Sashe 6
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Faruk kuwa da biyu ya yi, ya yi haka ne don ta gane yanzu ba ta a gabansa, amma sai ya ga ko a kwalara rigarta. Ganin duk abin da yake yi sam ba ta damuwa, sai ya tsiri zama da Rashida a falo su yi ta rungume-rungume yana shafa jikinta. Hakan ba ƙaramin tayar da hankalinta ya yi ba saboda tarbiyar yaranta. Da fari ba ta nuna musu komai ba, sai ta rinƙa kulle su a ɗaki. In suka damu za su fito su yi kallo, sai ta kunna musu a wayarta. Duk a kan wannan ta yi alƙawarin ba za ta tanka masa ba, ballanatana ya yi tunanin ko tana kishinsa ne. Duk abin da yake mata sai tana kawar da idanunta, wanda hakan ba ƙaramin ɓata masa rai ya ke yi ba. Ya so ace ta tanka ya nuna mata iyakarta, musamman yanzu da take masa wani gani-gani.
*_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 4
Da daddare bayan ta kwanta duka lokacin bai fi ƙarfe tara da rabi ba. So take su Raihan su yi bacci ta karɓi wayarta, ta ci gaba da karanta wani littafi mai suna "Sakacina ko halin maza" wanda Jamila Lawal Zango jamsy ta rubuta. Sam ba ta da ra'ayin karatun novel, domin asali tana kallon masu karantawa a mutanen da ba su da aiki, musamman da ta ji ana maganar Marubuta ba su da aiki sai rubutun batsa, da sanya mata su yi rashin kunya ga mazajensu, amma sai Maman Muwaddat ta yi recommending ɗin ta a kan ta ƙaranta litaffin saboda tsayuwarsa da ilmin dake ciki, kuma yana ɗauke da kewa, musamman ita da take cikin kaɗaici, wannan dalilin ya sa ta yarda ta tura mata labarin duk da cewar hankalinta bai kwanta ta fara karatun Hausa novel ba, amma kuma ba ta son ta ƙaryar mata da gwiwa. Don haka ta tura mata ta fara karanta. Da fari ta ji kamar ta daina, saboda ba ta jin wani daɗin karatun, tun da ba ta saba ba, amma da ta jure, sai ta fara jin daɗinsa, ta ji tana son ta kai ƙarshen labarin ganin yadda jarumar ta ke shan wahala, tare da mamakin ɗaya jarumar Zainab da ta yi watsi da damarta Allah ya ba ta mijin da yake mugun sonta, amma sakacinta da sakarcinta ya sanya wata ta ƙwace mata shi.Tunanin jarumar labarin take Juwairiya yadda ta sha gwagwarmayar rayuwa. Tabbas Allah ya jarrabce ta da ta yi rayuwa a gidan mijinta a matsayin 'yar aikin matarsa, alhalin babu wanda take so kamarsa, duk da cewar babu wanda ya ja mata sai mugun ƙanin babanta Bana Sani. Saboda cakwakiyar da ke littafin ta ƙasa su yi bacci ta ga yadda za ayi da ta yi auren kwangila don ta haifi yaro ya bawa matarsa. Tsananin mamakin mugun son zuciyar M.D da son matarsa da ya rufe masa ido ya kamata. Sai duk ta ƙosa ta ga ƙarshen labarin. Saboda zumuɗin ta ƙarshe karanta labarin ta fisge wayar tana faɗin,"Raihan ku yi barci gobe zan sanya muku karatu zan yi."
Raihna ta saka kuka tare da miƙa mata hannu tana faɗin,"Umma, don Allah ki ba ni cartoon ɗin ya kusa ƙare wa."
"Ba zan ba ki ba, na ƙasa na ga shin in Zainab ta gane matarsa ce ya za a.."
Maganar ta maƙale sakamakon jin ihun faruk da Rashida wanda ya tabbatar mata da saduwa suke yi. Hankalinta ya tashi matuƙa har sai da ta kasa ganin abin da yake rubuce a wayar. Tana cikin wannan tashin hankalin ta ji Raihan ta ce,"Umma Abba da Anty Rashida na kuk.."
Toshe mata baki ta yi tana hawaye."Ba kuka suke yi ba, al'janu ne suke kwaikwayon irin kukan su, maza ki kwanta kar su cinye ki"
Tsananin tsoro ya kamata da sauri ta kwanta ta rufe fuskarta da bargo.
Nasreen kuwa tsabar takaici ya kamata. Saboda ganin rashin hankali sai ta ji kamar ta je ta yi musu rashin mutunci. Karatun qur'ani ta sanya a wayar ta kai ta kusa da kunninta, ta yadda ba za ta ji ihun ba, a zuciyarsa ta sa ya sai ta yi masa magana, domin ba za ta yarda ya ɓata tarbuyar yaranta ba."
Sai da ta daina jin ihun sannan ta kashe wayar. Karatun da ba ta yi ba kenan, saboda takaici ta kwanta bacci.
Washegari da safe bayan ta kammala musu abin kari. Tana zaune a falo ya fito cikin shirin fita.
Ganinta zaune ya ɗauke kansa bayan ya wurgar mata harara. Tana lura da ya fito ta miƙe.
"Ina son magana da kai." Ta ce masa tare da shan gabanta.
