwana an girma an zama 'yan mata, domin a lokacin suna shekara goma sha takwas. Sun kammala karatun su na sakandiri suna shekarar farko a jami'a. Musaddik shi ne ya rubuta jamb yana jiran result ya fito. Su Ubaidah da Ubaidullahi ana sakandiri.
Alhaji Damir ya girma ya zama babban mutum. Ya ƙara kuɗi da wayewa.
Hajiya Nasreen, tana zaune a katafaren falonta da ya sha kaya masu kyau da tsada.
Tana sanye cikin tsaddaden leshi kalar golden doguwar riga. Kasancewar ranar juma'a ne, ya sa ya ta yi wannan shigar, amma har yau da ta girma in tana gida ƙananan kaya take sawa, babu ruwanta da yara, don su ma irin shigarsu kenan. Remote ne a hannunta tana canza tasha. Nauwal ne ya rugo da gudu Umaimah na bin sa a fusace.
Da sauri ya ɓoye a bayanta daidai lokacin da Alhaji Damir yake sakkowa daga matakalen bene.
"Umma, kin gan shi ko? Ki gaya masa Ni ba tsarar wasan sa bace, da zan sanya game Laptop ɗina, na shiga kicin ya canza."
"Umma, alƙawari ta yi mini kuma taƙi cikawa." Ya ce yana nishin gudun da ya yi.
"Nauwal zan zane ka fa, saboda ba tsararka bace. Oya tell her sorry." Ta ce tare da kama hannunta.
"Anty Umaimah sorry." Ya ƙarashe cikin muryar kuka, daidai lokacin da Damir ya sauko.
"Daina kuka boyna, zan siya maka na ka yau in sha Allahu zan yi maka oder."
A madadin ya yi kukan sai ya washe baki "Abba thank you." Shafa kansa ya yi cikin murmushi.
Yaron ya ruga yana murna sai Umaimah ta ji sanyi, domin siyan masa ita kanta za ta samu natsuwa.
Damir jawota ya yi ganin yaran sun tafi."Matata."
"Barka da fitowa mijina." Ta ce tana shafa sumansa.
"Ban yarda da cin hancin nan ba, bayan kin ƙi kwanciya ki huta."
"Yaran nan ba za su bar ni ba, kana ganin Husnah kuka ta rinƙa yi za ta sha tea."
"Ai yarinyar nan da shagwaɓa halin uwarta Marwana ta gado."
Dariya ta yi ta ce,"Marwana ko ita ka ta ƙorafi take yi da rigimarta, saboda ba ta barinta ta huta."
Zama ya yi sai ta zauna kusa da shi."Baby wankan nan ya cige ni ina za ka?"
"Wata ce tana ce wai don Allah, na taimaka na aure ta, shi ne na ke tunanin samo miki 'yar...."
Fara diddira ƙafarta ta yi, kamar za ta yi kuka."Ashe kuwa kana son yau na yi kwana prison, domin sai na nemo ta ko a birnin Sin take, na aikata mata ba daidai ba."
"Taimakon ki zan yi fa, yanzu kika gama cewa hidimar yara sun yi miki yawa."
"Ba su yi mini ba, zan iya in dai wata za ta shigo mu yi sharing ɗinka na haƙura, ko da ace aiki zai kashe ni."
"Zo nan kin ji matata, ke kaɗai kin ishe ni a rayuwata. Ina son ki ba zan iya haɗa ki da wata ba."
"Ni ma ina son ka mijina." Ta ce tana ƙoƙarin haɗa bakinsu.
Sallamar Little Marwana da Raihann ya sanya suka shigo. Yaran sun ga abin da za su yi, amma sai suka yi murmushi, domin sun saba da wannan. Sun yi kyau sosai. Yaran farare ga hutu da ya bayyana a jikinsu. Suna cikin shiga ta alfarma. Baƙar abaya ce a jikinsu da ta ɗauki fatarsu, sai suka yi rolling gyalen abayar. Kuma cikin ikon Allah dai suka tashi a tare. Raihann ce ta ɗan fi Little Marwana ƙiba, saboda ita ba ta son cin binci dai chocolate kamar ƙaramar yarinya.
"Umma, Abba na gaji gaskiya, a canza mini mota tana wahalar da ni."Little Marwana ta ce tare da zama ta dafe kanta, ita a dole ta gaji sai ka ce a ƙasa ta dawo.
"Magaji mafiyi. Umman yara kin san lokacin Marwana in tana son a canza mata mota, sai ta yi ta cewa motar ta yi kaza. Har sai ta san yadda ta yi ta aka canza mata, kin ga 'yarta ta gado ta."
Dariya ta yi jin abin da ya ce,"Abba ba haka bane Allah ka tambayi sis. Har cewa na yi ta tuƙa ta ce ba za ta iya ba. Da yasan wahala za ta bani cewa ta yi da motarta ta tafi."
"A canza mata tun da tana so." Cewar Nasreen tana kallonta.
"Ok, kin goyi bayanta kenan? Ban yarda ba sai na tambayi Raihann. Sai ya mayar da idanunsa kanta ya ce,"Da gaske take yi?"