Kallonta ya yi a wulaƙance, kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya ja ya tsaya."Ina fatan ba ƙorafi za ki yi mini kan bana kwana a ɗakin ki ba? Saboda kin san ba zan zo ba, don na samu wacce take da duk bin da na ke so."
Jin abin da ya ce ya sa ya ta saki murmushin takaici."Saboda me zan tambaye ka? An gaya maka na dawo don ina son na ci gaba da rayuwar aure da kai ne?"
"Na sani shi ya sa na ije ki a matsayin yar aiki." Ya ba ta amsa yana mata kallon mugunta.
"Lokaci ne komai zai wuce kuma ya zama tarihi." Ta ce masa kafin ya yi wata magana sai ta katse shi ta hanyar cewa,"Abin da kake yi kana tunanin wayewa ce? Kana da yara za ka zauna kana aikata haka? Dole yin hakan zai bayyana cewa ka samu macen da take iya biya maka buƙatunka?"
"Kina kishin haka tun da kin kasa yi?"
"Ko ɗaya ina dai maka nasiha ne saboda ba shi da alfanu, duba ga kana da yara kuma sam ba tsarin addi..."
"Ke!" Ya daka mata tsawa cikin ɓacin rai." kin isa ki kafa mini doka a cikin gidana? Ko da uban wani aka gida?" Ya ce mata yana zare idanunta.
"Ko ɗaya ina dai gaya maka ka bari ko don yaranka."
"To ba zan bari ba, kuma haka na yi ra'ayi zan cigaba. Idan ke kin kasa sanya ni a cikin wannan dadin na damu sai ki yi baƙinciki?"
"To shikenan, tun da haka ka ce inka so ka cika duniya da ihu." Ta ce masa tare da galla masa harara ta shige ɗakinta.
"Lallai yarinyar nan ta raina ni." Ya ce yana jinjina kansa. Wata zuciya ta ba shi shawarar ya je ya yi mata tijara, amma kuka sai ya fasa, a tunaninsa kishi ya sanya ta yi masa magana. Ficewa daga gidan ya yi.
Tun daga nan suka tsiro haka abun babu kyan tsari. Ganin haka da an yi magariba su Raihan sun ci abinci za ta sanya su baccin dole. Hakan da ta yi ta samu ta shawo kan damuwarta. Da suka ga ba ta ƙara musu magana ba, sai ya tsiri zama a farko yana ma Rashida waƙa.
Nasreen duk ta zo wucewa sai su kwashe da dariya Faruk ya fara waƙa yana cewa," Kalarki kalar ajebota jiki duk madara ko ina yana rawa." Rashida kuwa sai ta yi ta jin daɗi tana juya masa jikin. Ranar da ya fara dariya ya ba ta, saboda gani take kamar jahilci ya sanya shi yin wakan.
A haka dai suka ci gaba da zama sam ba ya shiga cikin sabgarta.
Kamar wasa ta fara zuwa da hijaban makaranta, sai ga shi mutane da yawa sun siya. Ba a ɗauki tsawon lokaci ba ya suka ƙare. Ita kanta mamaki ta rinƙa yi, domin wasu har cewa aka yi ta kawo. Cikin farin ciki ta cire ribarta ta kawo mata kuɗin.
Maman Muwaddat ta kalle ta ta ce,"Dama sana'a sa'a ce. Da gwaji in kina da abinci, sai ki ga Ubangiji ya dafa miki. Nima da haka na fara kamar wasa ya bani shawarar, amma yanzu har a unguwar nan ana saye. Kina nan tallar da kike yi a social media suma za su siya. Da sannu yaro ke iya tafiya. Wallahi in har kina sana'a za ki samu sauƙin rayuwa."
"Sosai Maman Muwaddat kin san kuɗin nan da nake gani, duk da ba nawa bane, wallahi ba ki ji yadda na ke ji ba."
"Za ki ji kuma bari na gaya miki sirri na sana'a, kin ga wannan dubu ashirin da biyar da kika samu? Kamata ya yi ace kin fara sai da ko da 'yan kunnaye ne da su, sai ki yi amfani da biyar ɗin, sai ki ga kin samu karin kanki."
Jim ta yi sai kuma ta kalle ta ta ce,"Kuma kin kawo shawara wallahi, amma kin san na fita na je kasuwa wata matsalar za..."
"Ai dama ba zuwa za ki yi ba, yanzu fa rayuwarmu a sauƙaƙe take. Ƙanina zan turawa kuɗin sai suyi ya tura miki a mota. Kuma ana samun riba sosai za ki yi dariya."
"Allah ina ga haka za a yi, saboda ba ki ji farin cikin da na ji ba, gaskiya riƙe kudi rahma ne."
Dariya suka kwashe suka tafa."Ba ki ji ance kuɗi sune abokan rayuwa, duk iskancin da Faruk yake miki, da ace ya san kina da su, kin ji na rantse ko zai yi kaɗan tun da shi tajararre ne."
"Hmmmmh! Allah dai ya shirya sa, amma Faruk ya yi nisa." Ta ce tana gyara zamanta.
"Har yanzu ba ya kwana a ɗakinki?"
"Ya kwana? An gaya miki yana ƙaunata ne? Baba ke tilasta masa zama da ni, amma Faruk ba shi da maƙiya kamata." Ta ce cikin takaici.
"Ki ci gaba da haƙuri kar ki sanya damuwa don baya kwana."