Dariya ta yi ta kalle shi."Eh Abba."
"Ba wani nan bakinku ɗaya." Ya ce yana dariya.
"Ni ma Abba a siya mini mota." Musaddik ya shigo falon yana faɗin haka.
"Ba za a siya ba sai ka girma." Cewar Nasreen tana harararsa.
"Umma na girma jami'a zan shiga don Allah ka siya mini mota."
"Kwantar da hankalinka in har ka ci jamb zan siya maka."
"Oh yes! Zan ci I did read." Ya ce cikin murna.
"Shikenan in sha Allahu zan yi wa Daddy Ahmad magana, in zai shigo da mota, sai ku faɗi wacce kuke so har da Raihann."
"Thanks dad." Suka rungume shi sun faɗin haka.
Murmushi yake yi cikin tsananin ƙaunarsu. Nasreen kallon shi take yi kamar ta lashe shi. Har yau ba ta taɓa ganin ya yi abin da zai bambanta su da yaransa ba. Haƙika babu abin da za ta iya saka wa Marwana, da ta shigo mata da shi cikin rayuwarta. Ya shayar da ita zuma, a lokacin da ta kwankwaɗi maɗaci take ganin ba za ta taɓa shan zuma ba. Damir ya zama hasken da ya haskaka rayuwarta. Ya kawo sauyi da dama a cikin rayuwarta.
Ranar safiyar juma'a suka tashi da tashin hankali. Domin Baba ya fita mota ta kaɓe shi. A lokacin da aka kira Nasreen aka gaya mata yana cikin mayuwayacin hali. Kuka ta fashe da shi, sannan a kira Damir. Yana ganin kiran hankalinsa ya tashi domin yana cikin asibitin. Ganin halin da yake ciki sai da ya yi hawaye, domin sai dai addu'a. Jini yake fita daga bakinsa kansa ya kumbura.
Kwantar mata da hankali ya yi, sannan ya sanya direba ya kawo ta asibitin.Ahmad shima kuka yake yi, ganin halin da yake ciki. Duk ƙoƙarin da likitoci suke yi kar ya yi magana, amma sai kuka yake yi yana neman gafara.
Nasreen tun da ta ga Damir ta ga kuma yanayin fuskokin su. Sai ta shiga cikin tashin hankali." Ya Ahmad ya jikin Baba?" Ta yi masa tambayar tare da kama hannunsa.
Hannunta ya ja suka shiga ciki, daidai lokacin da Zainab da Mama suka ƙaraso. Suna ganin halin da yake ciki sai kuka.
"Baba addu'a yake so Nasreen." Damir ya ce mata yana share hawaye.
Lokaci guda asibitin ya cika domin duk wanda ya zo, zai kira wani don ya zo in suna da rabon ganawa. Kuka sosai suke yi ganin halin da yake ciki. Kai rayuwa babu tabbas domin rai ba a bakin komai yake ba. Baba ya daina numfashi sai da taimakon oxygen.
Hanunnsa yake miƙo musu da su zo. Suna kuka suka ƙarasa gurinsa." Kun ga yadda Allah ya mayar da ni ko? Ku yafe mini irin rayuwar da na gina kuna cikinta. Na yi dana sani na tuba, don Allah ku yafe mini kar na koma gurin Ubangijina da haƙƙin ku na haife ku ban kula da rayuwarmu ba. Don Allah ku yafe mini." Ya ƙarashe maganar numfashinsa na ɗauke wa.
"Babu komai Baba, mun yafe maka Allah ya baka lafiya." Nasreen ta ce sai Ahmad ya riƙe hannunsa, ganin zai ƙara magana.
"Don Allah ka yi shiru ka bari ka warke"
"Ahmad mutuwa zan yi, kana ganin yadda na koma. Gara na roƙi gafararku. Maman Ahmad ku yafe mini."
"Ina ga mu yi mishi viser a fita da shi." Cewar Damir cikin tausayi yana kallonsa.
"Haka za a yi." Ahmad ya ce yana share hawaye.
Suna cuku-cukun viser a daren Baba ya cika. Nasreen kuka sosai take yi kamar ranta zai fita, saboda kasa komawa gida ta yi ganin halin da yake ciki. Damir ya riƙe ta ganin yadda take kuka sosai. Haƙuri ya rinƙa ba ta tare da jawo mata aya.
Shi kansa Ahmad sai da ya koka. Daya tuna irin rayuwar da suka yi da shi. Yau gashi a kwance ya yi kwanan keso. Kafin gari ya waye asibitin ya cika ana ta koke-koke. Hatta jikokin nasa sun ji mutuwarsa, domin ya canza ya ja su a jiki ga shi da tsokana. Sun saba da shi ya iya baƙar magana da barkwancin. Gida aka wuce da gawar, nan suka ci gaba da kuka suna roƙon masa gafara, har aka yi masa sutura aka kai shi makwancinsa, sannan suka zauna zaman makoki. Duk abin da ake ci Damir da Ahmad suke ɗawainiya, domin abincin mai kyau da ruwan faro ake sadaka dashi. Aka ci gaba da karɓar sadaka.